Maraba da batun janye wa’adin da aka dibar wa kabilar Ibo sai dai…

Da yawa daga cikin al’ummar kasar nan sun yaba da sanarwar da Hadaddiyar kungiyar Matasan Arewacin kasar nan (Coalition of Northern Youth Groups (CNYGs) ta yi a ranar Alhamis da ta wuce na janye wa’adin da ta dibar wa ’yan kabilar Ibo na barin Arewacin kasar nan. A lokacin da yake yi wa manema labarai […]

Maraba da batun janye wa’adin da aka dibar wa kabilar Ibo sai dai…

Da yawa daga cikin al’ummar kasar nan sun yaba da sanarwar da Hadaddiyar kungiyar Matasan Arewacin kasar nan (Coalition of Northern Youth Groups (CNYGs) ta yi a ranar Alhamis da ta wuce na janye wa’adin da ta dibar wa ’yan kabilar Ibo na barin Arewacin kasar nan.

A lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Otel din Transcorp Hilton da ke Abuja jim kadan bayan sun kammala taronsu, mai magana da yawun kungiyar AbdulAzeez Suleiman ne ya bayar da wannan sanarwar na janye wa’adin da suka dibar wa ’yan kabilar Ibo da ke zaune a Arewacin kasar nan.

Suleiman ya kara da cewa kungiyarsa ta dibar wa ’yan kabilar Ibo wa’adin ne bayan sun yi la’akari da yadda kungiyar da ke fafutikar Kafa Yankin Biyafara (IPOB) da ke karkashin shugabancin Nnamdi Kanu take furta wadansu zafafan kalamai da ke neman wargaza kasar nan.

Ya kara da cewa, ganin yadda wadansu manyan da ke Arewacin kasar nan irin su kungiyar Gwamnonin Arewa karkashin Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno da Sarakunan Gargajiya da Malaman addinai da masu fada a ji a yankin Arewa suka rika rokonsu da su janye wa’adin da suka dibar wa kabilar Igbo ne ta sanya suka dauki matakin janyewar a wannan lokaci.

Aminiya ta yaba da yadda kungiyar ta dauki matakin janye wa’adin a wannan lokaci, da ma tun farko bai kamata su dauki irin wannan mataki ba  saboda ya saba wa sashi na 41 na kundin tsarin mulkin kasar nan da ya ba kowane dan kasa damar zama a kowane sako da lungu na kasar nan ba tare da cin mutunci ko wata tsangama ba.

Abin bakin ciki ne ganin yau fiye da shekara 57 da samun ’yancin kan kasar nan amma har yanzu kan ’yan kasar a rarrabe yake. Maimakon mu zama dunkulalliyar kasa, sai wadansu tsiraru ke neman ganin kasar ta wargaje. Duk da an shafe fiye da shekaru uku ana yakin basasa har yanzu mutanen kasar nan ba su dauki darasi daga hakan na.

Sai dai abin da kowa ya zuba ido ya gani a wannan lokaci shi ne, yadda shugabannin yankin Arewacin kasar nan suka yi kokarin shawo kan Hadaddiyar kungiyar matasan Arewa to ya dace shugabannin da suka fito daga Yankin Kudu maso Gabas su ma su yi hobbasa wajen ganin sun tsawatarwa ’yan kungiyar da ke fafutukar kafa yankin Biyafura (IPOB) da su daina yin kalaman da ke neman tayar da hankulan al’ummar kasar nan. Ya dace su yi koyi da irin yadda shugabannin yankin Arewa suka yi na shawo kan hadaddiyar kungiyar Matasan Arewa na janye batun korar kabilar Ibo daga yankin Arewa.  Ana ganin shugabannin da ke yankin Kudu maso Gabashin kasar nan ba su tawa rawar gani wajen tsawatarwa ’yan kungiyar IPOB ba da hakan ta sa ake ganin suna cin karensu babu babbaka, hasalima ana zargin suna da hannu wajen karfafa wa kungiyar gwiwa a yunkurin wargaza hadin kan kasar nan.

Babu abin da kasar nan ke bukata da ya wuce samun zaman lafiya da kwanciyar hankali don a samu ci gaba mai ma’ana.

Don haka darasin da yakamata mu dauka game da batun janye wa’adin  da hadaddiyar kungiyar Arewacin kasar nan ta yi a kan kabilar Ibo shi ne, dole ne mu ci gaba da zama tare, dole ne mu kasance a halin cude-ni-cudeka muddin muna son a samu ci gaba mai ma’ana a kasar nan.  Babu wani bangare da zai iya rayuwa shi kadai ba tare da taimakon wani bangare ba.

Don haka muna kira ga sarakunan gargajiya da malaman addini da manyan ’yan siyasa da ke kowane bangare na kasar nan da su ci gaba da kokarin wayar da kan al’ummarsu game da muhimmancin zaman lafiya.  Sannan muna kira ga jami’an tsaro da su dauki shawarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi game da su rika sanya ido ga masu furta munanan kalaman da ke neman tayar da fitina a kasar nan.  Kadan ne daga cikin ’yan kasa suke furta kalaman batunci idan aka yi sake ba a dauki mataki a kansu ba, to hakan na iya bazuwa kuma ya kai matakin da ba za a iya shawo kansa nan gaba ba.

Ya dace mu hada kai don ganin mu ceto kasar mu daga yunkurin da wasu tsiraru suke yi na neman wargazata.