Manzon Allah: Haske mai kore duhu (34)
A ci gaba da kawo muku tarihin Manzon Allah (SAW) fiyayyen halitta, A yau za mu dora daga inda muka tsaya a makon jiya. 2- Mukaukis Sarkin Iskandariyya: Shi ne Sarkin Masar da Iskadiriyya an rubuta masa wasika kwatankwacin waccan, an gargade shi da daukar zunubin Kibdawa idan ya ki, ya karrama dan aiken Hatib, […]
A ci gaba da kawo muku tarihin Manzon Allah (SAW) fiyayyen halitta, A yau za mu dora daga inda muka tsaya a makon jiya.
2- Mukaukis Sarkin Iskandariyya: Shi ne Sarkin Masar da Iskadiriyya an rubuta masa wasika kwatankwacin waccan, an gargade shi da daukar zunubin Kibdawa idan ya ki, ya karrama dan aiken Hatib, ya kuma rubuta wa Annabi (SAW) cewa ya san akwai Manzon da ya rage amma yana zaton a Sham zai bayyana, sai dai bai karbi Musulunci ba. Har ya ba da kyautar bayi mata a kai wa Annabi (SAW) masu matsayi a kabilar Kibdawa, wato Mariya da Sirina da kuma wata baiwa Bagla. Manzon Allah (SAW) ya zabi Mariyatu ya ba mahayinsa Bagla, Sirina kuma ya ba wa Hassan dan Sabit.
3- Kisra Sarkin Farisa (Iran): An aika Abdullahi dan Huzaafa Assahmi ya kai wa Sarkin Bahrain da ya kai masa da aka gama karanta wa Sarkin Kisra sai ya mutsutsuke ya yayyaga takardar ya ce: “Bawa kaskantacce daga wadanda nake kula da su zai rubuta sunansa gabanin nawa?” Da Annabi (SAW) ya ji abin da ya aikata sai ya yi masa addu’a a kan Allah Ya mutsuttsuke mulkinsa, haka kuwa ya auku.
Darasai na Arba’in
Yadda aka gama da kewayen Khaibara da gabatowar Muhajirai daga Habasha
Yawan wadanda aka kashe a Khaibara daga Yahudawa mutum 93, Musulmi kuma an ce 15, an ce 16 an ce 17.
Wadanda suka yi hijira daga Habasha tare da Amru dan Umayya wanda ya kai wa Najjashi wasikar Manzon Allah (SAW) bayan sun gabato Madina sai suka nufi Khaibara su 16, cikinsu akwai Ja’afar dan Abu Dalib da Abu Musa Al-Ash’ari (Allah Ya kara musu yarda). Mata da yara kuma suka wuce garin Madina, sun iso an gama yakin ke nan. Manzon Allah (SAW) ya yi matukar jin dadin ganinsu yake cewa, “Ban san da wanne zan yi farin ciki ba, da bude Khaibara ko da zuwan Ja’afar? Abu Huraira ma ya taho daga Makka zuwa Madina ya samu Manzon Allah (SAW) ya tafi Khaibara sai ya musulunta kuma ya bi su can.
An raba ganima kuma an ba su wani kaso, dukkan mayakan an bai wa kowane mai doki rabo uku nasa daya na doki biyu, wanda ba mahayi ba kuma kaso daya.
Yahudawa da suka ga sun samu kubuta korarsu kawai aka yi kafin su bar wurin sai suka sako wata bukatar ga Annabi (SAW) cewa a bar su a Khaibara su rika noma kasarta don su suka fi kowa sanin kanta, duk abin da suka noma rabi nasu rabi na Musulmi. Sai kuwa Annabi (SAW) ya yarda da haka ko ba komai sahabbai ba za su shagaltu da noma ba, amma ya ba su sharadin a kowane lokaci ya so zai iya korarsu, suka amince.
Wadil Kura
Gari ne da yake a gaban Khaibara, mazaunansa Yahudawa ne Manzon Allah (SAW) ya wuce can ya kira su zuwa ga Musulunci sai dai ba su musulunta ba kuma ba su nemi kubuta ba, sun fito a yi yaki. Na farko ya fito Azzubairu (RA) ya kashe shi, sai na biyu ma haka. Na uku Aliyu (RA) ne ya kashe shi har dai aka kashe mutum 11, ya kasance duk lokacin da aka kashe wani ana kiransu zuwa ga Musulunci, kuma duk lokacin da Musulmi suka yi wata Sallah sai an kira su har aka yi yammaci amma dai suka ki mika wuya, don haka gari na wayewa rana ta dago ke nan aka auka musu aka karya su aka kwashi ganima.
Sulhu da mutanen Taima’a
Yahudawan wannan gari sun ji duk abin da ya faru tun daga Khaibara zuwa Wadil Kura’a, ana zuwa kansu ba su yi wata-wata ba suka nemi sulhu, a kan za su rika bayar da jizya su zauna cikin aminci a garinsu aka amince musu.
Auren Annabi (SAW) da Safiyya
Da Safiyya ta zama cikin kamammu Dihya dan Khulaifa Alkalbi ne ya dauke ta da izinin Annabi (SAW) sai dai sahabbansa suka ce lallai ba ta dace da kowa ba, sai da kai ya Manzon Allah (SAW)! Domin ita shugaba ce a tsakanin Banu Kuraiza da Banu Nadir, sai Manzon Allah (SAW) ya kira ta zuwa ga Musulunci ta musulunta daga nan ya ’yantata ya aure ta ’yancita ya zama sadakinta.
Bayan ya gama da wadannan garuruwa da aka ambata da kuma sulhu da Yahudawan Fadak bayan da’arsu, sai ya juyo Madina, a Saddus Suhba a kan hanyarsa ta Madina ne suka sauka a nan kuma ya tare da Safiyya kuma ya yi walima, tsawon kwana uku suka yi, sannan suka karasa Madina a farkon watan Safar ko Rabi’ul Awwal Shekara ta 7 Bayan Hijira.
Yakin Zatur Rika
Bayan Manzon Allah (SAW) ya dawo daga Khaibara ya samu natsuwa a Madina sai ya ji wani labarin kauyawa daga Banu Anmaru da Sa’alaba da Muharib za su kawo masa hari don haka ya shirya ya fita tare da mutu, 700 daga sahabbai. Sun sauka wani wuri da ake kira Nakhal mai nisan tafiyar kwana biyu daga Madina, sannan suka hadu da wata jama’a ta Gadafan sai bangarorin biyu suka kusanci juna, sashe ya tsoratar da sashe amma yaki bai gudana ba. Da lokacin Sallah ya yi Manzon Allah (SAW) ya jagoranci rabin sahabbai Sallah raka’a biyu, sannan bayan an gama ya sake jan rabin su ma raka’a biyu, wannan Sallah ta tsoro tana da wasu siffofi a wasu ruwayoyin. Allah Ya jefa tsoro a zukatan makiya suka warwatse gaba daya, daga nan Manzon Allah (SAW) ya dawo Madina.
An kira shi (wannan yaki) da wannan sunan ne saboda farfashewa da kafafun sahabbai suka yi don tafiya, an ce kuma wurin ne mai duwatsu masu mabambantan launuka, an kuma ce sunan wurin ke nan. Hakika kafin wannan yaki Annabi (SAW) ya aika wurare da yawa ana amintar da hanya da ladabtar da ’yan ta’adda da masu rarraba kan al’umma. Wannan ya faru ne a Shekara ta 7 Bayan Hijira.
Ramuwar Umara
A watan Zul-Kida na Shekara ta 7 Bayan Hijira Manzon Allah (SAW) ya shirya ya fita yin ramuwar Umarar da ba su yi ba ta dalilin sulhu, Ya wakilta Abu Zar Algifari (RA) a garin Madina sannan ya kora dabbobi 60 ya wakilta Najiya dan Jundub Al’aslami a kansu kuma ya wakilta Bishir dan Sa’ad a kan makamai, ya tafi da makamai ne a boye don taka-tsantsan da gudun yaudarar Kuraishawa. Ya yi harama a Zul-Hulaifa ya yi talbiyya Musulmi suka ci gaba da yi tare da shi. Sun yi tafiya har suka iso kwarin Ya’ajuj a nan ya aje makaman ya bar wa Awsu dan Khauli mutumin Madina tsaronsu, da mutum 200 daga sahabbai kuma suka gabaci Makka da irin makamin da matafiyi yake rikewa kamar yadda aka yi yarjejeniya. Ya shiga a kan taguwarsa yana talbiyya Musulmi na yi tare da shi dauke da makaminsu har suka shiga Harami suka fara Dawafi daga Hajarul Aswad kafadarsu ta dama a waje wanda ke nuna alamar karfi. Abdullahi dan Rawaha yana gaban Annabi (SAW) dauke da takobinsa.
Yana kirari da gargadi, su kuma mushirikai suna can zaune saman dutsen Arewacin Ka’aba suna kallo. Annabi (SAW) ya umarci Musulmi su yi sassarfa a zagaye uku na farko don mushirikai su ga karfinsu sai dai su rage a tsakanin Rukunul Yamani da Hajarul Aswad don ba su ganinsu ta wajen da yake Kudu ne.
Bayan ya gama Dawafi zagaye bakwai sai ya je ya yi Sa’ayi bakwai a tsakanin Safa da Marwa, daga nan ya yanka hadayarsa a Marwa sannan ya yi aski, su ma Musulmi haka suka aikata sannan ya aika wadansu inda aka aje makamai su je su tsare, wadancan su ma su zo su yi yankarsu, bayan nan ya zauna kwana uku a Makka kuma ya auri Maimuna ’yar Harisa wadda take mata ce ga amminsa Hamza Shugaban Shahidai, ta wakilta lamarinta ga Al’Abbas da ta sa mu wannan daukaka, shi ya daura auren dama ya yi Umararsa tun farko da aka shigo Makka. Da asubahin rana ta hudu Manzon Allah (SAW) ya bar Makka zuwa Madina bayan sun yi tafiyar mil tara daga Makka sun sauka a Sarfu, a nan ya tare da Maimuna (Allah Ya kara mata yarda), sannan ya wuce zuwa Madina yana cike da farin cikin cikar mafarkinsa da gaskata shin da Allah Ya yi. Abin mamaki a inda ya tare da Maimuna, a daidai nan wurin ta rasu bayan wasu shekaru kuma a nan aka rufe ta.
Za a iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141 ko [email protected]