Maraba da kwamitin kar-ta- kwana na Hukumar zabe ta kasa
Ranar Juma`ar da ta gabata shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa, wato INEC, Farfesa Attahiru Mahmud Jega ya bada shelar kafa wani Kwamitin kar ta kwana mai Wakilai goma da Hukumar ta dora wa alhakin ya bi mata sawun irin dukkan matakan da ya kamata ta dauka wajen ganin, ba wani ko wata […]
Ranar Juma`ar da ta gabata shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa, wato INEC, Farfesa Attahiru Mahmud Jega ya bada shelar kafa wani Kwamitin kar ta kwana mai Wakilai goma da Hukumar ta dora wa alhakin ya bi mata sawun irin dukkan matakan da ya kamata ta dauka wajen ganin, ba wani ko wata da ya cancanci ko ta cancanci ya ko ta kada kuri`a a babban zaben kasa na shekara mai zuwa da ba zai kada kuri`arsa ba, a dalilin zamansa dan gudun hijirah a sanadiyar tashe-tashen hankula na `yan kungiyar Jama`atu Ahlis Sunnah Lid Da`awatiWal Jihad da ake yi wa lakabi da Boko Haram. Rikicin da ya gallabi jihohin shiyyar Arewa maso Gabas na Adamawa da Barno da Yobe, har kuma ya fantsama cikin kasa da kasashen makwabta, yau sama da shekaru biyar.
A sanadiyar wannan rikici da yake kokarin zama tamfar ciwon ajali, wato gwamma jiya da yau, kimanin mutane sama da miliyan daya da rabi, suka bar matsugunnansu, suka zama `yan gudun hijirah, walau a cikin kasar nan da ma a kasashen makwabta irinsu Jamhuriyar Nijar da Chadi da Kamaru da makamantansu, baya ga dububan mutane, wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikkata.
Kwamitin da aka diba wa wa`adin kwanakin aiki bakwai daga ranar Litinin da ta gabata 22-12-14, na ya kammala aikinsa tare da mika rahotansa ga shugaban Hukumar ta INEC, yana karkashin jagorancin Misis Thelma Iremiran Kwamishar Hukumar ta kasa, ya yin da Daraktan tsare-tsare da bi-biya, na Hukumar Barista Okechukwu Ndeche yake Sakataren Kwamitin. Dukkan mambobin Kwamitin manyan jami`an Hukumar ta INEC ne da suka hada da Kwamishinonin Hukumar na jihohin da rikicin na Boko Haram ya fi ta`azzara wato jihar Adamawa Barista Kassim Gaidam da na jihar Barno Farfesa Tukur Sa`ad da na jihar Yobe Malam Sadik Abubakar Musa.
Sanarwar da ta tabbatar da kafa wannan Kwamiti ta fito daga Sakataren Yada labarai na Farfesa Jega, wato Mista Koyode Robert Idowu, ta shata ayyukan da aka diba wa Kwamitin, sun hada da ya duba tare da yin nazari akan kalubalen da ke tattare da tsarin shari`a da na tsaro da na siyasa da na gudanar da mulki da suke tattare da yiwuwar `yan gudun hijirar za su fuskanta wajen kada kuri`unsu a babban zaben 2015 in Allah Ya kaimu. An kuma bukaci Kwamitin da ya iya auna shawarwari da matsayin aka bayar ko aka cimmawa a tarurrukan kasa da kasa ko na cikin gida da kungiyoyin da suka yi tarurruka ko muhawara ko tattaunawa akan makomar mutanen da suke gudun hijira a cikin kasarsu da irin yadda suka iya gudanar da zabubbuka a inda suka samu kansu da sauran makamantan matsalolin `yan gudun hijirar cikin gida da yin zabubbuka.
Tun kusan sama da shekara daya ke nan, aka shiga rudanin cece-kucen yiwuwar `yan gudun hijirar rikicin Boko Haram, su iya kada kuri`unsu. Shugaban Hukuamar INEC din shi ya fara barawa akan zai yi wuya Hukumar ta iya gudanar da zabubbuka a cikin yankunan da annobar ta Boko Haram ta tagayyara. Amma bayan kakkausan martanin da ya rinka samu daga `yan asalin wadancan yankuna, musamman `yan siyasa, ya sanya ala tilas, Farfesa Jega ya noke, ta yadda har batun makomar `yan gudun hijirar ya kai ga samun kulawar Majalisar Dattawa da zuwa yanzu ta yi wa al`amarin tukkar hanci.
A ranar Talatar makon jiya, Majalisar Dattawar, lokacin da take karatu na biyu a daftarin dokar da Sanata Mohammed Ali Ndume (APC Barno), ya gabatar da aniyar a gyara sashe na 42 na Kundin zabubbuka na shekarar 2010, wanda ya yi tanadi kamar haka:- 42. Hukumar ta kafa wadatattun tashoshin zabe a dukkan wuraren yin rijista, sannan kuma ta samar da masu kada kuri`a a kowace tashar zabe. Wannan sashe shi Sanata Ndume ya so Majalisar ta gyara da aniyar ganin an kawo batun `yan gudun hijirah a duk inda suke a ba su damar su kada kuri`unsu a cikin zabubbukan 2015.
Bayan doguwar muharawa da `yan Majalisar Dattawan suka tafka, daga karshe, sun amince da cewa ya zama wajibi Hukumar INEC ta dauki dukkan matakan da suka kamata wajen tabbatar da cewa ba wani dan kasar nan da ya rasa damar kada kuri`arsa a cikin babban zaben kasar nan. Ra`ayin `yan Majalisar Dattawan ne cewa bisa ga la`akari da muhimmancin zabe ga jama`ar kasa, wanda ta hanyarsa ne za su samu tofa ta albarkacin bakunansu akan batutuwan da suka jibanci makomar zamantakewarsu da ta tattalin arziki da ta siyasa kanta da sauran batutuwan da suka shafi rayuwarsu gaba dayanta, to kuwa su yi zabe ya zama wajibi muddin suna da raid a lafiya suna kuma cikin kasar nan. Anan ne Majalisar Dattawan ta umurci shugaban Kwamitinta na INEC Sanata Andy Ubah, da ya tabbatar ta tuntubar Hukumar INEC, don daukar matakan da suka kamata.
Mai yiwuwa bisa ga yadda wasu suke zargin gwamnatin shugaba Dokta Goodluck Jonathan da kara iza wutar rikicin na Boko Haram, don wai kawai ta yi amfani da shi wajen rage masu kada kuri`a na wadancan sassa, zarge-zargen da a kullum take ta musamtawa, da ba`a yi ca. . . ba akan gwamnatin tarayyar da Hukumar ta INEC da kuwa zai yi matukar wuya Hukumar ta INEC ta waiwayi makomar wadancan mutane da yanzu suke gudun hijira, bare har a ce za a yi da su a cikin zabubbukan masu zuwa, bisa ga yadda ba a mutunta `yanci da hakkin dan Adam a kasar nan. A kasashen da suka ci gaba mutanen da suke kwance shajaran-majaran da masu tabin hankali ne kadai ba su kada kuri`unsu a zabubbukan kasa, amma mutum ko da gidan Yari da makamantansu yake garkame, to, kuwa ya zama wajibi a sama masa damar da zai kada kuri`arsa, bare ga mai lalurar gudun hijirah.
Idan da rikici irin na Boko Haram, rikici ne da zai hana `yan kasa kada kuri`a, to, kuwa mutanen kasashe irinsu Afganistan da Irak da Siriya da Cuba da makamantansu da suka dade cikin makamantan irin wannan rikice da ba su taba yin zabubbuka ba, amma sai ga shi zuwa yanzu dukkan wadannan kasashe sun gudanar da zabubbukan kasa, wadanda kuma sakamakonsu suka zama karbabbu ga `yan kasa da na waje.
Da wannan dama da za a ba `yan gudun hijirarmu, sai mu yi ta addu`a ga Allah SWT da ya kawo mana zaman lafiya, da kwanciyar hankali da arziki, ta yadda za a gudanar da zabubbukan lami lafiya, koma a yi zabubbukan rikicin na Boko Haram ya kare. Allah kuma Ya ba mu ikon zaben shugabannin na gari da za su jibanci tallafa wa rayuwarmu, ba `yan gangan da `yan ganganci ba amin summa amin.