Manzon Allah: Haske mai kore duhu (32)
Daga Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa Darasi na Talatin da Takwas Tafiyar Manzo (SAW) Umara da saukarsa a Hudaibiyya Annabi (SAW) ya gani a mafarki shi da sahabbansa sun shiga Haramin Makka suna amintattu, kawunansu a aske kuma suna yin kasaru. Ya sanar da sahabbai niyyarsa ta tafiya yin Umara, su ma suka yi […]
Daga Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa
Darasi na Talatin da Takwas
Tafiyar Manzo (SAW) Umara da saukarsa a Hudaibiyya
Annabi (SAW) ya gani a mafarki shi da sahabbansa sun shiga Haramin Makka suna amintattu, kawunansu a aske kuma suna yin kasaru.
Ya sanar da sahabbai niyyarsa ta tafiya yin Umara, su ma suka yi nufin fita tare da shi sai dai kauyawa da munafukai sun zaci idan ya tafi ba zai dawo ba, don haka suka ki tafiya suna masu fadar a nema musu gafara dukiya da iyali sun shagaltar da su.
Ya fita tare da sahabbai a watan Zul-Kida shekara ta 6 Bayan Hijira, yawansu mutum 1,400, tare da abin hadayarsa don mutane su gane ba yaki ya fito ba. Da suka kawo Zul-Hulaifa ya yi Harama da Umara.
Sannan ya tafi har ya kai Asafan a nan ne dan leken asirinsa ya zo ya shaida masa cewa Kuraishawa sun hadu za su yake shi kuma sun toshe hanyar shiga Harami. Da ma Kuraishawa sun sauka a Zul-Dawa sai suka aiki Khalid dan Walid da mahaya 200 zuwa Kura’ul Gamim kusa da Asafan don tare hanyar shiga Makka kuma sun nemi taimakon Habishawa.
Manzon Allah (SAW) ya nemi shawarar sahabbai shin su kai hari ga Habishawa ne ko su nufi Ka’aba duk wanda ya tare musu hanya su yake shi.? Sai Abubakar (Allah Ya kara masa yarda) ya ce, “Umara muka fito ba yaki ba amma duk wanda ya shiga tsakaninmu da Ka’aba shi za mu yaka, sai Manzon Allah (SAW) ya dauki shawararsa.
Khalid ya samu suna Sallar Azahar don haka ya ce wa mushirikai za mu kai musu hari idan suna yin Sallar La’asar daga nan Allah Ya saukar da Sallar Tsoro a wannan dan tsakani kafin lokacin La’asar sai wannan damar ta kubuce musu.
Manzon Allah (SAW) da sahabbai suka canja hanya suka bi ta Zatul Yamin can gangaren Makka suka sauka a Hudaibiyya, Budail dan Wirka’u ya zo tare da wadansu mutane na kabilarsa ta Haza’awa. Suna nasiha ga Annabi (SAW) suka ba shi labarin shirin Kuraishawa na yakarsa da toshe hanyar da suka yi. Sai ya ce ba abin da ya zo yi sai Umara, ba yaki ba kuma ya ce a shirye yake a yi yarjejeniya da sulhu idan kuwa Kuraishawa suka ki, to zai yake su har ya sare wuyoyinsu ko Allah Ya zartar da lamarinSa.
Buraid ya isar da wannan labari ga Kuraishawa sai suka aiki Makruz dan Hafs, sai Manzon Allah (SAW) ya ce masa kamar dai yadda na fada ga Budail, sun sake aikar Shugaban Habishawa, dama su mutane ne masu girmama yin hadaya da ya koma ya ce wa Kuraishawa gaskiya bai kamata a hana Dan Abdul Muddalib shiga Daki Mai alfarma ba, Kuraishawa sun hallaka! Sai suka ce masa shi bai waye ba kuma ba ya da masaniya game da makidoji, nan suka bar shawararsa.
Sun sake aika Urwah dan Mas’ud, shi ma dai ba nasara ya dawo ya ce ni na ga Kisra da Kaisar da Najjashi amma ban taba ganin mai mulkin da sahabbansa suke girmama shi ba kamar yadda sahabban Muhammad (SAW) suke girmama shi ba.
Ana cikin wannan ne wadansu matasan Kuraishawa su 70 ko 80 suka yi nasu yunkurin na gamawa da wannan ja-in-ja, sai Musulmi suka kama su, amma Annabi (SAW) ya sake su ya yi musu afuwa sai haka ya jefa tsoro a zukatan Kuraishawa har suka karkata da a yi sulhu.
Sulhun Hudaibiyya
Don karfafa maganarsa cewa ba yaki ya zo ba, Manzon Allah (SAW) ya aiki Usman dan Affan (Allah Ya kara masa yarda) zuwa birnin Makka ya tabbatar wa Kuraishawa da haka, kuma ya taho da Musulmi masu rauni, da kuma albishir din budi har babu wani mai imani da zai sake boyewa a cikin Makka.
Abban dan Sa’id Ba’umawuye, shi ne ya sanar da su sakon kuma sai suka bijiro masa da ya je ya yi Dawafi amma ya ki tunda an hana Manzon Allah (SAW). Sun rike shi wanda a nufinsu la’alla don su yi shawara ce sannan su sake shi tare da amsarsu, sai dai dadewar da ya yi bai dawo ba labari ya yadu a tsakanin Musulmi cewa an kashe shi, kashe dan aike kuwa yana nufin sanarwar yaki ce. Da labari ya kai ga Annabi (SAW) ya ce ba za mu bari ba har sai mun gama da mutanen, ya kira sahabbai yana karkashin itaciya a kan su zo su yi masa mubaya’a in dai har an kashe Usman za su yake su ba gudu ba ja da baya. Ya sanya hannunsa mai albarka ya kuma dora dayan a madadin Usman ya ce wannan na Usman ne sannan duk sahabban nan suka ci gaba da dora hannuwansu a kan nasa kaf dinsu, ana gamawa Allah (SWT) Ya saukar da wannan ayar yana mai tabbatar da imanin sahabbai da yardarsu ga albishirin budi. “Hakika Allah Ya yarda da muminai a lokacin da suke yi maka mubayi’a a karkashin itaciya…”
Kuraishawa da suka ji haka tsoro mai tsanani ya shige su suka gaggauta aiken Suhail dan Amru don a kulla sulhu, ya zo ya yi magana mai tsawo, sannan Manzon Allah (SAW) ya karbi sharuddan daga wurinsa, sharuddan da suka bayar su ne:
1-Manzon Allah (SAW) ya koma ba zai yi Umara a yanzu ba amma shekara mai zuwa ya dawo ya yi kuma kada ya wuce kwana uku a cikin Makka sannan kuma ba tare da wani makami a tare da shi ba, sai dai ’yar sanda don kariya irin ta matafiyi.
2-Kowa daga bangarorin ya ajiye makamansa babu yaki ko muna-muna tsakaninsu har tsawon shekara goma.
3-Wanda yake son shiga kullin alkawarin Muhammad ko na Kuraishawa to ya shiga yanzu.
4-Duk wanda ya gudo daga cikin Kuraishawa ya zo Madina wurin su Annabi (SAW), to su mayar da shi Makka, amma wanda ya gudo zuwa Makka daga cikin Musulmi ya zo wurinsu ba za su mayar da shi Madina ba.
Manzon Allah (SAW) ya kira Aliyu (Allah Ya kara masa yarda) yana masa imla’i yana rubutawa. Idan ba mu manta ba yana daga mu’ujizar Annabi (SAW) shi Ummiyi ne, ma’ana bai iya karatu ko rubutu ba, ya umarce shi ya rubuta: “Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Sai Suhail ya ce mu ba mu san Mai jinkai ba ka rubuta da sunan Ubangiji. Annabi (SAW) ya sake umartarsa da rubuta haka din. Sannan ya ce ka rubuta wannan shi ne abin da Muhammad Manzon Allah (SAW) ya yi sulhu a kansa, nan ma ya sake cewa ai da mun yarda kai Manzon Allah ne da ba mu hana ka shiga Daki ba, kuma da ba mu yake ka ba, sai dai ka rubuta Muhammad dan Abdullahi. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai ni Manzon Allah ne koda kun karyata ni amma duk da haka ya sake bai wa Aliyu umarni ya goge Manzon Allah ya maye da Dan Abdullahi din. Sai Aliyu ya ki gogewa yana ganin yaya za a yi haka, sai ya nuna masa inda Rasulullah yake ya goge da hannunsa mai albarka. An rubuta kwafi daya ga Kuraishawa daya kuma ga Musulmi.
Ana wannan rubutu ne sai ga Abu Jundul da ne ga Suhail ya zo a daure cikin mari ya nufi Musulmi sai Suhail ya sa aka mayar da shi, sai Manzon Allah (SAW) ya ce ba za mu warware alkawarinmu ba daga yanzu don haka ba zan hukunta ka ba.
Suhail ya bugi Abu Jundul har ya yi kara ya ce, “Ya ku Musulmi! Za ku mayar da ni wurin mushirikai alhali suna fitinar da ni saboda addinina?” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce yi hakuri lallai Allah zai sanya maka mafita kai da masu rauni. Umar har zai kawo farmaki kan Suhail sai ya fasa.
Za a iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141 ko [email protected]