Manzon Allah: Haske mai kore duhu (7)
Annabi (SAW) ya yi aure yana da shekara 25 a magana mafi inganci, lokacin kuma matarsa Khadija tana da shekara 28 bisa fadin Ibn I’shak. Koda yake akwai ruwayoyin da suke ambata shekarun Khadija a wannan lokaci a kan 40, amma ruwaya mafi inganci ta nuna shekarunta ba su kai haka ba. Maganar Ibn Is’hak […]
Annabi (SAW) ya yi aure yana da shekara 25 a magana mafi inganci, lokacin kuma matarsa Khadija tana da shekara 28 bisa fadin Ibn I’shak. Koda yake akwai ruwayoyin da suke ambata shekarun Khadija a wannan lokaci a kan 40, amma ruwaya mafi inganci ta nuna shekarunta ba su kai haka ba. Maganar Ibn Is’hak ce malamai suka fi ingantawa.
Khadija mace ce attajira ’yar babban gida, tana da karimci da girman daraja, tana da hakuri da kamun kai da kuma kaifin hankali. Ta haifi ’ya’ya shida tare da Manzon Allah (SAW) kuma sun yi shekara 21 tare da ita, kafin rasuwarta. Babu wanda a farkon Musulunci, Annabi (SAW) ya amfana da rayuwarsa da dukiyarsa kamar Nana Khadija. Ta bai wa Annabi (SAW) shawarwari bisa mas’aloli masu yawa, kuma ya amfana da rayuwa da ita.
A shekara ta 40 bayan shekarar giwaye, Allah (SWT) Ya aiko Mala’ika Jibrilu zuwa ga Manzon Allah (SAW), wanda ya same shi a kogon Hira, a ranar Litinin 17 ga Ramadan (bisa wani kaulin). Ya samu Annabi (SAW) a wannan kogo, inda ya saba zuwa don kebe kansa da yin tunani da kuma kaurace wa ayyukan bautar gumaka da suka shahara a garin Makka. Jibril (AS) ya fara ne da umartar Annabi (SAW) cewa ya yi karatu! Ya ce, “Me zan karanta?” A yayin da ya damke shi tare da jijjiga shi ya ce: “Yi karatu!” Annabi (SAW) ya sake ce masa, “Me zan karanta? Ni ba mai karatu ba ne.” Suka yi haka da shi har sau uku, daga nan mala’ika Jibril (AS) bayan ya damke shi ya jijjiga shi, sai ya karanta masa ayoyi biyar na farkon Suratul Alak.
“Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, Wanda Ya yi halitta. Ya halitta mutum daga gudan jini. Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci. Wanda Ya sanar (da mutum) game da alkalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.” (Alak:1-5).
Abdullahi Ibn Abbas ya ce: “An fara saukar wa Manzon Allah (SAW) wahayi a lokacin yana dan shekara arba’in, daga nan ya zauna a Makka shekara 13, ya koma Madina ya yi shekara 10, ya kuma rasu yana da shekara 63.” (Imamu Bukhari ya ruwaito shi).
Daga wannan haduwa tasu da mala’ika Jibrilu sai Manzon Allah (SAW) ya firgita, ya dawo gida wurin matarsa Khadija cikin tsoro, ya ba ta labarin abin da ya faru da shi a kogon Hira. Sayyidatu Khadija ta yi kokarin kwantar masa da hankali da kawar masa da damuwa, cikin lalama da rarrashi. Ta ce masa. Tabbas na san Allah ba zai tozarta ka ba har abada, domin kana sada zumunta, kana fadin gaskiya, kana daukar nauyin marasa gata, kuma kana bin kadin masu rauni. Da irin wadannan sanyayan kalamai ta kwantar masa da hankali.
Baya ga kwantar masa da hankali da Khadija ta yi kokarin yi, har ila yau kuma, Hadisi ya inganta cewa wannan baiwar Allah (Ummuna Khadija) ta dauki Annabi (SAW) zuwa ga wani daga cikin danginta babban malamin addinin Annabi Isa (AS) mai suna Warakah Ibn Nawfal Ibn Asad Ibn Abdul Uzza, kasancewarsa masani kuma marubucin Linjila don samun karin bayani na abin da ke faruwa da Annabi (SAW). Kuma a lokacin da Annabi (SAW) ya bayyana wa wannan malami labarin abin da ya same shi, sai ya ce masa ‘Wannan (wanda ya zo gare ka) ai Namus ne (wato Mala’ika Jibrilu), wanda Allah Ya tura zuwa wurin Musa (AS).
Ina ma zan yi tsawon rai har in ga lokacin da mutanenka za su kore ka?’ Manzon Allah (SAW) ya ce ashe mutanena za su kore ni? Sai Warakah ya ce masa; Lallai haka ne! Domin babu wani wanda zai zo da irin abin da aka aiko ka, face mutanensa sun kyamace shi kuma sun uzzura masa. Amma idan har ka tarar da ni a raye lokacin da ka fara isar da sako, zan taimaka maka iya bakin kokarina. Amma ba a dade da wannan ba, sai Allah Ya yi wa Warakah rasuwa.
Bayan Ma’aiki (SAW) ya samu sararawa na wani lokaci sai wata rana Mala’ika Jibrilu ya kara bayyana a gare shi, yana yi masa kalmomi na kwantar da da hankali da bushara a gare shi cewa shi Manzon Allah ne zuwa ga mutane. Nan ma Manzon Allah (SAW) ya firgita ya dawo gida zuwa ga matarsa Khadija, ya yi mata bayanin abin da ya faru da shi, kuma ya neme ta da ta lullube shi da mayafi, ta kuma lullube shi. Ta sake maimaita masa kalmominta na kwantar da hankali da rarrashi da yabo da karfafawa da nuna kyakkyawan zato gare shi. Sai mala’ika ya sake zuwa ya isar masa da wahayi, inda aka saukar da ayoyi biyar na farkon Suratul Muddassir.
“Ya wadda ya lulluba da mayafi! Ka tashi domin ka yi gargadi. Kuma Ubangijinka sai ka girmama Shi. Kuma tufafinka sai ka tsarkake su. Kuma gumaka ka kaurace musu.”(Mudassir: 1-5).
Tun daga wannan lokaci ne Annabi (SAW) ya fara isar da sakon da aka aiko shi. Ya fara da kira a kadaita Allah Shi kadai, wajen bauta kuma a nisanci gumaka. Farkon wadanda suka yi imani da shi su ne matarsa Khadija, Aliyu bin Abi Talib da Zaidu bin Harisa da Abubakar AS-Siddik da sauransu.
Daga nan kuma sai babban abokinsa Abubakar As-Siddik wanda ya kasance kan gaba wajen karbar kiransa, shi ma ya fara kiran makusanta da abokansa don su amsa kiran Manzon Allah (SAW), irin su Usman bin Affan da Zubairu bin Auwam da Abdurrahman bin Auf da Abu Ubaida bin Jarrah da Sa’ad bin Abi Wakkas. Wadannan su ne suka fara musulunta a farkon kira, a lokacin ana kiran mutane a boye.
Daga nan kuma sai sakon Allah ya zo ga Annabi (SAW) don ya kira makusantansa, kamar yadda Allah (SWT) Yake cewa: “Kuma ka yi gargadi ga danginka mafiya kusanci.”(Shu’arah:214).
A bisa wannan umarni ne, Annabi (SAW) ya shirya ganawa har sau biyu a cikin dare da danginsa na jini, don ya isar musu da sakon Allah. Kuma a duk ganawar, Baffansa Abu Lahab shi yake fitowa fili yana nuna tsananin adawarsa ga sakon Annabi (SAW), tare da yi masa barazana don ya bar wannan aiki (na isar da sakon Allah). Amma Manzon Allah (SAW) bai canja ra’ayinsa ko yin kasa a gwiwa ba wajen isar da sakon Allah.
Wata rana Annabi (SAW) ya hau kan Dutsen Safa ya yi shela, yana kiran mutanen garin Makka don su zo su saurari abin da yake dauke da shi. Wakilan kabilu daban-daban daga Larabawan Makka suka hallara a wurin. Sai Annabi (SAW) ya ce musu shin yanzu idan na ce muku wasu rundunonin yaki na abokan gaba suna gangaren duwatsun nan, suna kokarin kawo muku hari, za ku yarda da ni? Sai suka ce masa, za mu yarda da kai domin ba mu san ka da wani mummunan abu ba. Sai ya ce musu, to lallai ina kiranku da ku kadaita Allah wajen bauta, ku kaurace wa bautar gumaka, don guje wa wata azaba da ta dara ta abokan gaba ta riske ku a Ranar Alkiyama. Sai nan take Baffansa Abu Lahab ya fito fili ya karyata shi ya kuma yi masa barazanar daukar tsattsauran mataki a kansa idan bai bar wannan da’awa tasa ba.
Za a iya samun Aliyu Muhammad Sa’id, Gamawa, Ta +2348023893141
Email: [email protected]