Maraba da Manzon Allah (2)
Ya Rasulullah (SAW) muna sane cewa Larabawa wadanda ka fito daga cikinsu, sun rarrabu zuwa kabilu-kabilu da suke fada da juna da zubar da jini a tsakaninsu. Sun musanya tauhidin da Annabi Ibrahim (AS) ya kawo musu da bautar gumaka da taurari da mala’iku da aljannu, Ka’aba wadda aka gina ta domin Allah Makadaici ta […]
Ya Rasulullah (SAW) muna sane cewa Larabawa wadanda ka fito daga cikinsu, sun rarrabu zuwa kabilu-kabilu da suke fada da juna da zubar da jini a tsakaninsu. Sun musanya tauhidin da Annabi Ibrahim (AS) ya kawo musu da bautar gumaka da taurari da mala’iku da aljannu, Ka’aba wadda aka gina ta domin Allah Makadaici ta koma matattarar gumaka.
Wannan jahilci ko Jahiliyyar ba ta tsaya kan Larabawa kadai ba, can nesa da Larabawa inda mutane ke zaune nesa da hamada ga iyakokin “manyan mutakabbiran duniya,’ wato kasashe biyu masu fada-aji a lokacin wato Daular Farisa da ta Rum. Kowaccensu sananniya ce a duniya wajen zubar da jinin dan Adam ta hanyar yaki. Duk da fadin kasa da kowaccensu ke da shi, amma kusan kullum suna rike da wuyan juna domin kara fadin daulolinsu ne.
Majusawa masu bautar wuta a Farisa (Iran da zagayenta) sabuwar akidar nan ta raba mutane zuwa rukuni biyu jinin Ubangiji (’ya’yan sarauta) da na ya ku bayi ke cin kasuwa. Dab da aiko ka kuma sun samu kansu a tsaka mai wuya sakamakon bullar akidar Mazda da ke da’awar mallakar mutane ta yadda ta kai sun dauki mata tamkar haja ga maza. Kuma kamar mabiya Mani wanda karnonin baya ya yi da’awar sabon addini ta hanyar gwama koyarwar Almasihu (AS) da ta Zoroaster, akidar Mazda ta bayyana ne sakamakon almundahanar shugabannin addinin majusanci. Haka aka rika fafatawa a tsakanin wadannan akidoji biyu, har zuwa aiko ka (SAW). Sai kuma sarakunan Sassaniya da suke hada kai da limaman Zoroaster inda suka rika bude fagen jin dadi da dora wa talakawa harajoji iri-iri da zaluntarsu.
A can duniyar Daular Rum ko Byzantine kuwa duk da tana da’awar bin addinin da aka saukar daga sama, tana da’awar bin Almasihu (AS) sai ga shi ta gauraya sakon tauhidi da Annabi Isa Almasihu (AS) ya zo da shi da akidojin arnan Girka da arnan Rumawa, inda hakan ya haifar da wani sabon addini Kiristanci da ya saba da koyarwar Yesu (AS). Domin a wajejen shekara ta 381 Miladiyya, Majalisar Cocin Greco-Roman ta bayyana kafirtar akidar Arius na Iskandariyya wadda mafi yawan yankunan gabas suke bi, inda a madadinta majalisar ta tilasta yin imani da cewa Ubangiji da Yesu Almasihu jiki daya ne kuma suna tare. Shi kuwa Arius da mabiyansa sun yi imani ne da kadaitaka da buwayar Ubangiji Allah. Suka ce Ubangiji Yana nan tun fil azal, yayin da aka halicci Yesu Almasihu a wani lokaci.
A daukacin karni na biyar zuwa na shida, cocin ya ci gaba da fama da cece-kuce da muhawara a kokarinsa na fassara da bayar da ma’anar siffofi biyu (ilahantka da mutumtaka) gaYesu Almasihu bisa hasken akidojin Girkawa da akidar Mithra ta mutanen Farisa, kuma tasirin wadannan akidoji biyu abu ne da ake gani balo-balo a coci-cocin Kiristoci a yanzu. Bayan haka ne wata akida ta Ruhu Mai tsarki da Mahaifiyar Ubangiji (Maryam) da akidar ukuntaka (Trinity) suka bayyana, inda aka samu hatsaniya a kasar Sham (Siriya) da Masar da Afirka ta Arewa, inda Kiristoci masu tauhidi suke da akidar cewa, ‘Ubangiji Uba’ Yana sama da ‘ubangiji da.’ A takaice ta’addanci da musgunawa da takurawa ga wasu darikokin addinin Kirista masu bin gangariyar koyarwar Almasihu (AS) da sauran al’umma shi ne abin da ya zama ruwan dare a duniyar Kiristoci a wancan lokacin da ake shirin aiko ka ya Manzon Allah! Domin ka zama raba-gardama wajen mayar da mutane zuwa ga shiriyar Manzanni (AS).
Ya Ma’aikin Allah! A can warwatse jefi-jefi a Yammacin Asiya da Afirka ta Arewa wasu kananan kasashe ne da suke karkashin Yahudawa, kuma wadanda suke da fahimta ta cewa Allah Madaukaki Ya aiko Manzanni. Sai dai kuma shiriyar da wadannan Manzanni suka kawo sun gaza gyara mugun girman kan Yahudawa, wadanda sunayensu suka buga tambura wajen fasadi da barna a bayan kasa. Sun juya baya tare da caccanja dokoki da shari’o’in da Annabi Musa (AS) ya kawo, inda suka yi watsi da Littafin Allah a bayan bayansu suka rungumi son rayukansu, suka yi ta kashe Annabawansu a karshe suka bullo da wata sabuwar akida da suke kira Yahudanci (Judaism). Wato suka mayar da addinin Annabawan Bani Isra’ila ya koma kabilanci, maimakon jerin ayyukan imani.
Gagarumar tawayen da Bani Isra’ila suka yi ga babban mujaddadin karshe na Annabawan Bani Isra’ila Annabi Isa Almasihu (AS) abu ne da har zuwa yau ba a mance da shi ba. Ya Ma’aikin Allah! Idan muka gusa gabas, ga kasashen Indiya da China da al’adu suke baje kolinsu, a lokacin aiko ka suna cikin duhun kafirci, akidar mutanen China ta sanya su cikin rudu ta yadda ba su iya tunanin da ya dace da hankali balle addini.
Zuriyar gidan sarauta na Sui (da suka yi mulki daga shekara ta 581-618 Miladiyya), kuma suka yada akidar Buddah sun jefa China a cikin zubar da jini. Kuma a yayin da addinin Buddah ya gaza fitar da talakawa daga halin kunci, tsohuwar akidar Tao da mahukuntan kasar na baya suka rika bi, ta yi tsada ga talakawa idan aka lura da tsadar da ke cikin bin ta da ibadoji masu sarkakiya da wasu yanke-yanke da suka saba wa hankali. Kuma wadanda suke dandana kudarsu a hannun dukkan wadannan akidoji da takaddamomin, su ne talakawa wadanda su ne ma ake kashewa a karkashin zaluncin da ke kunshe a wadancan addinai da akidoji.
A kasashen da ke yankin Indiya kuwa ba a cewa komai saboda munin rayuwa, akidar addinin Hindu da muguwar falsafarsa suna da matukar takurawa ga jama’a, inda suka mayar da masu karancin samu ko talakawa zuwa matsayin da bai gaza na dabbobin daji ba. Wannan ya sa addinin Hindu ya gaza karbuwa ga sauran jama’ar duniya, saboda ya kebanta da wani yanki ne kawai, ko a ce Arewacin Indiya da yankunan Aryan da ta mamaye. Don haka a jawo wasu su karbi addinin abu ne mai wahala, saboda dole ne mutum ya fito daga wata zuriya kafin ya zama mabiyin addinin, kuma wani gunkinsu mai suna Karma ne zai yanke hukuncin makomar mutum.
Baya ga haka ga wasu abubuwa masu daure kai da suka shafi camfe-camfe da akidu da bautar macizai da hotunan batsa na gumaka da ake da su a Indiya fiye da ko’ina a duniya. Ga bautar aljanu da amfani da mutane a matsayin hadaya da hana aure a tsakanin wata kabila da wata kabilar ga kone mata tare da gawarwakin mazajensu, ga yin lalata da mata a tsakanin limaman addinin Hindu da sauran miyagun al’adu.
A wajen kasashen da ke da’awar ci gaba a tsallaken Kogin Jezartes can deshin Asiya ta Tsakiya inda baroron Turkawa da wasu kabilu ke zaune, rike suke kyam da addinan gargajiya da ayyukan sihiri irin na Shamani.
A nan Afirka Kudu da Sahara kuwa bautar gumaka da dodanni irin na arnanci ne ke baje kolinsu. Yayin da can Turai yankin kabilun Abar da Bulgeriyawa da Jamusawa da Faransawa da sauransu ne suke ta dimuwa kan sauran birbishin wayewar Romawa.
A takaice dai yake-yake da zubar da jini da bautarwa da zaluntar mata da tauye su, su ne suka mamaye ko’ina. Mai karfi ne kadai ke da gaskiya.