Manzon Allah: Haske mai kore duhu (6)
Lokacin da Annabi (SAW) ya kai shekara takwas, sai kakansa ya rasu, amma kafin rasuwarsa, sai da ya ba da wasiccin rikon Annabi (SAW) ga Baffansa Abu Dalib shakikin mahaifinsa (SAW), wanda ya ci gaba da kula da shi, ya kuma ba shi cikakkiyar kula da taimako da goyon baya musamman lokacin da aka ba […]
Lokacin da Annabi (SAW) ya kai shekara takwas, sai kakansa ya rasu, amma kafin rasuwarsa, sai da ya ba da wasiccin rikon Annabi (SAW) ga Baffansa Abu Dalib shakikin mahaifinsa (SAW), wanda ya ci gaba da kula da shi, ya kuma ba shi cikakkiyar kula da taimako da goyon baya musamman lokacin da aka ba shi manzanci, duk da cewa bai musulunta ba. Saboda haka ne ma Ranar Kiyama Allah zai sassauta masa azaba kamar yadda ya tabbata a ingantaccen Hadisi.
Abu Dalib ya ci gaba da kula da shi da fifita shi da nuna masa jinkai da kauna. A kan wannan Allah Ya yalwata gidansa da abinci har kowa ya koshi ko da kadan ne.
Annabi Muhammad (SAW) ya taso cikin garin Makka kuma ya tafiyar da samartakarsa cikin ban mamaki. Koda yake ya yi sana’oi irin na mutanensa, kamar kiwo da kasuwanci, amma Allah (SWT) Ya tsare shi daga fadawa ga irin ayyuka munana da suka zama ruwan dare a wannan yanki nasu. Annabi (SAW) ya kaurace wa bautar gumaka ta kowace hanya, hatta ma abincin da mutanensa suke dafawa don bautar gunki. Ba ya halartar bukukuwansu na shekara-shekara wanda suke shiryawa don bauta wa gumakansu. Haka kuma, Annabi (SAW) bai shigar da kansa ayyukan barna da suka shahara a lokacinsa, kamar shan giya da caca da zinace-zinace da karya da kashe-kashen rayuka. Wani abu kuma shi ne Annabi (SAW) bai koyi rubutu ko karatu a wurin kowane dan Adam ba a doron kasa. Ya gudanar da rayuwar samartakarsa bisa tsari mai cike da tsabta, ya zama abin misali a cikinsu a wajen rikon amana da gaskiya da juriya da kamewa da kaurace wa dukan ayyukan barna.
Rayuwar Annabi (SAW) ta kasance abar koyi tun daga farkon rayuwarsa. Ya shiga cikin ayyukan taimakon juna, misali ya shiga ayyukan kwato ’yanci da tallafa wa masu rauni. Haka nan a tasowarsa, ya kasance amintaccen mutum, mai himma ta sana’a da dogaro da kai har kowa na son huldar kasuwanci da shi. Ya zo cikin littafin Attarikul-Islamiy cewa Annabi (SAW) ya warware rikicin mutanen Makka yayin da suke sake ginin Ka’aba, wanda har abin ya zama abin alfahari ga kabilun Larabawa.
Darasi na Tara
Allah Ya kiyaye Annabi (SAW) daga kazantar Jahiliyya
Allah Madaukaki Ya kiyaye AnnabinSa (SAW) daga kazantar Jahiliyya da kowane irin aibi, tun yana karami, Ya kuma kawata shi da halaye masu kyau, har ya zamo sunan da ya fi shahara da shi a cikin mutanensa shi ne; Al-amin (wato amintacce.)
Abin da ya faru na cire rabon Shaidan daga cikin zuciyarsa tanadi ne ga manzancinsa, an tsarkake shi daga wasi-wasin Shaidan da shirka da bata irin ta Jahliyya. Tun yana yaro bai kasance mai wargi da wasanni irin na yara ba. Ba ya karya ko hassada ko zalunci. Hakika rasa iyayensa da kakansa bi-da-bi da kuma sana’ar kiwo da ya taso cikinta dukansu horarwa ne na iya hakuri da juriya da daukar nauyin mas’alolin da za su hau kansa na hakurin cutarwar mutane da iya ba da kariya wanda zai yi ga addinin Allah. Allah da kanSa Ya tarbiyyantar da Annabi (SAW), ya kyamaci shirka tun yana karami.
Manzo (SAW) ya ce: “Ubangijina Shi Ya tarbiyyantar da ni kuma Ya kyautata tarbiyyata.”
Darasi na Goma
Tafiyarsa zuwa Sham
Abu Dalib ya yi nufin tafiya kasuwanci zuwa kasar Sham amma saboda shakuwa da Annabi (SAW) ya ji ba zai iya barinsa ba, a kan haka ya yi tafiyar da shi lokacin yana dan shekara 12. Yayin da suka sauka a wani gari kusa da Busra wani babban malami ya fita zuwa gare su sunansa Rahibul Bahira, yana isowa gare su ya rike hannun Annabi (SAW) ya ce: “Wannan shugaban talikai ne, Ma’aikin Ubangijin talikai, wannan Allah zai aiko shi don rahama ga mutane.”
Bahira ya ga wasu alamomi ne tare da Annabi (SAW) wadanda suke a cikin littafinsu na Attaura na Annabin karshe, kamar inuwar girgije da take bin Annabi (SAW) da sujudar bishiya da kuma tambarin Annabta da yake a kafadarsa. Daga nan ya karrama su da liyafa kuma ya roki Abu Dalib ya yi gaggawar mayar da Annabi (SAW) gida kada ya isa da shi Sham don tsoron Yahudawa da Romawa a kansa, saboda idan suka gan shi za su gane kamar yadda suka san ’ya’yansu. Daga nan sai Abu Dalib ya juya ya mayar da shi Makkah.
Darasi na Goma Sha Daya
Yakin Fijar
Wani yaki ne da aka yi shi tsakanin Kuraishawa, Banu Kinanah da kabilar Kais a daya bangaren, fitina ta tsananta a tsakaninsu har ta kai an kashe adadi mai yawa. Daga baya aka yi sulhu kan cewa kowa ya lissafa nasa mamatan wanda nasa ya fi yawa sai a ga abin da ya karu sama a biya diyya, haka kuwa aka yi. A can baya an yi makamanciyar wannan husuma har sau uku duk shekara sai dai babu yaki a cikinsu, wannan ne na hudun kuma na karshe wanda aka gwabza har aka rasa rayuka. An kira yakin da wannan suna don keta alfarmar Makka da watannin alfarma wadanda aka haramta yaki a cikinsu. Wannan shi ne yakin Jahiliyya guda daya wanda Manzo (SAW) ya halarta a lokacin yana da shekara ashirin a duniya a shekara ta 590 Miladiyya.
Rantsuwar Falaloli
Daya ce daga rantse-rantsen Jahliyya. A watan Zul-Kida aka kulla alkawarin rantsuwa ta aminci na ba da kariya da kwato hakkin wanda aka zalunta daga cikin kabilu biyar na Kuraishawa, kabilun su ne:
Banu Hashim dan Abdu-Manaf,
Banu Muddalib dan Abdu-Manaf,
Banu Al’As dan Abdul-Uzza,
Banu Zuhrah dan Kilab.
Banu Tamim dan Murrah.
Shi ma wannan taro Manzon Allah (SAW) ya halarta a gidan Abdullahi dan Jud’an. Annabi (SAW) ya ba da labari cewa: “Lallai na halarci wani taron kulla alkawari da ’yan uwan mahaifina wanda aka yi a gidan Abdullahi bin Jud’an, na fi jin dadin wannan taro fiye da a ba ni jajayen rakuma, kuma da za a kirawo irin wannan taro a cikin Musulunci da na amsa.” (Musnad na Imam Ahmad).
Darasi na Goma Sha Biyu
Haduwarsu da Khadijah, aurensa da aiko shi da Manzanci
Manzon Allah (SAW) ya rayu cikin tsari mai nagarta da sadaukantaka da karfin hali da karimci tare da halin girma. Don haka kowa yana sha’awar alaka da shi. Saboda shaharar da ya yi wajen gaskiyarsa da rikon amanarsa, wata attajira a garin Makka ta samu labarinsa kuma ta aika masa da bukatar su yi hadin gwiwa wajen kasuwanci. Khadijatu bint Kuwailid ta nemi Annabi Muhammad (SAW) da ya jagoranci ayarin kasuwancinta zuwa kasar Sham, lokacin da yake da shekara 25 a duniya. Annabi (SAW) ya jagoranci wannan ayari cikin nasara kuma an dawo gida cike da farin ciki da murna saboda riba mai yawa da aka samu. Dawowarsu gida ke da wuya, abokin tafiyarsa Maisara, wani bawan Khadija da ta hada su don su yi tafiya tare, ya kwashe labarin al’amarin Annabi Muhammad (SAW) – nagartarsa da amanarsa da kamewarsa da kwarewarsa wajen kasuwanci duk ya gaya mata.
Wannan al’amari shi ya jawo hankalin Khadija zuwa ga Annabi (SAW) har ta aika masa kawarta Nafisa bint Muniyah don mika bukatarta ta son ta aure shi. Annabi (SAW), ya amince da bukatar Khadija ya kuma yanke shawarar aurenta.
Za a iya samun Aliyu Gamawa ta:
Tarho: +2348023893141
Email: [email protected]