Manzon Allah: Haske mai kore duhu (42)

2- Ayarin Fuzarah Wannan ayari sun zo ne bayan Manzon Allah (SAW) ya dawo daga Tabuka su wajen goma sha wani abu ne, sun yi ikirari da Musuluncinsu. Manzon Allah (SAW) ya tambaye su game da garuruwansu, sai suka yi kukan farin da ke addabarsu suka ce “Ka roka mana Allah Ya ba mu ruwa […]

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (42)
Manzon Allah: Haske mai kore duhu (42)

2- Ayarin Fuzarah

Wannan ayari sun zo ne bayan Manzon Allah (SAW) ya dawo daga Tabuka su wajen goma sha wani abu ne, sun yi ikirari da Musuluncinsu. Manzon Allah (SAW) ya tambaye su game da garuruwansu, sai suka yi kukan farin da ke addabarsu suka ce “Ka roka mana Allah Ya ba mu ruwa ka nemar mana ceton Ubangijinka don ya nema mana cetonka. A nan ne Manzon Allah (SAW) ya tabbatar musu Allah kadai ake neman ceto a wurinSa, Shi ba ya nema a wurin kowa! Shi ne abin bautar da babu wani abin bauta sai Shi, Mai girma da Daukaka. Ya hau kan munbari ya roki Allah har sai da aka saukar musu da ruwa mai yawan gaske.

3- Ayarin Najran

Wani yanki ne da ya yi iyaka da Yamen kuma babban yanki ne yana da alkaryu 73. Suna da mayaka dubu 100, kuma suna kan addinin Nasara ne. Manzon Allah (SAW) ya aika musu da wasika yana kiransu zuwa ga Musulunci, sai suka hadu suka yi shawarar su aiki ayari ya je wurinsa a magance matsalar. Da suka zo suna sanye da kayan kawa na alfahari da alharini da zobban zinari. Manzon Allah (SAW) bai yi musu magana ba sai wadansu manyan sahabbai suka yi musu ishara da su je su cire zobban da kambunan, sai suka aikata. Sannan ya yi musu magana ya kira su zuwa ga Musulunci amma suka ki karba suka ce mu masu mika wuya ne gabaninku. Sai ya ce musu Musulunci ai ya hana muku abubuwa uku:

-Bautar kuros (gicciye).

-Cin naman alade.

-Riyawar da kuke yi cewa Allah yana da da.

Sai suka ce to wane ne misalin Isah? Sai Allah Ya saukar da wannan ayar a cikin Ali Imran: “Lallai misalin Isa a wurin Allah kamar Adamu ne, an halitta shi daga turbaya, sa’annan aka ce masa ‘kasance’ sai ya kasance.” (Ali Imran: 59).

Bayan ya karanta musu har zuwa aya ta 61 sai ya nemi su zo a yi mubahala a ga mai gaskiya a cikinsu. Suna jin haka suka nemi ya dan ba su lokaci sai suka kebe suna shawara, suka ce tabbas idan har Annabi ne kuma muka yi to babu wanda zai saura cikinmu sai ya hallaka, daga nan suka amince su dai rika bayar da Jizya. Aka yarje musu kuma aka rubuta a rubuce kullin zaman amana da ’yancin yin bautarsu. Sai suka ce, to, ka aika wani amintacce tare da mu. Sai Manzon Allah (SAW) ya aika Abu Ubaida Amir dan Jarrah (RA), shi ne ya sa ake kiransa da Amintaccen Wannan Al’umma.

4- Ayarin Da’ifa

Ya gabata an tsare mutanen Da’ifa bayan gama Yakin Hunain inda suka ki fitowa a yi yaki, a karshe aka yanke shawarar a kyale su. Lokacin da Musulmi suke komawa ne Urwa dan Mas’ud Assakafi ya bi sawun Manzon Allah (SAW) kuma ya riske shi kafin ya shiga Madina, ya Musulunta sannan ya koma ga mutanensa, sun nuna kamar suna sonsa daga baya suka harbe shi ya rasu.

Wannan aika-aikar ta hana su kwanciyar hankali suna tsoron a kawo musu hari, sai suka aiko Abdulyalil da wadansu mutum biyar daga madaukakansu.

Manzon Allah (SAW) ya saukar da su kusa da masallaci suna jin karatun Alkur’ani kuma suna ganin ana yin Sallah, a cikin kwanukan da suka yi Manzon Allah (SAW) ya kira su zuwa ga Musulunci ba su dai musulunta ba sai daga baya suka nemi Manzon Allah (SAW) ya yi musu rangwame a kan wasu abubuwa, ma’ana a bar su su rika aikata su: su ne shan giya da zina da cin riba. Kuma kada ya sa su rusa babban gunkinsu Lata kuma ya yafe musu yin Sallah kuma kada ya sa su rusa gumakansu da hannuwansu. Sai Manzon Allah (SAW) ya ki amma ya yarda kada su rusa gumakan da kansu. Sun musulunta Usman dan Al-As shi ne dan karaminsu ya kasance ya koyi karatun Alkur’ani a wurin Annabi (SAW), idan ya same shi yana barci sai Abubakar (RA) ya karantar da shi kuma ya boye haka ga mutanensa a haka ya haddace wani abu mai yawa. Da suka musulunta sai Manzon Allah (SAW) ya wakilta shi a kansu saboda kwadayinsa ga karatun Alkur’ani da neman ilimin addini.

Bayan ayarin ya koma sai suka boye imaninsu gudun yaki, suka shaida wa mutanensu cewa sun hadu da kausasawa da takobi a fili, suka fadi sharuddan da aka yi musu da hanin giya da zina da sauransu ko kuma a yake su. Da suka ji haka sai suka shiga shirin yaki cikin kwana biyu ko uku sai dai ko’ina ba su kai ba Allah Ya jefa tsoro a zukatansu suka ce wa ayarin ku koma ku ce mun yarda da abin da ya yi umarni kuma mun mika wuya. Sai mutanen suka ce musu ai mun gama komai dama mun musulunta, daga nan duk Sakifawa suka musulunta.

Manzon Allah (SAW) ya aika Khalid dan Walid da Mughira dan Shu’uba Assakafi da wadansu mutane zuwa Da’ifa su rusa Allata, suka je suka rusa ta da gininta.

5- Ayarin Banu Amir

Su uku ne suka zo wurin Manzon Allah (SAW) kuma su ne shugabannin mutanensu kuma shaidanun mutanen, kuma su ne dai suka yaudari sahabbai a Bi’iri Ma’unah. su ne: Amir dan Dufail da Urbad dan Kais da Jabir dan Aslam.

Sun zo ne da nufin kashe Manzon Allah (SAW) da suka zo wurinsa ya kira su zuwa Musulunci, sai Amir ya ce: “Ina ba ka zabi cikin abu uku: Mutanen Sahlu su zama naka ni kuma mutanen Mudar. Ko in zamo Khalifa a bayanka. Ko in yake ka ni da Gadafan.” Sai Manzon Allah (SAW) ya kore dukkan wadannan ya ce: “Ya Allah! Ka isar mini ga Amir kuma Ka shiryar da mutanensa.” Bayan su Amir sun juya kan hanyarsu ta komawa ya sauka gidan wata ’yar uwarsa, Allah Ya aiko masa da annoba ya fara kwara amai, ya sa aka kawo masa dokinsa ya hau ke nan ya mutu a kansa. Shi kuma Urbad tsawa ta kona su shi da rakuminsa, shi ne fadar Allah: “Kuma aradu tana tasbihi game da gode maSa, da mala’iku domin tsoronSa. Kuma Yana aiko tsawarwaki, sa’annan Ya samu wanda Yake so da su, alhali kuwa su, suna jayayya a cikin (al’amarin) Allah, kuma Shi ne mai tsananin (shirya) hila.” (Ra’ad: 13).

Mu’ila dan Jamil shi ma dan kabilarsu ce kuma ya ruwaito wannan kissar ya je wurin Manzon Allah (SAW) ya musulunta yana dan shekara ashirin ya yi mubaya’a ya mika masa rakuminsa, ya rayu tsawon shekara dari a Musulunci ana kiransa da ma’abocin harshe biyu saboda fasaharsa.

6- Ayarin Banu Hanifa

Sun zo Madina su goma sha bakwai a cikinsu akwai Musailamatul Kazzab, sun sauka gidan wani mutum sannan suka zo suka musulunta. An ce har da Musailama, a wata ruwayar kuma an ce bai je ba, ya ce sai idan Manzon Allah (SAW) ya yarda ya zama Khalifa a bayansa. Da ma Manzon Allah (SAW) an nuna masa a mafarki fitowar makaryata a bayansa. Da Musailama ya gabato wurinsa yana rike da gutsuren ganyen dabino a hannunsa, ya tsaya cikin sahabbai. Bayan Manzon Allah (SAW) ya yi magana sai Musailama ya ce: “Idan ka so ka bar wannan lamarin tsakaninka da mu, kuma ka sanya shi gare mu bayanka.”

Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ta +2348023893141 ko imel:[email protected]