Manzon Allah: Haske mai kore duhu (37)
Yana haye kan taguwarsa Kaswa (SAW), Usama na bayansa Abubakar yana gefensa, shi kuma yana karanta Suratul Fathi har suka shiga Masallacin Harami ya isa Ka’aba wurin Hajrul Aswad ya yi Dawafi yana kan taguwarsa, akwai gumaka 360 a Ka’aba sai yana dangwararsu da sanda yana fadin fadar Allah: “Ka ce gaskiya ta zo karya […]
Yana haye kan taguwarsa Kaswa (SAW), Usama na bayansa Abubakar yana gefensa, shi kuma yana karanta Suratul Fathi har suka shiga Masallacin Harami ya isa Ka’aba wurin Hajrul Aswad ya yi Dawafi yana kan taguwarsa, akwai gumaka 360 a Ka’aba sai yana dangwararsu da sanda yana fadin fadar Allah: “Ka ce gaskiya ta zo karya ta lalace …”
Da ya gama Dawafi ya kira Usman dan Dalha ya karbi mabudin Ka’aba ya sa aka bude ta kuma ya sa aka fitar da gumakan da ke cikinta aka karya su, sannan ya shiga shi da Usama dan Zaid da Bilal ya rufe kofa ya fuskanci inda yake kallonsa ya yi Sallah raka’a biyu sannan ya zagaya cikinta ya yi kabbara kowace nahiya kuma ya kadaita Allah.
Ya fito ya tarar Kuraishawa sun cika Masallacin makil sai ya yi huduba mai isarwa wadda ta tattaro hukunce-hukuncen Musulunci da watsi da lamuran Jahiliyya, sannan ya tambaye su ya ce: “Ya taron Kuraishawa! Me kuke ganin ya kamata in yi da ku?” Sai suka ce, “Alheri dan uwa mai karimcin dan dan uwa mai karimci.”
Sai Manzon Allah (SAW) ya yi musu afuwa wanda ya janyo mutane da yawa suka musulunta suka rika tururuwa suna yi masa mubaya’a da hannayensu sahu-sahu.
A cikin wadanda suka musulunta a ranar akwai Abu Kuhafata, hakika Manzon Allah (SAW) ya yi farin ciki da musuluntarsa, mata ma sun yi tasu da baki a kan ba za su yi shirka ba ko sata ko zina ko kashe ’ya’yansu ko kiren karya ta hannuwansu ko kafafuwansu ko sabawa a horo da kyakkyawa, cikinsu har da Hindu matar Abu Sufyan tana dari-dari a kan abin da ta aikata.
Umar (RA) yana zaune kasa kadan daga inda Annabi (SAW) ya zauna yana amsar bai’a gare shi.
An samu wadansu mutane sun zo yin mubaya’a a kan za su yi hijira, sai Annabi (SAW) ya ce babu sauran hijira bayan Bude Makka.
An zartar wa wadansu wadanda hukuncinsu ya cancanci kisa hukunci su biyar maza hudu mace daya. Ibn Khatal da Mukaisu dan Sababah da Alharis dan Nufail ko dan Tulatil Alkhuza’i da Kuyana dan Khatal da Ummu Sa’ad baiwar Dan Khatal. Akwai wadanda suka gudu ko suka boye amma daga baya suka dawo suka musulunta.
Manzon Allah (SAW) ya shiga gidan Ummu Hani ya yi wanka kuma ya yi Sallar Walha (Duha) raka’a takwas da Azahar ta yi ya sa Bilal ya yi kiran Sallah a kan Ka’aba. Annabi (SAW) ya umarci Bilal da ya hau saman rufin Ka’aba ya kira Sallah, sannan ya hallara mutanen Makka ya yi musu jawabi, yana mai cewa: “Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ba Ya da abokin tarayya. Allah (SWT) Ya cika alkawarinSa, Ya taimaki bawanSa, Ya ci galaba a kan dukkan abokan gaba. Dukkan ayyukan alfahari da Jahiliyya na take su a karkashin tafukan kafana, illa aikin Shayar da Mahajjata da Kula da (gyaran) Dakin Ka’aba. Ya ku Kuraishawa! Duk ji da kai na zamanin Jahiliyya da alfahari da abubuwan bautarku na gargajiya yanzu sun zama tarihi. Dukkan bani Adama sun samo asali ne daga Adam, shi kuma Adam daga turbaya. Daga nan sai ya karanta wata aya a cikin Alkur’ani, inda Allah (SWT) Yake cewa: “Ya ku mutane! Lallai ne Mu, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangogi da kabilu, domin ku san juna. Lallai ne mafificinku daraja a wurin Allah, (shi ne) wanda yake mafificinku a takawa. Lallai ne, Allah Masani ne, Mai kididdigewa.” (Hujirat:13).
Manzon Allah (SAW) ya zauna a Makka kwana goma sha tara, yana sanar da mutane addini kabila-kabila da kira ga bautar Allah, ya kuma aika wuraren da manyan gumakansu uku suke a wajen garin Makka hannun wasu kabilu wato: Manat da Suwa’a da uzza ya gargadi wadanda ya tura su yi komai a natse cikin kwanciyar hankali. Sa’id dan Zaid an aike shi a watan Ramadan a kan (ya rusa) Manat tare da mutum ashirin. Amru dan Al’As a kan (ya rusa) Suwa’a a watan Ramadan da ya je ya rusa shi kuma mutanen suka musulunta ganin gazawar abin bautar nasu. Khalid dan Walid a kan Jazima an aike shi a watan Shawwal tare da mutum 350, da ya je sai ya kira su zuwa ga Musulunci suka ki sai ya yake su kuma ya kama su, ya ba da umarnin kowa ya kashe wanda ya kama. Saura sun aikata haka, amma sai Ibn Umar (RA) ya ki. Da suka dawo aka shaida wa Annabi (SAW) abin da ya faru, sai Manzon Allah (SAW) ya daga hannunsa ya ce har sau biyu “Allah na barranta gare ka a kan abin da Khalid ya aikata.” Ya kuma ji bakin cikin a kan abin da Khalid ya aikata. Shi kuma Khalid sabon shiga Musulunci a ganinsa daidai ne abin da ya yi. Manzon Allah (SAW) ya aika Aliyu (RA) da dukiya mai yawa ya sa aka biya diyya ga magadansu kuma aka biya su barnar da aka yi musu, sannan ya yi wa Khalid fada da gargadi. Kuma a hanya ya yi sa-in-sa da Abdurrahman dan Awfu kan abin da ya faru, da Manzon Allah (SAW) ya ji sai yake yi masa kashedi ya ce: “Saurara ya Khalid! Ka kyale sahabbaina, wallahi da (dutsen) Uhudu zinari ne sannan a ciyar da shi ta hanyar Allah da bai kai mudun dayansu ko rabinsa ba.”
Darasi na Arba’in da Hudu
Yakin Hunain
Bayan an gama Bude Makka kuma mutane masu yawan gaske sun musulunta kuma (Annabi SAW) ya ’yanta bayi. Manyan kabilu sun taru suka yi shawara a kan su kai wa Manzon (SAW) hari tunda ya yaki mutanensa su ma yana zuwa kansu, don haka suka yi shiri suka fita tare da matansu da ’ya’yansu da dukiyarsu. Manzon Allah (SAW) da ya ji labarin kabilar Huwazin sun hada runduna za su yake shi, sai ya fito shi ma da rundunar da ya zo da ita wurin Bude Makka mutum dubu 10 kuma ya kara samun wadansu mutum dubu biyu yawansu ya kama dubu 12. Ya wakilta Utab dan Usaid a garin Makka sannan suka tafi. Kafin su kai wani mahayi ya zo ya ba Manzon Allah (SAW) labarin irin yawan da wannan runduna take da shi, har wadansu suka ce ba za su yi galaba ba a yau.
A dare na goma ga watan Shawwal shekara ta 8 Bayan Hijira Manzon Allah (SAW) suka shiga kwarin Hunain, ya ba Aliyu dan Abu Dalib (RA) tutar muhajirai, ta Awsu ya ba Usaid dan Hudair, ta Khazraj ya ba Habbab dan Munzir, sannan sauran kabilun kowane aka ba da tasu. Su kuma Huwazin shugabansu Malik dan Auf An-Nadri yake jagorantarsu tare da Banu Sakif da Banu Jusham da Banu Sa’id dan Bakri da sashen wadansu mutane daga Banu Hilal da Banu Amru da Awfu dan Amir.
Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ta +2348023893141 ko imel:[email protected]