Manzon Allah: Haske mai kore duhu (45)
Hakika Suratun Nasri ta sauka a cikin tsakiyar wadannan kwanuka. A rana ta uku bayan jifar jamrori ya bar Mina sun sauka a Abtahu suka yi Sallar Azahar da La’asar da Magariba da Isha’i, sannan ya umarci A’isha (RA) tare da dan uwanta Abdurrahman dan Abubakar (RA) ya rakata ta yi harama a Tan’im saboda […]
Hakika Suratun Nasri ta sauka a cikin tsakiyar wadannan kwanuka. A rana ta uku bayan jifar jamrori ya bar Mina sun sauka a Abtahu suka yi Sallar Azahar da La’asar da Magariba da Isha’i, sannan ya umarci A’isha (RA) tare da dan uwanta Abdurrahman dan Abubakar (RA) ya rakata ta yi harama a Tan’im saboda ta rama Umarar da ta kubuce mata saboda haila da ta zo mata gabanin ta yi. Bayan sun dawo ya ba da umarnin tafiya.
Ya hau dabbarsa suka tafi Ka’aba ya yi Dawafin Ban-Kwana, ya yi Sallar Asuba suka fita ta can kasan Makka sannan suka nufi Madina.
Da suka kusa Madina ya yi kabbara uku kuma ya karanta La’ilaha illallahu wahdahu la sharikalahu lahul mulku walahul hamd…har zuwa “Wahazamal ahzaba wahada.”
Darasi na Hamsin
Aika Usamah dan Zaid
Manzon Allah (SAW) ya zauna a Madina bayan dawowarsa daga aikin Hajji cikin tasbihi da gode wa Allah a kan abin da Ya nuna masa na shigar mutane addinin Musulunci kungiya-kungiya, wanda samun nasara ce ga da’awarsa ta tsawon shekara ashirin da uku.
Jakadoji sun ci gaba da kwararowa a wannan lokaci daga wurare masu yawa Manzon Allah (SAW) yana fuskantarsu da yi musu kyauta idan za su koma.
Ya shirya Usama dan Zaid (RA) tare da mayaka 700 zuwa Balka’a da Darum cikin kasar Falasdinu inda aka yi Yakin Mu’uta da aka kashe mahifinsa. Bayan sun tafi sun sauka a Jurfu kimanin mil uku daga Madina a nan ne aka zo masa da labari mai sanya damuwa na rashin lafiyar Manzon Allah (SAW). Da jin haka sai ya dan dakata har ya ji samun saukinsa, sai dai ba haka Allah Ya hukunta ba.
Manzon Allah (SAW) ya isar da manzanci, ya mayar da kayan amana ga masu su wanda a nan aka rika tsinkayar barinsa duniya ya kusa ta hanyar ayyukansa da maganganunsa. Manzon Allah (SAW) ya yi ittikafi na kwana 20 a watan Ramadan din shekara ta 10 Bayan Hijira, kuma Mala’ika Jibril (AS) ya bijiro masa da karatun Alkur’ani sau biyu sabanin yadda ya saba yi sau daya. A kan haka yake ce wa Fatima (RA): “Ba na ganin haka sai ajalina ne ya kusanto.” Lokacin da yake ban-kwana da Mu’az dan Jabal (RA) da zai tafi Yamen ya yi masa wasiyya ya ce: “Ya kai Mu’az! Lallai kai da kyar ne za ka same ni bayan wannan shekara tawa, me yiwuwa ma ka wuce ta wannan masallaci da kabarina.” A nan sai Mu’az ya shiga kuka mai tsanani saboda rabuwa da Manzon Allah (SAW).
Darasi na Hamsin da Daya:
Jinyar Manzon Allah da wafatinsa da jana’izarsa (SAW):
A farko-farkon watan Safar na shekara ta 11 Bayan Hijira, Manzon Allah (SAW) ya fita zuwa Uhud ya ziyarci shahidanta bayan ya dawo ya hau munbari ya ce: “Na kubuce muku kuma ni mai shaida ne a kanku kuma lallai ni ina ganin tafkina a yanzu kuma hakika an ba ni mabudan taskokin kasa ko mabudan kasa kuma ni wallahi ba na jiye muku tsoron ku yi shirka a bayana, sai dai ina jiye muku tsoron ku rika fitina a cikinta!”
A karshe-karshen watan Safar din ne kuma ya tafi Makabartar Baki’a da dare ya nema musu gafara.
Ranar Litinin din karshen watan Safar ne ya halarci wata jana’iza a Baki’a da ya dawo sai ya samu A’isha (RA) tana ciwon kai tana cewa “Oh kaina! Sai ya ce “Wallahi ni ne dai kaina yake ciwo, me zai cutar da ke idan kin rasu gabanina? Sai in wanke ki in sanya miki likkafani, in yi miki Sallah kuma in rufe ki.” Ta ce sai na ba shi amsa: “Na rantse da haka za ta faru idan ka dawo daga janazata wani aure za ka yi. A nan ne Manzon Allah (SAW) ya yi murmushi kuma a nan take ciwon ajalinsa ya fara.” (Ahmad da Ibn Majah).
Ya dauki wata uku yana kwance cikin jinya, wadda kuma sannu a hankali sai kara ta’azzara take yi. Da ma kuma jinyar annabawa mai tsanani ce, kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake cewa “Mu annabawa ladarmu ninki biyu ne, don haka kuma tsananin jinyarmu ma mai nauyi ne.”
A cikin tsawon wannan lokaci da Annabi (SAW) ya yi a kwance, ana zagayawa da shi tsakanin dakunan matansa. Ana nan har al’amari ya tsananta ga Manzon Allah (SAW), ya kai ba ya iya fita masallaci don jan mutane Sallah. Kuma Annabi (SAW) ya nemi izini daga sauran matansa na su amince masa ya yi jinya a dakin Sayyidatuna A’shatu (RA), maimakon zazzagayawa da shi a tsakanin gidajen sauran matansa, kuma suka amince. A nan Abbas da Aliyu (RA) suka kama shi yana tsakaninsu kafafunsa na jan kasa har ya kai dakin A’isha (RA).
A wannan ranar ya fita kuma ya ja mutane Sallah bayan an idar ya yi musu huduba a cikin abin da ya fada akwai: “Lallai wadanda suka gabace ku sun kasance suna rikar kaburburan annabawansu da salihan bayinsu masallatai. Ku saurara! Kada ku riki kaburbura wurin bauta, lallai ni na hane ku daga aikata haka.” Kuma ya ce: “Allah Ya la’anci Yahudu da Nasara da suke rikar kaburburan annabawansu wurin bauta.”Kuma ya ce: “Kada ku riki kabarina wani gunki da ake bauta mawa.” Kuma ya yi wasiyya da Ansarawa mutanen Madina da a mu’amalance su da alheri sannan ya ce: “Lallai bawa Allah ya ba shi zabi tsakanin ya bar shi a duniya yadda ya so ko ya ba shi abin da yake a wurinSa, sai (bawan Annabi) ya zabi abin da yake wurinSa (Allah).” Sa’idul Khudri ya ce sai Abubakar (RA) ya kama kuka ya ce iyayenmu maza da mata fansa gare ka ya Manzon Allah! Sai mutane suka ce dubi wannan tsohon, Manzon Allah (SAW) yana cewa an ba shi duniya da Lahira shi kuma yana cewa ya ba da fansar iyayenmu. Manzon Allah (SAW) ya kasance shi aka ba zabi, kuma Abubakar shi ne mafi saninmu.
Manzon Allah (SAW) ya yabi Abubakar (RA) kuma ya yi umarni da a rufe dukkan kofofin masallacinsa amma ban da kofar Abubakar. Wannan duk ya faru ne a ranar Laraba. A ranar Alhamis ciwonsa ya kara tsananta kwarai ga sahabbai sun taru wurinsu su ji wasiyya daga Manzon Allah (SAW), sai ya ce su kawo takarda ya rubuta musu abin da ba za su bata ba a bayansa.
Umar (RA) ganin irin radadin ciwon da Manzon Allah (SAW) yake ji kasantuwar ana rubanya wa annabawa zafin ciwo, sai ya ce hakika ciwo ya rinjaye shi, kuma kuna da Littafin Allah, Littafin Allah ya ishe ku. A nan sai mutane suka yi sabani, wadansu suka ce a dauko wadansu su ce a bar Annabi (SAW) ya huta. Da ka-ce-na-ce ta yawaita, sai Manzon Allah (SAW) ya ce “Ku tashi daga wurina!”
A dai wannan ranar ya yi wata wasiyyar cewa a fitar da Yahudawa da Nasara da mushirikai daga Tsibirin Larabawa. Kuma a rika ba da kyauta ga ayarorin masu zuwa kamar yadda yake saka musu. Ya karfafa wa mutane game da al’amarin Sallah da abin da hannun damansu ya mallaka wato bayi sannan ya ce “Na bar muku al’amurra biyu wadanda ba za ku taba bata ba matukar kun yi riko da su: “LITTAFIN ALLAH DA SUNNATA.” Yayin da zafin zazzabi ya yi tsanani a jikin Manzon Allah (SAW) sai iyalansa su kawo ruwan sanyi kusa da shi, yana sanya hannunsa a ciki.
Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ta +2348023893141 ko imel:[email protected]