Manzon Allah: Haske mai kore duhu (35)

Darasi na Arba’in da Biyu Yakin Mu’uta Mun ji a baya yadda Sharhabil ya kashe dan aiken Manzon Allah (SAW) zuwa ga Sarkin Busra, wato Alharisa dan Umair wanda a zahiri sanarwa ce ta a yi yaki. Bayan dawowarsa daga ramuwar Umara ce a (ranar) 1 ga watan Jimada Akhir shekara ta 8 Bayan Hijira […]

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (35)

Darasi na Arba’in da Biyu

Yakin Mu’uta

Mun ji a baya yadda Sharhabil ya kashe dan aiken Manzon Allah (SAW) zuwa ga Sarkin Busra, wato Alharisa dan Umair wanda a zahiri sanarwa ce ta a yi yaki.

Bayan dawowarsa daga ramuwar Umara ce a (ranar) 1 ga watan Jimada Akhir shekara ta 8 Bayan Hijira (SAW) ya shirya runduna mai yawan mayaka 3000 zuwa Mu’uta, ya shugabantar da Zaid dan Haris a kanta ya ce idan aka kashe shi Ja’afar dan Abu Dalib ya dauki tuta, shi ma idan aka kashe shi Abdullahi dan Rawaha ya dauka.

Ya yi musu wasiyya su zo masa da makashin Alharis (RA) kuma su kira mutanen zuwa Musulunci idan sun ki su yake su da sunan Allah ta hanyar Allah, su yaki wanda ya kafirce kuma kada su yi yaudara, kada su yi guluwwi. Kada su kashe yara da mata da tsofaffi da wanda ya shagaltu wurin bautarsa, kada su sare dabino ko itaciya ko rusa gini.

Ya yi wa rundunar rakiya yana karfafa su har ya kai su Saniyatul Wada’i, suka nufi Balka’a a Sham suka sauka a Mu’an can Kudancin Urdum (Jordan). A nan suka samu labarin Hirakal ya sauka a Masharif iyakar da Larabawa suke tare da mayakansa dubu 200. Sahabbai sun dan girgiza da suka ji irin wannan yawa nasu ba zato, don haka suka fara shawara cikin kwana biyu shin su sanar da Manzon Allah (SAW) ne ya karo musu mayaka ko su ci gaba kawai su yake su?

A nan sai Abdullahi dan Rawaha (RA) jagora na uku ya karfafe su ya ce shahada fa kuka fito nema, kuma mu ba muna yaki da yawa ko karfi ko yawan makamai ba ne. Muna yaki don addinin da Allah Ya karrama mu da shi, kyawawa biyu ne, wato nasara ko shahada. Take sahabbai suka ce wallahi Dan Rawaha (RA) ya fadi gaskiya. Wannan magana ita ta zaburar da sahabbai suka ji za su iya gwabzawa da wannan runduna mai karfin makamai da kwarewa da gogewa da kuma yawan gaske ta Rumawa. Rumawa sun shirya ne don abin da suka hango zai zama barazana ga daularsu mai karfin gaske, musamman yankin Sham inda ya zama kamar sabuwar cibiya ga Musulunci, kuma ga kara yaduwa da Musulunci yake yi.

Zaid ne jagora na farko yana rike da tutar Manzon Allah (SAW), kai-tsaye ya wuce gaba ya kutsa cikin sojojinsu aka fara yi masa ruwan kibiya, mashi da sarar wukake, suna yakarsa yana yakarsu, shi a wancan lokaci tuddan Aljannah kawai yake hange da korayen kyale-kyalenta, a haka har aka ci karfinsa amma yana sakin tutar kafin ta je kasa sai Ja’afar ya yi maza ya karbe. Sai ya ji dadi, murmushi cike da fuskarsa yana kallon tutar da Ja’afar ya dauka har ransa ya fita.

Ja’afar ya san wannan ce damarsa ta karshe kodai ya samu gagarumar nasara ga wannan addini na Allah, ko ya rabauta da shahada, shi ya sa ma ya ce wa Annabi (SAW) yana son tafiya wannan yaki. Ya ratsa ta cikin mayakan Rumawa babu alamar tsoro tare da shi, ratsawa irin ta mai neman shahada fiye da samun nasara. Har ma wasu baitoci yake rerawa. Su kansu Rumawan sun sha mamakinsa kai ka ce wanda yake da wata kariya duk jikinsa, tuni suka zagaye shi da suka da sara har hannunsa na dama ya cire ya mayar da tutar hannun hagu nan ma suka bi da sara suka sare hannun, sai ya saka tutar tsakanin dungunan hannayensa ya matse suka ci gaba da sukarsa ta ko’ina amma ya turje shi dai bai yarda tutar Manzon Allah (SAW) ta fadi kasa ba. A nan Abdullahi dan Rawaha ya ji karar takubba ta yawaita yana juyawa ya fahimci Ja’afar (RA) ya yi kasa sai ya taho a sukwane da sauri ya dauki tutar shi ma ya fuskanci abin da aka kaddara masa.

Abdullahi dan Umar ya ruwaito cewa, “Ina tare da Ja’afar a yakin Mu’uta sai muna nemansa, muka same shi makiya sun yi masa sara da suka fiye da casa’in a jikinsa!”

Abdullahi dan Rawaha (RA) kafin haka yaki yake sosai amma da ya karbi tutar ya san wani nauyi ya hau kansa na kiyaye abin da zai jefa mayakan Musulmi (cikin) hadari sai ya girgiza jikinsa ya ce: “Yake rayuwata! Tsoron me kike yi na ratsa hanyar zuwa Aljannah. Abin da kika dade kina buri ne, kawai ya afka kan rundunar Rumawa da karfinsa, ba don an kaddaro masa ya yi shahada ba da sai a ce ba wanda zai iya da shi, sai dai nan shi ma suka rufar masa sai da ya yi shahada! A wannan hali Manzon Allah (SAW) a can Madina yake shaida wa sahabbai an kashe Zaidu, Ja’afar ya dauka yana ta yaki har aka kashe shi, can kuma ya ce Abdullahi ya dauka shi ma an kashe shi daga nan ya sunkuyar da kansa ya dago idanunsa na kyalli ya ce dukkansu an daga da su zuwa Aljannah.

Bayan Abdullahi ya fadi tutar ba ta fadi kasa ba sai da Sabit dan Arkam (RA) ya dauke ta ya mika wa Khalid dan Walid (RA) shi kuma Khalid yana ganin bai cancanci a ba shi ita ba, tunda ga wadanda suka riga shi shiga Musulunci shi da bai dade ba? Sabit ya ce ka ga ka fi ni kwarewa, ka halarci Badar da Uhud da wasu yake-yake da aka yi. Daga nan Sabit ya nemi jin ta Sahabbai suka ce sun yarda Khalid ya zama jagora. Manzon Allah (SAW) a can Madina ya bai wa sahabban da suke tare da shi labarin jagorancin Khalid har ya kira shi da takobi daga takubban Allah!

Khalid ya ratsa cikinsu ya yi kokarin raba rundunar Musulmi rukuni-rukuni, ya ba kowane rukuni umarnin abin da za su yi, sannan ya yi kokari ya samar da wagegen fili cikin Rumawa inda ta nan Musulmi suka samu suka fice daga wurin wanda wannan dabara ce ta kwarewa wajen ceto wadanda aka rufar mawa don gudun salwanta ko hallakar da su, idan an fi su yawa sai su sake tattaruwa su hada karfi da wasu dabarun. Wuni aka yi ana yaki da yamma bangarorin kowa ya koma gefensa.

Da asuba Khalid ya shirya sojojin Musulmi rukuni-rukuni, na baya su dawo gaba sannan su koma wadansu su gabato, na dama su koma hagu haka da suke yi sai tsoro ya shiga kafirai suka dauka an karo sojojin Musulmi ne (cikin) dare, suna so su kawo hari tsoro ya hana, ga shi gwabzawar da aka yi duk yawansu Musulmi 12 suka kashe. Su kuwa ba a san adadin yawan nasu ba amma dai suna da yawa, Rumawa suka kasa zuwa inda Musulmi suke, sun dauka an shirya musu wata yaudara ce. Sai Musulmi suka matsa Mu’uta suka zauna har tsawon kwana bakwai suna rikita tunanin makiya, Rumawa suna ganin so ake a ja su wurin sahara inda ba za su iya kubuta ba a haka yakin ya tsaya.

Za a iya samun Malam Aliyu Gamawa ta +2348023893141 ko [email protected]