Maraba da dokar hana bara a Jihar Kano amma..

Kusan kimanin makonnnin biyu kenan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zartas da Dokar hana bara a jihar, dokar da aka dade ana zaman jiranta, bisa la`akari da irin kaskancin da wulakanci da tozartaswa da ke tattare da yin bara, a lokacin da wasu suka mayar da barar sana`a. Dokar hana barar ta 2013, mai […]

Maraba da dokar hana bara a Jihar Kano amma..
Maraba da dokar hana bara a Jihar Kano amma..

Kusan kimanin makonnnin biyu kenan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta zartas da Dokar hana bara a jihar, dokar da aka dade ana zaman jiranta, bisa la`akari da irin kaskancin da wulakanci da tozartaswa da ke tattare da yin bara, a lokacin da wasu suka mayar da barar sana`a. Dokar hana barar ta 2013, mai sunan ”Dokar hana yin bara akan tituna ta shekarar 2013,”
Wannan Doka da za ta fara aiki daga ranar da gwamnan jihar ya rattaba mata hannu, kamar yadda sashinta na 3, ya bayyana. Shi kuwa sashenta na 2, shi ya kasa Mabaratan rukuni uku. Rukunin farko su ne kananan yara da shekarunsu na haihuwa ba su kai 14 ba. Mai karatu ka a nan ana  batun Almajiran makarantun Allo da sauran kananan yara da walau iyayensu kan tura su bara, ko ma wadanda suke barar tare da iyayen nasu, da sauran kananan yara masu nakasa.  
Rukuni na biyu su ne yaran da shekarunsu suka kai 14, amma ba su haura 18 ba. A nan ana maganar Almajiran makarantun Allo da sauran yara masu nakasa da makamantansu. Rukuni na uku, su ne baligai da suka kai shekaru 18, da haihuwa zuwa abin da ya haura, Irin wadannan mabarata kusan su ne mafi yawa a cikin mabaratan da ake fama da su a yau, sun kuma kunshi kurame da makafi da guragu da kutare da bebaye, da sauran masu mutuwar zuciya, wadanda da zarar wata `yar nakasa ko wani ciwo ya same su ko da sun warke sukan ci gaba da yin amfani da waccan dama cikin yin barace-barace.
Shi kuwa sashi na 4, tanadi ya yi akan irin hukuncin da duk wanda aka kama akan ya karya wannan doka fiye da sau daya za a iya daure shi akalla watanni hudu, ko tarar Naira dubu goma (N10,000), ga wanda aka kama ya karya dokar a karon farko, dokar ta yi tanadi yin gargadi da sallamarsa. A dai tanadin hukuncin dokar ya ce wanda duk aka kama da zarar an tabbatar da laifin da ya aikata, ya kuma kammala zaman jarun din da aka debar masa ko ya biyan tarar, idan ba dan kasa ba ne za a tasa keyarsa zuwa kasarsa, idan kuma dan kasa ne, dokar ta ce Alkali na da ikon ya sa a tasa keyarsa zuwa jiharsa ta asali; shi kuwa dan asalin Jihar ta Kano, za a mayar da shi karamar Hukumarsa.
Sashi na 6, na dokar ya tanadi cewa jami`in Hukumar Hisbah ta jihar da duk wani jami`in tsaro suna da ikon su kama wanda duk suka yi karo da shi yana karya wannan doka, sannan ya shigar da kara gaban kotun yanki ta shari`ar musulunci ko Kotun Majistare da ke cikin jihar. A karkashin sashi na 6(a)(i), dokar ta tanadi cewa inda laifin karya dokar ya shafi karamin yaro, to, Kotu na iya kiran mahaifinsa ko marikinsa ta damka shi a hannunsa da yarjejeniyar zai kula da dansa.
Wuraren da dokar ta haramta yin bara sun hada da akan dukkan shatale-talen titunan jihar da kan rawul-rawul da wuraren hada-hadar jama`a, kamar ofis-ofis da kasuwanni  da kusa da fitilun kan tituna da dukkan wuraren taruwar jama`a.
Tabbas, ba sai an fadi ba, lallai akwai bukatar a ce an hanajama`a bare-barare koda da wane irnin suna, ba don kome ba, saidon irin koma baya da barar take jawo wa mutanen arewacin kasar nan daga abokan zama na kudanci, wadanda su ma suke da nakasassun, amma su ba a ganin nasu nakasassun suna bara, ba don kome ba sai don irin yadda mahukuntansu da `yan uwa da sauran masu hannu da shuninsu suke taimaka masu ta fannoni, irin na ilmi da sauran ayyukan dogaro da kai. da koda kananan yara kusan miliyan 10, da aka ce ba sa zuwa makarantar Boko a kasar nan, kididdigar masana ta tabbatar da cewa rabin wannan adadi suna cikin shiyyar Arewa maso Yamma da ta kunshi jihohin Kanon kanta da Katsina da Sakkwato da Jigawa da Kebbi da Kaduna da Zamfara.
Tun shigowar mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, yau kusan shekaru 15, daga lokaci zuwa lokaci, jihohi irin su Sakkwato da Jigawa da Edo da Zamfara da Imo da Nassarawa da Kabbi, sun bullo da bada tallafi ga nakasassun jihohinsu da yakan kama daga N5,000, zuwa N7,000, duk wata. Dadin-dadawa wasu kuma sun mayar da hankali wajen koyar da sana`o`in hannu da bada jari da daukar nakasassu irin ayyukan da za su iya yi, musamman masu ilminsu.
 Amma a jihar Kano da shekara da shekaru take da Cibiyoyintsugurnan da nakasassu a dukkan kananan Hukumomin jihar 44, baya ga shahararriyar Cibiyar horar da nakasassu ta unguwar Mariri da ke kewayen birnin Kano da Cibiyar tsugunnan da kutare da ke Dawakin.
Maganar da ake ciki Gwamnatin Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso ta rufe dukkan Cibiyoyin tsugunnar da nakasassunta da ke fadin jiihar, ta baya-bayannan ita ce ta Mariri, inda a ranar Litinin din makon da ya gabata aka ce wai gwamnatin jihar ce ta yo hayar wasu matasan da suka fatattaki daruwan nakasassun da ke Cibiyar Maririn, da sunan wai za ta yi wani aiki a Cibiyar, inda aka ruwaito Babban Sakataren Hukumar ba da agajin gaggawa na jihar Alhaji Ali Bashir Nakkel yana shaida wa manema labarai cewa, a wurin gwamnati nakasassu 25, da Malamansu kawai, gwamnati ta san da zamansu, su kuma wai za su ci gaba da zamansu, sauran wadanda aka sallama din kuwa inji shi, zauna gari banza ne. Wannan kora ta sanya a ranar Larabar da ta wuce daruruwan nakasassun suka yi wata zanga-zangar lumana zuwa Majaisar Dokokin jihar, inda suka nuna damuwarsu akan waccan doka da irin matakan da gwamnatin ta dauka akan Korar nakasassun, ba tare da ta sama wasu wata madafar rayuwa ba.
Ba ko shakka kamata ya yi a ce gwamnatin Jihar Kanon ta wannan zamani ta himmatu wajen ganin ta taimaka wa nakasassun jihar, ta fannonin da take da su bila adadin kamar yadda sauran jihohin da ba su kai ta arziki ba suke yi. Babu adalci ko kadan a cikin irin wannan harka don an ce cikin ma`aikata 5,000, da gwamnatin Kwankwason ta dauka, biyar rak ne nakasassu. Lallai kuma akwai kuma bukatar gwamnonin jihohin Arewa su tara hankalinsu wuri daya su bullo da tsare-tsare da matakai na bai daya da za su hana mutanensu barace-barace, don kuwa yanzu in Kano ta fara aiwatar da wannan doka, to, Almajiranta manya da kanana wata jihar suka dosa. Allah Ya ba su ikon hada kai a wannan fanni mai muhimmancin gaske a rayuwar mutanensu da ma na kasa baki daya.