Mara lafiya ya sace motar daukar gawa a Kano
’Yan sanda sun kama barawon motar ne a kauyen Takwasa a Jihar Jigawa
’Yan sanda sun kama barawon motar daukar marasa lafiyan ne a kauyen Takwasa na Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa a yayin da yake kokarin tserewa da ita.
- Harin Giwa: Wadanda suka mutu sun karu zuwa 40
- Najeriya A Yau: Yadda ’Yan Ta’adda Suka Ruguza Ilimi A Arewacin Najeriya
Kakakin ’yan sandan jihar Jigawa, ASP Lawan Shiisu, ya ce “’Yan sanda sun gano motar ce a kauyen Takwasa ta Karamar Hukumar Babura a Jihar Jigawa, a hannun wani mutum dan asalin Karamar Hukumar Daura ta Jihar Katsina, mai muguwar karaya a kafarsa.”
Ya ce an yi sanar gano motar ce bayan samun rahoton, “sace wata motar daukar marasa lafiya — kirar ‘Hummer Bus’ mara lamba a jikinta— da magungunan da ke cikinta, mallakin Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano, a kauyen Kanya Hore da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano.
Daga nan ne ’yan sanda daga Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa suka dukufa aiki, inda washegari suka gano ta da misalin karfe 8 na safiyar ranar Litinin 11 ga watan Disamban da muke ciki.