Maraba da Jan Zaki

Tun kafin cikan Gwamnatin Muhamadu Buhari ta cika shekara guda bisa karagar mulkin a kasar nan sai ‘yan Najeriya suka fara gwada halayyarsu ta gajen hakuri, suna ta korafi game da abin da suke kira tafiyar sandar da take yi, wanda a sakamakon haka har sai da aka yi watanni shida kafin a fitar da […]

Maraba da Jan Zaki

Tun kafin cikan Gwamnatin Muhamadu Buhari ta cika shekara guda bisa karagar mulkin a kasar nan sai ‘yan Najeriya suka fara gwada halayyarsu ta gajen hakuri, suna ta korafi game da abin da suke kira tafiyar sandar da take yi, wanda a sakamakon haka har sai da aka yi watanni shida kafin a fitar da sunayen ministocin da za su kasance cikin gwamnatinsa. Bayan haka nan kuma an ci gaba da surutai game da  mawuyacin halin da tattalin arzikin kasa ya kasance duk kuwa da cewa ana sane da yadda aka gaje shi daga gwamnatin da ta gabata wacce ta yi facaka da dukiyar al’umma, aka sace na sacewa, sa’an nan aka durkusar da kasar. Dangane da haka ne aka yi wa Baba Buhari lakabi da Go-Slow watau mai tafiyar sanda wajen tafiyar da harkokin gwamnati, alhali kuwa ana matukar bukatar hanzari don magance karayar arzikin da ya fado mata, kuma ya kawar da ita daga cikin kangin wahalhalun zamantakewa da na mulki.

Ana cikin haka ne kuma sai aka tsiri wasu tsegunguma cewa wai akwai gungun wasu mutane a Fadar Shugaban kasa wadanda suka zagaye shi, sai abin da  ransu ya raya ne kadai yake aiwatarwa, ko kuma sai abubuwan da suka kitsa masa ne zai dukufa akai don aikatawa.  An dora laifin afkuwar wasu al’amura marasa armashi a fagen siyasa kan take-taken wadancan mutanen da ake zargi da makure jam’iyyar APC mai gwamnati, suka kuma zare mata lakka, suka hana ta kuzari wajen  karkata gwamnatinta  bisa turbar aiwatar da dukkan kyawawan manufofin da ta yi alkawarin samarwa idan ta ci zabe. 

Haka nan kuma a tashin farko an samu tangarda da Majalisun kasa wadanda suka firfitar da shugabanni ba yadda jam’iyyar APC ta so ba, amma duk da haka nan ba a bar al’amarin da aka ce rashin biyayya g jam’iyya ya haifar ba ya dagula dangantakar Fadar Shugaban kasa da shugabancin majalisun, amma sai dai dangantaka tsakanin  wasu manyan shugabannin jam’iyya da Shugabancin Majalisar Dattijai ta ci gaba da yin tsami har ya zuwa yanzu. Abin sha’awa game da haka shi ne wannan bai gurbata kyakkyawar dangantakar da Shugaba Buhari ya kulla da Majalisar Dattijan ba, kuma a sakamakon haka dukkan abubuwan da ya nema daga gareta da kuma ‘yar-uwarta ta Wakilai ba wanda aka ki sahale masa.

To amma ko da ajizancin dan Adam ya bayyana game da lafiyar Shugaba Muhamadu Buhari har hakan ya kai shi ketarewa kasar Ingila neman maganin matsalar da ya yi ta fama da ita har sau biyu, inda aka yi ta kwarmato game da haka, duk kuwa da cewa ya bar kasar a hannun mataimakinsa kamar yadda doka ta tanada. Wasu da yawa sun yi ta kitsa zantuttuka mara dadin ji, wadanda kuma suka yi kama da labarin kanzon kurege game da rashin lafiyarsa da kuma yadda suke ta zunden cewa hakan ba zai  iya barinsa ya ci gaba da aikinsa na jan ragamar kasar nan ba, ko da bayan komowarsa kasar ne sai dai ya yi murabus. Dangane harkokin mulki da na siyasa suka sukurkuce, amma talakawan da suka zabe shi ba su raba daya biyu ba game da amincewar da suka yi masa na ci gaba da jan ragamar gwamnatinsu da suka yi amanna ita ce mai kawo canji. 

Wadancan gungun mutanen da ake zargi sun yi wa Shugaba Buhari zargagungun a Fadar Aso, sai kuma suka koma kan mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ya danka wa ragamar mulki, suka yi ta yin abubuwan da suka gwanance akai, wadanda kuma suka janyo dalilan da suka sanya ake ganin Gwamnatin Buhari na tafiyar sanda. Haka nan dai aka yi ta zargin cewa shi ma sun yi masa daurin deman-minti, suka hana shi aiwatar da wasu muhimman abubuwan da talakawa suka zaku don ganin an wuce wurin, musamman ma batun binciken da aka rigaya aka kammala kafin sake  ficewar Shugaba Buhari a karo na biyu zuwa kasar Ingila na Sakataren Gwamnati, Dabid Babachir Lawal da kuma Shugaban hukumar leken asiri ta kasa, NIA. Ayo Oke. An kuma samu dogon jinkiri kafin a rantsar da wasu ministoci biyu da Shugaba Buhari ya zazzakulo, ya aike da su majalisa don amincewa, kuma ko da aka rantsar da su ba a tuttura su wajen aiki ba sai da aka kai ruwa rana. 

Baicin wadannan kuma akwai wasu batutuwa da yawa da aka jefa a cikin mala, aka ce wai sai Baba Buhari ya dawo da kansa ya aiwatar, kamar sake lale ga majalisar zartarwa ta ministoci da nannada mukaman da suka rage na  shugabanni da daraktocin wasu muhimman hukumomin gwamnatin tarayya. Haka nan kuma  akwai wasu batutuwa masu muhimmancin gaske da suka taso gadan-gadan suka kuma nemi tayar da kura ko kawo yamutsi a kasar, irin su batun ballewar wani yanki  daga kasar da kuma bukatun ‘yan wasu sassa su bar wuraren da suke zaune bisa wani kayyadadden wa’adi da kuma tsohon zance da aka dade ana ta tusawa watau batun sake fasalin kasar nan bisa tsare-tsare da ra’ayoyi mabambanta. Duk da cewa Mukaddashin Shugaban kasa na wancan lokacin ya dauki matakan ganin cewa wadancan batutuwa ba su tabarbare ba sun zame wa kasar karangiya ko alakakai ba, amma Shugaba Buhari ya nuna cewa yana sane da su a daidai lokacin da ake ta babatu game da su duk kuwa da cewa yana kwance a can Landan yana jiyya. 

Shi ya sa bayan kwanaki biyu da komowarsa ya tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro a wani gajren jawabin da ya yi wa jama’ar kasar nan, inda ya yi kashedin cewa gwamnati fa ba za ta amince da wasu take-taken da za su janyo balbalcewar kasar nan ba, domin kuwa an rigaya an cimma matsayar kasancewarta  daya, kuma dunkulalliya, sa’annan kuma dukkan ‘yan Najeriya na da ‘yanci daidai-wa-daida na zama da gudanar da harkokinsu a dukkan sassa ko lungunan da suka ga dama. To wanan ya isa ishara ga masu neman yin amfani da wadancan batutuwan don rarraba kawunan jama’a ta yadda za a tayar da  dargar da za ta kai kasar kasa da kuma jan kunnuwan masu aikata masha’ar satar bil-adama da ta’addanci, domin kuwa ya nuna cewa za su dandana kudarsu a sabuwar kotun da za a kafa don lallasa su. 

Tun can da farko Uwargidar Shugaba Buhari ta taba bayyanawa, jim kadan bayan komowarta daga ziyarar da ta kai Ingila don duba maigidanta, cewa yanzu tun da ba zaki  Sarkin Dawa, ‘yan kananan namun dawa suna ta sakewa suna aikata masha’a da shegantaku son ransu, to su sani fa  zaki ya kusa komowa, kuma da zarar ya dawo kowa zai shiga taitayinsa.  Wannan shi ne abin da jama’ar Najeriya ke jira su gani ke nan, watau canje-canje masu ma’ana a harkokin gudanar da gwamnati , ta yadda za a yi awon gaba da wasu rubabbun kaya, a kawo sababbin jini da za su gungura ta gaba,  sa’annan  kuma a dukufa wajen yi wa jam’iyyar APC  gyaran fuska, ta yadda za a dora ta bisa mikakkiyar siradin da zai kai ta ga nasara a zabe mai zuwa. Muna  marhaban da murnar komowar  Jan Zaki, da kuma yi masa tunin cewa tun da lafiya ta samu, to ka da a yi bori da sanyin jiki.  

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara