Manzon Allah: Haske mai kore duhu (41)
Manzon Allah (SAW) ya sanar da Huzaifa sunayen ko su wane ne da abin da suka zo yi, shi ne ya sa ake kiran Huzaifa da ‘Sahibus-Sirrin-Nabiyyi’ wato Ma’abocin Sirrin Annabi (SAW). Da Usaid ya ji ya tunzura har ya nemi a bar shi ya kashe su, sai Manzon Allah (SAW) ya hana shi, ya […]
Manzon Allah (SAW) ya sanar da Huzaifa sunayen ko su wane ne da abin da suka zo yi, shi ne ya sa ake kiran Huzaifa da ‘Sahibus-Sirrin-Nabiyyi’ wato Ma’abocin Sirrin Annabi (SAW). Da Usaid ya ji ya tunzura har ya nemi a bar shi ya kashe su, sai Manzon Allah (SAW) ya hana shi, ya ce za a ce bayan na yi yaki da mushirikai yanzu na dawo kan mabiyana, tunda suna furta kalmar shahada dole in kyale su.
Munafukai sun gina wani masallaci don kafirci da cutar da Musulmi da kawo rarrabuwarsu, suka aika wa Annabi (SAW) kafin wannan tafiya, kan ya zo ya yi Sallah tare da su a cikinsa a daidai lokacin da yake shirin fita. Sai ya ce musu yana kan hanyarsa ta tafiya, su bari ya dawo idan Allah Ya yarda. A yayin dawowar ce ya rage sauran tafiyar yini daya, sai Jibril (AS) ya sauko ya zo masa da labarin masallacin, sai ya aika aka kone shi aka rusa.
Wadanda ba su je yaki ba munafukan cikinsu sun zo suna rantse-rantsen karya sai Manzon Allah (SAW) ya bar wannan sirri a hannun Allah. An samu wadansu mutum uku muminai masu gaskiya da suka zo suka tabbatar ba su da uzurin da ya hana su tafiya. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce su jira har sai Allah Ya yi musu hukunci, an umarci Musulmi da kada wanda ya yi musu magana, mutanen su ne: Ka’ab dan Malik da Murarah dan Rabi’a da Hilal dan Umayyah. Ai kuwa mutane suka canja musu babu mai yi musu magana balle wata mu’amala wannan ya sa kasa ta yi musu kunci, duniyar ta yi musu duhu ransu ya kuntata. Sun wanzu cikin kuncin har kwana arba’in sai kuma aka kara musu wani kuncin cewa kada su kusanci matansu, haka suka zauna cikin damuwa har sai da suka cika kwana hamsin sannan Allah Ya saukar da ayar amsar tubarsu a cikin Suratut Tauba: “Kuma (Allah) Ya karbi tuba a kan ukun nan wadanda aka jinkirtar har kasa da yalwarta ta yi kunci a kansu, kuma rayukansu suka yi kunci a kansu, kuma suka tabbatar babu wata mafaka daga Allah face (komawa) zuwa gare Shi. Sa’an nan Allah Ya karbi tubarsu, domin su tabbata a kan tuba. Lallai Allah ne Mai karbar tuba, Mai jinkai. (Tauba:118).
Musulmi sun yi farin ciki da wannan kuma suka yi musu bushara, an gaskata su, su kuma sun yi farin ciki inda suke ganin ita ce mafi sa’adar rana a rayuwarsu, an saukar da wasu ayoyi wadanda suka bayyanar da sirrin karyar munafukai. Manzon Allah (SAW) ya dawo daga Tabuka ne a watan Rajab shekara ta 9 Bayan Hijira.
Sarkin Habasha Najjashi kuma ya rasu a wannan wata, Annabi (SAW) ya yi masa Sallah, ita ce ‘Sallar Ga’ib’ ga wanda baya nan. A watan Sha’aban kuma Ummu Kulsum ta rasu (Allah Ya kara mata yarda). Manzon Allah (SAW) ya sallace ta kuma ya rufe ta a Baki’a, hakika ya yi bakin ciki kwarai a kan rashinta. Ya ce ga Usman (RA) “Da ina da ’ya ta uku lallai da na aura maka.” A dai wannan shekarar ce a watan Zul-Kida shugaban munafukai Abdullahi dan Ubayyu ya rasu dansa wanda yake Musulmi ne ya nemi Manzon Allah (SAW) ya yi masa Sallah. Umar (RA) ya yi kokarin ganin ba a sallace shi ba, amma kwadayin musuluntar mutanensa ya sa Manzon Allah (SAW) ya sallace shi, sai aka saukar da ayar hanin Sallah a kan munafuki idan ya rasu.
Darasi na Arba’in da Bakwai
Abubakar Assiddik (RA) ya jagoranci Musulmi a Hajji
Larabawa sun kasance suna yin aikin Hajji duk shekara kuma suna ba shi muhimmanci kwarai, suna dauka cewa a kan addinin Annabi Ibrahim (AS) suke wanda tuni canje-canje da bidi’o’i da shirka suka shiga cikinsa dumu-dumu.
Lokacin da Annabi (SAW) ya Bude Makka ya wakilta Uttab dan Usaid a kanta, sai ya yi aikin Hajji tare da Musulmi har da mushirikai, yanzu da shekara ta zagayo Manzon Allah (SAW) ya tura Abubakar (RA) ya jagoranci Musulmi su yi irin wadda Musulunci ya koyar. Abubakar ya taho da dabba ashirin na hadayar Manzon Allah (SAW) nasa kuma guda biyar, ya fita tare da Musulmi dari uku daga Madina suka nufi Makka a farko farkon Zul-KIda shekara ta 9 Bayan Hijira.
Bayan sun tafi ne sai farkon-farkon Suratul Bara’a ya sauka a kan a yi watsi da mushirikai wadanda suka ki cika alkawarinsu da wadanda ba a yi kulli da su ba, kuma a ba su lokaci tsawon wata hudu su yi abin da za su iya a cikinsa kafin su san ba su iya gajiyar da Allah ba, kuma Allah Mai kaskanta kafirai ne. Haka nan kuma da umarni kan a cika wa mushirikai wadanda ba su warware alkawarinsu ba kuma ba su yi fito-na-fito da Musulmi ba lokacinsu. Manzon Allah (SAW) ya aika Aliyu (RA) ya isar da wannan sako ga mahajjata Ranar Hajji Babba, ya riski Abubakar (RA) a Dujana ko Urju, sai Abubakar (RA) ya ce mai umarni ko wanda ake umurta? Sai ya ce wanda ake umarta kuma ya kasance yana Sallah a bayan Abubakar (RA). Abubakar ya tsayar wa mutane a kan Hajjinsu, a Ranar Yanka, Aliyu (RA) ya tsaya wurin Jamra ya karanta wa mutane farkon Suratul Bara’a na alkawura da ba da lokaci da cikawa. Bayan nan sai Abubakar (RA) ya tura wadansu mutane suka yi shela cewa daga wannan shekarar kada wani mushiriki ya sake yin Hajji kuma kada wanda ya kara Dawafin Daki (Ka’aba) tsirara.
Darasi na Arba’in da Takwas
Zuwan jama’a-jama’a wurin Annabi (SAW)
1- Ayarin Tujaib
Wani reshe ne na Banu Kinda, lokacin da suka zo wurin Manzon Allah (SAW) da suka gabatar da sadakokin mutanensu da abin da yake da fifiko a matalautansu, hakika ya yi farin cikin zuwansu, ya karrama su. Abubakar (RA) ya ce babu wadansu Larabawan da suka gabato mu kamar wadannan. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai shiriya ta Allah ce wanda Yake nufinsa da alheri sai Ya yalwata kirjinsa.”
Sun kasance suna tambaya game da Alkur’ani ne da kuma sanin Sunnah. Da za su koma Manzon Allah (SAW) ya saka musu da mafi kyan abin da ake ba ayarin jama’a. Akwai wani yaro a cikinsu wanda ya nemi Manzon Allah (SAW) ya roka masa gafara da jinkai da samun wadatar zuci. Ya roka masa sai ya zama mafi kamewar mutanensa. Bayan rasuwar Manzon Allah (SAW) wadansu sababbin shiga Musulunci da wadanda suka shiga don kada su ba da Jizya ko wata manufa sun yi ridda, amma shi Allah Ya tabbatar da shi ya rika yi wa mutanensa wa’azi sai ba su yi ridda ba.
Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ta +2348023893141 ko imel:[email protected]