Maraba da APC, amma…
Rajistar da hukumar zabe ta kasa baki daya ta yi wa jam’iyyar habaka ta APC al’amari ne da ke tabbatar da irin alherin da zai wakana a fagen siyasar kasar nan nan gaba, kuma hakan ya ba marasa ba kunya. Tun da farko dai an dauka cewa jam’iyyun CPC da ta ANPP da kuma ACN […]
Rajistar da hukumar zabe ta kasa baki daya ta yi wa jam’iyyar habaka ta APC al’amari ne da ke tabbatar da irin alherin da zai wakana a fagen siyasar kasar nan nan gaba, kuma hakan ya ba marasa ba kunya. Tun da farko dai an dauka cewa jam’iyyun CPC da ta ANPP da kuma ACN ba za su taba dunkulewa wuri guda don cire wa kawunansu kitse ba daga wuta, ba kuma za su iya share wa talakawan kasar nan hawayen kukansu ba, domin ana yi musu ganin ba su da uwa a gindin murhu sa’anan kuma an ce dukkansu zaman marina suke yi, kowacce akwai inda ta mayar da gabanta. To sai ga shi nan an yi abin da ba a taba yin kamarsa ba a tarihin siyasar Najeriya, domin kuwa sun haden, an kuma yi masu rajistar. Haihuwar wannan sabuwar jam’iyya ya zamanto tilas ne don a samar da ‘ya guda maimakon yuyuyu, wacce za ta kwace goriba daga hannun kuturu cikin sauki, wato ta hambarar da ladifiyar gwamnatin da ta kasa tabuka katabus cikin shekaru 14 don biyawa jama’a dimbin bukatunsu.
Tun a watan Fabrairun bara ne aka faro doguwar tafiyar neman tabbatar da wannan jam’iyyar bisa mawuyaciyar hanya, cike da kututturai da kwazazzabai kuma cikin yanayi mai wahalarwa. Haka nan kuma abokan adawa da makiyan ci gaban kasa sun gicciya turaku, suka kakkafa shingaye bisa wannan hanya don tadiye manyan jami’an jam’iyyun da suka yunkura don aikata alherin da zai amfani daukacin al’ummomin kasar nan. Amma duk da haka nan ba su karaya ba, haka nan suka yi ta zakudawa, suna ta nausawa har sai da suka shawo kan dukkan matsalolin da suka ci karo da su, suka kai ga biyan bukatarsu, suka yi shukura da hamdala ga Maiduka game da taimakon da Ya yi musu. To ba ma sai an fada ba, wannan rajista ta sabuwar jam’iyya ta faranta wa dubun-dubatan talakawa rai, sun kuma nuna haka ta hanyar firfitowa hululu a wurare daban-daban don nuna murnarsu da kuma kara nuna goyon bayansu ga shugabanninta. Talakawa sun yi amanna cewa wanzuwar wanan jam’iyar zai inganta harkokin siyasa, domin kuwa zai ba su zabi tsakanin jam’iyyar da ta dade tana damawa, tana ba talakawa suna sha, suna furzarwa saboda rashin dadi, da kuma wacce suka tabbatar an kafa ta ce domin ta warkar musu da matsalolinsu, ta kuma wuce gaba a dukkan al’amurransu don samun maslaha da fataha a dukkan abubuwan da aka sanya a gaba.
Babban abin da wannan jam’iyyar ta ce za ta sanya a gaba shi ne yaki da rashawa da ha’inci da cin hanci, da kuma magance dukkan almundaha da toshe kafafen da dukiyar talakawa ke tsiyayewa. Baicin haka nan kuma ta yi alkawarin samar da shugabanni managarta, masu cika alkawurra, ba masu wasa da hankalin jama’a ba, wadanda za su kawo karshen matsalar wutar lantarki don farfado da masana’antun da suka dade da durkushewa ta yadda marasa aiki za su samu abin yi, magidanta kuma su tsira daga sharrin fatara da talauci, mutuncinsu ya farfado a idanun iyalansu wadanda suka rigaya suka mayar da su lusaran da ba su iya turzawa don sauke nauyin da ke bisa kawunansu.
Amma duk da cewa jam’iyyar APC a shirye take ta shiga fagen siyasar kasar nan da kafar dama, sai ta yi taka-tsantsan da magabciyarta, wato jam’iyyar PDP, wacce ke tutiya da bugun kirji cewa a matsayinta na giwa bukkar daji a lamurran siyasar kasashen Afirka, ba abin da wannan sabuwar jamiyar za ta yi mata, domin a cewarta ba abin da gara za ta yi da dutse sai lasa. Wannan babbar magana ce ganin cewa duk da gawurtar jam’iyyar PDP babu abin da ta tsinana wa kasar illa haddasa rikice-riken kabilanci da tayar da yamutsi da sunan addini, don ta ji dadin rarraba kawunan jama’a ta yadda za ta mike kafa ta yi ta mulki har sai Mahdi ya zo, ya ture. Ta haka ne kawai za ta iya yin galba don ta san jama’a sun dade da dawowa daga rakiyarta, saboda babu abin alherin da take tsinana musu tun bayan darewarta karagar mulki shekaru aru-aru da suka shude.
To a yanzu ne jam’iyyar PDP za ta zabura don daidaita wannan sabuwar jam’iyyar, za ta kara dukufa bisa wadancan manufofi nata na tayar da husuma don kara rarraba kawunan jama’a, za ta kuma ci gaba da yin amfani da kabilanci don tozarta wasu daga cikin gagga-gaggan shugabannin sabuwar jam’iyar da niyyar shafa masu kashin kaji don kada su yi wani tasiri ko rawar gaban hantsi. Dangane da haka ne ake kira ga ‘ya’yan sabuwar jam’iyyar da kada su tsattsaga bangwayensu ta yadda kadangarun bariki za su ji dadin kurdawa; kada kuma shugabanninsu su bayar da wata ‘yar kafa da za ta sa makirai, gwanayen kulle-kulle, daga cikin shugabannin PDP kutsowa cikinsu da siffar kura cikin fatar tunkiya. Tuni ma wasu shugabannin PDP da kurayensu suka yi kuka sun fara wasa wukake, wasu na lasan baki, wasu na wanke tukwane, wasu na neman kirare, don hura wutar da za a dafa naman giwar da za a yayanka bayan an kifar da ita. To sai a yi hattara kada wannan sabuwar jam’iyyar ta yi karkon kifi, kaman yadda sauran suka yi, bayan shugabanninsu sun ingiza su cikin tarkon jam’iyyar PDP. An dai ce gani ga wane ya isa tsoron Allah.