Manzon Allah: Haske mai kore duhu (5)

Mako huDu da suka gabata ne muka fara kawo muku tarihin Manzon Allah (SAW) daga littafin TARIHIN FARIN JAKADA na Ustaz Aliyu Sa’idu Gamawa. Yau za mu Dora daga inda muka tsaya game da salsalarsa (SAW) kamar haka: Amma an tabbatar da cewa Adnan shi ne jika na 38 ga Annabi Isma’il (AS) Dan Annabi […]

Manzon Allah: Haske mai kore duhu (5)
Manzon Allah: Haske mai kore duhu (5)

Mako huDu da suka gabata ne muka fara kawo muku tarihin Manzon Allah (SAW) daga littafin TARIHIN FARIN JAKADA na Ustaz Aliyu Sa’idu Gamawa. Yau za mu Dora daga inda muka tsaya game da salsalarsa (SAW) kamar haka:

Amma an tabbatar da cewa Adnan shi ne jika na 38 ga Annabi Isma’il (AS) Dan Annabi Ibrahim Khalilullah (AS). Ibn Is’haK ya ce: “Al’amarin da yake a wajenmu shi ne, mutum ya kame bakinsa daga kan Adnan har zuwa Isma’il (AS). Haka kuma Shehun Malami Abdulganiyyi Al-MaKdisi ya ce: “Danganta nasabar Annabi Muhammad (SAW) har zuwa kan Adnan abu ne da aka haDu a kan ingancinsa babu saBani, amma abin da ya biyo bayan Adnan cikin kakanninsa an yi saBani a kansa.”

Hadisi ya inganta, Annabi (SAW) yana cewa, “Lallai Allah Ya zaBi Kuraishu a cikin Banu Kinanah, kuma Ya zaBi Banu Hashim a cikin Kuraishu. Sannan Ya zaBe ni daga Banu Hashim. Lallai ni zaBaBBen zaBaBBu ne.” (Tirmizi ne ya ruwaito). Wannan tsarkakakkiyar nasaba ta Annabi (SAW) ta nuna zuriya mai daraja, ta muhimman mutane jagororin ayyukan alheri. Tarihi ya tabbatar da cewa kakansa na goma shi ne Kuraishu wanda ake jingina dukan Kabilar Kuraishawa zuwa gare shi don darajarsa. Kakansa na 16, Ilyas shi ne ya fara hadaya a matsayin sadaukar da dabba don girmama Ka’aba. Kusayyu, kakansa na huDu shi ne ya gina Mash’arul Haram a Muzdalifa; shi da ’ya’yansa ne ke hidima ga baKin da ke kai ziyara ga Ka’aba. Akwai wani kakansa Hisham wanda kasancewarsa mai dukiya, ya shahara wajen sadaukar da dukiyarsa don taimakon mutane da ciyar da abinci ga mabuKata, ya tona rijiyoyi a garin Makka. Haka ma kakansa AbdulmuDDalib ya ba da gudunmawa mai yawa wajen farfaDo da rijiyar Zamzam da yin hidima ga baKi masu ziyarar Ka’aba wajen tanadin ruwan sha da abinci. Wannan ita ce nasabar Manzon Allah (SAW) wadda ta tattara manyan mutane masu karimci da daraja a tsakanin al’ummominsu.

Annabi (SAW) yana cewa: “Na fito daga Adam, daga tsarkakakkun iyaye na aure, ba daga tsatson wawaye ba.” Nasabarsa ta mahaifiyarsa kuwa ita ce; Aminatu ’yar Wahabi Dan Abdu Manaf Dan Zuhra Dan Kilab Dan Murrah Dan Ka’ab Dan Lu’ayyu Dan Galib. Kuma daga nan ne kakanninsa ta Bangaren mahaifi da mahaifiya suka haDu.

Darasi na Bakwai

Shayarwa, rainonsa da tasowarsa

Baya ga mahaifiyarsa, wadda ta fara shayar da shi, ita ce Ummu Aiman, kuyangar mahaifinsa. Daga nan sai Suwaiba wadda ta shayar da shi bayan mahaifiyarsa. Kafin haka ita ta shayar da Baffansa Hamza (RA) da Abu Salma Dan Abdul Asdi. Asali ita baiwar Abu Lahabi ce wadda ya ’yanta saboda murnar haihuwar Manzon Allah (SAW), wanda bayan kira zuwa ga Musulunci ya zama babban maKiyinsa.

Ta shayar da shi na ’yan kwanaki, kafin daga bisani a damKa shayar da shi zuwa hannun Halimatus Sa’adiyya daga Banu Sa’ad. Ita Halimatus Sa’adiyya tare da mijinta Haris bin Adbul’uzza suna zaune ne a sararin hamadar Hudaibiyyah kusa da garin Makka. Domin Larabawa a wancan lokaci sukan zauna a Kauyuka saboda ’ya’yansu su tashi da kyawawan al’adu da Dabi’u na asali waDanda ba su gurBata da rayuwar manyan garuruwa ba tare da laKantar harshen Larabci ba. Bayan sauran matan sun Ki karBarsa don sun ga shi maraya ne ba za su samu abin da suke tunanin samu ba. Allah Ya Kaddara Halima ba ta samu yaron raino ba sai ta karBe shi, tun a kan hanyarsu ta komawa gida ta fara ganin albarka, ita aka bari a baya ga abin hawanta mai rauni amma sai da ta kamo sauran har ta wuce su kuma dukan jakuna suka kasa kamo ta.

A wannan ranar taguwarsu da ba ta da nono domin fari da suke fama da shi sai ga ta sun cika da madara mai yawan gaske. Danta na goye ya kasance ba ya barci don yunwa da ta fara ba wa Annabi (SAW) nononta nan da nan suka cicciko Danta ya sha ya Koshi suka yi barcin da suka daDe ba su yi irinsa ba.

Annabi (SAW) ya rayu a KarKashin kulawar Halimatus Sa’adiyya har na tsawon shekara huDu, koda yake tana kai shi ya ga mahaifiyarsa duk wata shida-shida, domin ta gan shi ta kuma auna ci gaban rayuwarsa. HaKiKa zaman Annabi (SAW) a hannun Halimatus Sa’adiyya ya jawo musu albarka da alheri mai yawa a wannan gida. Tarihi ya inganta cewa hatta nono da abinci a gidan da yalwar arziki yawadata gare su sakamakon zaman Manzon Allah (SAW) a hannunsu.

Ana cikin haka ne sai wani abin mamaki wanda ya tsorata Halimatus Sa’adiyya ya faru ga Annabi (SAW) a gidanta. Wannan al’amari ya faru ne, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ba da labari da kansa, cewa, “Jibrilu ya je masa yana cikin wasa da yara, sai ya kama shi ya kwantar da shi ya tsaga Kirjinsa, ya fito da zuciyarsa, ya tsaga ta (ya fitar da wani abu a cikinta), ya ce: ‘Wannan shi ne rabon ShaiDan daga gare ka.’ Sai ya sanya zuciyar cikin wata tasa ta zinariya, ya wanke ta da ruwan zamzam, sannan ya mai da ta wurin zamanta. Yaran da ke tare da shi suka ruga a guje zuwa ga Halimatus Sa’adiyya suka ce lallai an kashe Muhammad (SAW). Koda suka kawo Dauki cikin gaggawa sai suka tarar da shi duk yanayinsa ya canja. Anas ya ce ina ganin alamun Dinkin da aka yi a Kirjin Manzon Allah (SAW). Imam Muslim ne ya ruwaito.

Tarihi ingantacce ya nuna cewa an yi wa Manzon Allah (SAW) irin wannan gyarar zuciya har sau uku a cikin Kuruciyarsa. Malamai sun ce da farko an cire masa rabon ShaiDan daga zuciyarsa, sannan a karo na biyu aka sanya masa tausayi aka kuma cire hassada, a karo na uku kuma aka kwarara mata hikima aka kuma Kara tsarkake ta don shirya shi bisa aikin isar da saKo.

Wannan abu na ban mamaki game da buDe Kirjin Annabi (SAW) ya sa Halimatus Sadiyyah ta ji tsoro, don haka ta mayar da shi gidansu, wurin mahaifiyarsa. Nan ya zauna tare da mahaifiyarsa yana tare da ita har shekara biyu.

Darasi na Takwas

Rasuwar mahaifiayrsa

Manzo (SAW) ya zauna a wurin mahaifiyarsa cikin dangisa na tsawon shekara biyu daga nan mahaifiyarsa ta rasu. Ta tafi Madina ce don ziyarar kabarin mahaifin Annabi (SAW) da danginta, ta yi tafiyar ce da Suwaibatul Aslamiyya mai yi mata hidima tare da surukinta AbdulmuDallib, ta zauna a can tsawon wata Daya. Mahaifiyarsa ta rasu ne a hanyar dawowarta zuwa Makka a wani guri da ake kira Abwa’i, a lokacin yana da shekara shida. Saboda haka ne ma lokacin da Annabi (SAW) ya zo wucewa ta wannan gurin zai nufi garin Makka shekarar da aka yi buDin Makka (Fathu Makka) sai ya tsaya a wurin ya nemi izinin Ubangijinsa domin ya ziyarci kabarinta. Allah Ya yi masa izini, sai ya tsaya ya yi kuka har ya sa waDanda suke tare da shi kuka. Kuma ya ce: “Ku ziyarci kaburbura domin suna tunatar da mutuwa.” (Muslim ne ya ruwaito shi).

Ummu Aiman (baiwar da ya ci gadonta a wurin mahaifinsa), ita ta ci gaba da rainonsa bayan rasuwar mahaifiyarsa, sai kakansa AbdulmuDDalib ya ci gaba da kula da shi. Ya nuna masa wata irin kula da tausasawa da tausayawa waDanda bai taBa yin irinsu ga ’ya’yansa ba har yana gabatar da shi a kan ’ya’yansa a komai.

Za a iya samun Aliyu Muhammad Sa’id, Gamawa Ta +2348023893141

Email: [email protected]