Maraba da dokar hana sakin aure a Jihar Kano (6)

A yau cikin ikon Allah za mu karkare wannan batu da muka faro kimanin makonni 5 da suka gabata. Idan aka dubi matsalolin da aka lissafo a bangaren maza da mata game da yawaitar sakin aure, abin akwai tayar da hankali.  Abin mamakin shi ne yadda ake yin sakin aure a kan abin da bai taka […]

Maraba da dokar hana sakin aure a Jihar Kano (6)

A yau cikin ikon Allah za mu karkare wannan batu da muka faro kimanin makonni 5 da suka gabata.

Idan aka dubi matsalolin da aka lissafo a bangaren maza da mata game da yawaitar sakin aure, abin akwai tayar da hankali.  Abin mamakin shi ne yadda ake yin sakin aure a kan abin da bai taka kara ya karya ba. Ba nufin wannan doka ba ce ta hana miji ya saki matarsa, tunda Allah Ya halatta yin saki, sai dai yadda aka mayar da abin tamkar wasan yara ne ya sa gwamnatin Jihar Kano ta fara yunkurin bullo da hanyoyin da suka kamata don hana ko takaita yin sakin ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.  Yadda wadansu magidanta ke wayar gari su saki matansu babu gaira babu dalili, inda suke jefa irin wadannan mata cikin matsala, akwai abin dubawa.

Idan aka kirkiro irin wannan doka, to maza masu irin wannan hali za su shiga taitayinsu, don sun san idan sun yi haka, to akwai tara ko diyyar da  za su ba matan.

Wata kididdiga da aka yi a Jihar Kano ta nuna daruruwan mata ne ake rabuwa da su a kowane mako, inda ake mayar da su zawarawa.  Idan ka hada na wata daya ko shekara abin ba a magana. Baya ga matsalar rashin samun miji ga ’yan mata ana mayar da wasu zawarawa, kuma hakan ba alheri ba ne.

Sai dai kafin a yi dokar ya dace gwamnati ta yi nazari mai zurfi.  Akwai dalilai masu yawa da ke sa wadansu maza ke sakin matansu.  Ma’ana wasu laifin ba na mazan ne ba, daga bangaren matan ne da tilas sai sun saki matan. To dokar ta yi la’akari da irin wannan matsala.  Ya zama idan laifin sakin ya bullo ne daga bangaren mata to a yi wa maza adalci.

Maza da yawa suna korafi a mafi yawan lokuta, laifin na mata ne, su suke janyowa a sake su amma a dora laifin a kan maza.

Don haka jama’a za su iya yi wa kansu alkalanci game da batutuwan da na tabo da ke janyo sakin aure a bangaren maza da mata. Wadannan kadan ne daga cikin matsalolin da suke tattare da zamantakewar aure musamman a Arewacin kasar nan.

Muna kira ga  Gwamnatin Jihar Kano a karkashin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta yi nazari mai zurfi kafin ta aiwatar da wannan doka don a yi wa kowane bangare adalci.

Fatarmu dai a samu daidaito a tsakanin ma’aurata idan kuma saki ya auku a rabu cikin mutunci ba tare da hayaniya ko tashin hankali ba. Da fatar mun amfana daga wannan tsokaci.

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805