Manzon Allah: Haske mai kore duhu (47)

Allahu Akbar! A yau muke kawo karshen tarihin rayuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da dan uwa Malam Aliyu Gamawa ya tsakuro ya wallafa. Mu yi nutso, mun kamfato wani abu daga rayuwar Annabi (SAW), wanda ba a haifi kamarsa ba kuma ba za a haifa ba. Ba karshen littafin ba ke nan, a’a akwai […]

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (47)
Manzon Allah: Haske mai kore duhu (47)

Allahu Akbar! A yau muke kawo karshen tarihin rayuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) da dan uwa Malam Aliyu Gamawa ya tsakuro ya wallafa. Mu yi nutso, mun kamfato wani abu daga rayuwar Annabi (SAW), wanda ba a haifi kamarsa ba kuma ba za a haifa ba. Ba karshen littafin ba ke nan, a’a akwai bangaren da ya tabo matsayin halaye da dabi’u da mu’ujizojinsa da sauransu da insha Allah wani lokaci za mu tabo su. Allah Ya sa mun amfana da abin da muka karanta, tare da fatar za mu rika dabbaka darussan da ke cikin wannan littafi.

Abubakar (RA) ya kasance shi ne yake wakiltar Annabi (SAW) a wajen gabatar da Sallah kuma ya shagaltu matuka wajen al’amarin jinyar Manzon Allah (SAW). Saboda haka ba ya samun lokaci don ziyartar matarsa da ke wani kauye a wajen Madina. Wata rana sai ya yanke hukuncin kai ziyara ga matar tasa don ganin halin da suke ciki. Bayan ya samu kai ziyarar dawowarsa cikin garin Madina ke da wuya sai ya tarar da gidan Manzon Allah (SAW) a cikin rudani. Muminai sun taru a Masallacin Manzon Allah (SAW) suna ta rusa kuka, an shiga cikin dimuwa da firgici. A nasa bangaren kuma Umar Ibn Khaddab (RA) ya fito da takobi yana cewa duk wadda ya sake furta cewa Manzon Allah (SAW) ya mutu zai fille masa kai. Wato dai Abubakar (RA) ya tarar Annabi (SAW), babban abokinsa, shugabansa kuma makusancinsa ya bar duniya. Sannan ya tarar mutane sun shiga rudu da dimuwa, babu wanda ya san abin da zai yi a wannan lokaci. Daga nan sai ya karasa cikin gidan Manzon Allah (SAW) ya nemi ganin Manzon Allah, kuma A’isha (RA) ta bude masa fuskar fiyayyen halitta ya yi mata duba ta karshe, ya sumbace ta, sannan aka rufe ta. Bayan ya tabbatar da cewa Manzon Allah (SAW) ya koma ga Ubangijinsa, sai ya fito zuwa ga mutane sannan ya ja hankalinsu da cewa duk wanda yake bauta wa (Annabi) Muhammad, to hakika (Annabi) Muhammad (SAW) ya rasu, wanda kuma yake bauta wa Allah to Allah Rayayye ne ba Ya mutuwa. Daga nan sai ya karanta musu ayar Alkur’ani cikin Suratu Ali Imrana, inda Allah (SWT) Yake cewa: “Kuma Muhammadu bai zama ba face Manzon (Allah), lallai manzanni sun shude a gabaninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, za ku juya a kan duga-duganku? To wanda ya juya a kan duddugensa ba zai cuci Allah da komai ba. Kuma Allah zai saka wa masu godiya.  Kuma ba ya yiwuwa ga wani rai ya mutu face da izinin Allah. Wa’adi ne mai kayadadjjen ajali. Kuma wanda yake nufin sakamakon duniya Muna ba shi daga gare ta. Kuma wanda yake nufin sakamakon Lahira Muna ba shi daga gare ta. Kuma za Mu saka wa masu godiya.” (K:3:144-145).

Jin wadannan ayoyi ke da wuya sai Umar dan Khaddab (R.A) ya dawo cikin hayyacinsa sannan aka samu natsuwa, muminai suka dauki kaddara suka amince da hukuncin Allah.

Darasi na Hamsin da Biyu

Sanin Matsayin Manzon Allah (SAW)

A cikin wannan fasali mun dan tsakuro wasu daga cikin darajojin da Ubangijinmu Madaukakin Sarki ya ba Manzon Allah a cikin Alkur’ani.

  1. Manzon Allah Allah (SAW) fitila ne kamar yadda Allah Ya kira shi da kanSa: “Ya kai Annabi! Lallai Mu, Mun aike ka kana mai shaida, kuma mai bayar da bushara kuma mai gargadi. Kuma mai kira zuwa ga Allah da izininSa, kuma fitila mai haskakawa.” (Suratul Ahzab 45-46).
  2. Manzon Allah haske ne: “Ya ku Mutanen Littafi! Lallai ne, ManzonMu ya je muku, yana bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kuna boyewa daga Littafi, kuma yana rangwame daga abu mai yawa. Hakika wani haske da wani Littafi mai bayyanawa ya je muku daga Allah. Da shi Allah Yana shiryar da wanda ya bi yardarSa zuwa ga aminci, kuma Yana fitar da su daga duffai zuwa ga haske da izininSa,kuma Yana shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.” (Suratul Ma’ida:15-16)
  3. Kuma kafin Allah (SWT) Ya aiko shi sai da Ya wanke masa kirjinsa, Ya dauke masa jin nauyin wahalar kira zuwa ga addini, sannan Ya daukaka ambatonsa. (Suratus Sharhi 1-8).
  4. Allah da kanSa ne Ya fara yi wa Manzon Allah salati, sannan Mala’ikunSa. Bayan haka ne Ya ce mu ma mu sa baki a cikin wannan aiki mai albarka. (Suratu Ahzabi:56).
  5. Babu wani mahaluki da Allah Ya rantse da rayuwarsa in ba Manzon Allah ba. Kamar yadda Ibn Abbas (RA) ya fada (a tafsirin Suratul Hijri: 72)
  6. A suratud Duha kuma Ya rantse cewa bai fita batunsa ba kamar yadda wadansu suka zata saboda jinkirin wahayi da aka samu. (Suratud Duha: 1-3).
  7. A Suratun Najmi Allah Ya rantse don kare Annabinsa daga kasancewa a kan bata ko furuci da son zuciya kamar yadda mushrikai suke rayawa. (Suratu Najmi: 1-5).
  8. A Suratu Yasin, Allah Ya rantse da Alkur’ani cewa Annabi Muhammadu (SAW) yana cikin Manzanni. (Suratu Yasin: 1-3).
  9. Kai, ba wata addu’a da Manzon Allah ya daga hannunsa ya yi zuwa ga Allah face Allah Ya yi gaggawar karba masa. Wani lokacin ma idan ya yi fata tun bai roka ba Yake ba shi, kamar yadda ya faru ga labarin sauya alkibla, inda Madaukakin Sarki Ya ce:

“Hakika Muna ganin jujjuyawar fuskarka zuwa sama. To, za mu juyar da kai zuwa ga alkiblar da kake so. To ka juyar da fuskarka zuwa Masallaci Mai alfarma…” (Suratul Bakara: 144)

Wane Annabi ne ya fi?

Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana mana darajar Annabawa a matsayinsu na fiyayyu kuma zababbu a cikin bayinSa. Sannan Ya bayyana fifikon Manzanni a kan Annabawa wadanda adadinsu yana da yawan gaske, kuma Allah ne kadai Ya san yawansu. (Majmu’ul Fatawa Ibn Bazz, 2/66-67). Sai kuma fiffikon Ulul Azmi guda biyar a kan sauran Manzanni, su ne: Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa da Muhammad (SAW) Amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya. Wannan kuwa abu ne da ya fi karfin a bukaci kafa masa dalili. Amma dai ga wasu daga cikinsu:

“Ka tuna lokacin da Muka riki alkawari daga Annabawa, da kuma wurinka da wurin Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa dan Maryam, muka rika daga gare su alkawari mai girma.” (Suratul Ahzab: 7)

Allah Ya aiko Annabawa zuwa ga jama’arsu ne kawai. Nuhu zuwa ga mutanensa, Hudu zuwa ga Adawa, Salihu zuwa ga Samudawa, Shu’aibu zuwa ga Madyana da sauransu. Duk a cikin Manzanni ba wanda aka aiko shi ga duniya baki daya sai Annabi Muhammad (SAW). Allah (SWT) Ya ce, “Ka ce, ya ku mutane! Hakika ni, Manzon Allah ne zuwa gare ku gaba daya…” (Suratul A’raf: 158)

Kuma an aiko shi ne don ya zama rahama ga kowa da kowa: “Ba Mu aiko ka ba face rahama ga talikai.” (Suratul Anbiya’:107)

Wadannan dalilai da ire-irensu masu tarin yawa sun tabbatar cewa, Manzon Allah (SAW), Cikamakin Annabawa, shi ne limaminsu kuma shugabansu, sannan mafifici a cikinsu. Kuma da bakinsa mafi tsarki da albarka ya fada cewa: “Ni ne shugaban mutane Ranar Alkiyama…” (Sahihul Bukhari, Hadisi na 4435 da Sahih Muslim, Hadisi na 287 daga Abu Huraira (RA).

Ya Allah! Muna godiya da Ka sa mu cikin al’umarsa. Ya Allah! Ka sanya mu cikin cetonsa.

Za a iya samun Ustaz Aliyu Muhammad Sa’id Gamawa ta +2348023893141 ko imel:[email protected]