Maraba da Manzon Allah (4)

Hujjojin Annabtakarka: Ya Ma’aikin Allah! Hujjojin annabtakarka a fili suke, ka taso ne a cikin al’ummar da ba ta iya rubutu da karatu ba, kuma kai ma haka ka taso balle a ce ka koyo wannan addini ne daga wurin wasu. Kuma sunanka amintacce tun kafin ka fara karbar sakon wahayi balle a ce akwai […]

Maraba da Manzon Allah (4)
Maraba da Manzon Allah (4)

Hujjojin Annabtakarka:

Ya Ma’aikin Allah! Hujjojin annabtakarka a fili suke, ka taso ne a cikin al’ummar da ba ta iya rubutu da karatu ba, kuma kai ma haka ka taso balle a ce ka koyo wannan addini ne daga wurin wasu. Kuma sunanka amintacce tun kafin ka fara karbar sakon wahayi balle a ce akwai nakasu a tarihinka, kasancewar ba ka iya rubutu da karatu ba, ya sa ba wanda zai ce ka kwaikwayi abin da ke cikin sakonnin sauran addinai ne. Haka ka kasance har zuwa lokacin da wahayi ya fara zuwa maka lokacin da ka cika shekara 40, haka Alkur’ani Mai girma ya zo maka muka iske shi yau a hannuwanmu. Wannan Alkur’ani ya kawo mafi yawan labaran abubuwan da suka faru da Annabawan da suka gabata daki-daki tamkar kana tare da su. Baya ga haka ka ba mu labaran abubuwan da za su faru nan gaba, kamar faduwar daular Farisa da ta Rum da daukakar Musulunci a kan sauran addinai a daukacin duniya. Ka kalubalanci duk Balaraben da ke jin wannan Alkur’ani kirkira ne, a matsayinsa na Balarabe ya kawo misalin aya goma irinsa, aka kasa. Kai ka kalubalanci mutanen duniya da aljannu su hadu su taimaki juna wajen kawo misalin Alkur’anin, amma har yau an kasa. Littafi ne da shi ba waka ba, ba zube ba, kuma ba zance sururu ba. Littafi ne da in ana karanta shi zai burge ka, koda ba ka san ma’anar abin da ake fada ba.  Ya Rasulullah! Allah Ya sanya sonka a zukatan dukkan  wadanda suka yi imani da kai, da wadanda suka rayu tare da kai. Wannan soyayya ta kai matsayin da sahabbanka suke shirye su sadaukar da rayukansu da iyayensu saboda kai. Ko yau ya Ma’aikin Allah (SAW), wadanda suka yi imani da kai suna girmama ka suna sonka. Duk masoyinka a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa da ta iyalansa da dukiyarsa domin ya kare martabarka!
Ya Rasulullah! A tarihin dan Adam ba a samu mutumin da aka rubuta tarihi kansa irinka ba, kuma duniya ta ba da shaidar cewa kai ne mutum mafi kwarjini da martaba da kyawawan halaye. Kuma kai kadai ne duniya ta fi ambata a tsakanin mutane safe da maraice. Da an ambace ka, mumini zai ce (Tsira da Aminicin Allah su kara tabbata a gare ka) cikin jin dadi da nuna maka kauna!
Baya ga haka mabiyanka suna yawan maimaita kalmomin yabo ga Allah, suna yin salloli na musamman da addu’o’in da ake yi a lokacin gudanar da kowane irin aiki, kamar zikirin safe da maraice da irin gaisuwar da mutum zai yi idan ya hadu da ’yan uwansa da addu’ar da zai yi idan zai shiga ko zai fita daga gida ko zai shiga ko zai fita daga masallaci ko zai shiga ko zai fita daga ban-daki. Ka koyar da mabiyanka addu’ar da za su yi idan za su kwanta barci ko in suka tashi daga barcin da wadda za su yi idan suka ga jinjirin wata ko za su ci sabon abin marmari da ’ya’yan itatuwa ko za su ci abinci ko abin sha, ko za su sanya tufafi ko za su hau abin hawa ko za su yi tafiya ko in sun nufi dawowa da sauransu. Tabbas ta haka suna yi ne tare da tunawa da kai, domin kai ka koyar da su haka.
Dukkan wadanda suka yi imani da kai ya Muhammad (SAW) duk abin da za su aikata a kowane motsi nasu kama daga Sallah da Azumi da Zakka da Hajji suna yi ne yadda ka koyar ko ka ce kon ka aikata a aikace. Wadannan duk suna dada karfafa mana yin imani da kai ne ya Ma’aikin Allah (SAW) ta hanyar koyi da kai, kamar dai kana tsaye a gabanmu ne muna kwaikwayarka.
Hakika babu wani kuma ba za a samu mutumin da zai samu irin wannan kauna da girmamawa da biyayya da da’a a babba ko karamin aiki kamarka ba a bayan kasa ya Manzon Allah (SAW)!
Tun daga aiko ka, a kowane bangare na duniya har zuwa yau, mutane ke ta tururuwa suna bin ka, ya Manzon Allah daga dukkan jinsunan mutane farare da bakake. Wasu daga cikin wadanda suka bi ka, Kiristoci ne ko Yahudawa ko maguzawa masu bautar gumaka, ko wadanda ba su da wani addini. Daga cikin wadanda suka mika maka wuya ya Manzon Allah! Akwai wadanda suka yi fice wajen hikima da hangen nesa da ilimi da basira, sun bi ka ne, saboda sun ga alamun gaskiyarka da mu’ujizojinka. Ba su bi ka domin an tilasta su ba, ba su bi ka saboda haka suka iske iyayensu da kakanninsu ba. Hasali ma da dama daga cikin wadanda suka bi ka ya Manzon (SAW)! Sun bi ka ne a lokacin da Musulunci ke da rauni, Musulmi suna ’yan kadan a lokacin da ake musguna wa mabiyanka a bayan kasa. Da dama daga cikin wadanda suka bi ka, ya Manzon Allah (SAW)! Sun zabi bin ka ne ba domin samun wani abin duniya ba, sun bi ka a lokacin da suka fuskanci muguwar kuntatawa da cutarwa, kuma duk da wannan musgunawa da cutarwa ba su yi watsi da addininka ba. Wannan ya nuna cewa tabbas kai Manzon Allah ne, ba mutum ne da kawai ya ci ya koshi ya tashi ya yi da’awar annabta ba.
Ya Manzon Allah! Ka zo da babban addini wanda ya kunshi akida da dokoki, ka siffanta mana Allah da mafi kyawun siffofi na cika da kamala, sabanin addinin Kirista wanda ya kasa bambance tsakanin Almasihu (AS) da Allah Uba. Ka kuma tsarkake Allah daga dukkan nakasa da kasawa fiye da yadda dan falsafa ko mai hikima zai iya siffanta Allah. Tabbas ya Manzon Allah! Babu wani mai tunani da ya iya siffanta Allah da mafi kyawun siffa irin yadda ka yi, ka nuna tsabar ilimin sanin Allah da daukakarSa.
Ya Manzon Allah ka kuma nuna tsabar ilimi wajen sanin halitta da abin da ke kunshe a duniya, lura da yadda ka koyar da mabiyanka yadda za su gudanar da rayuwarsu da ta sauran halittu. Ka nuna tsabar tausayi da rahama ga halittu fiye da yadda wani dan Adam a gabaninka ya nuna. Shari’arka cike take da adalci da daidaito da tausayi ga dukkan dan Adam. Ka kawo shari’ar da ta shafi harkokin rayuwar dan Adam – kamar saye da sayarwa da aure da shika da ba da bashi ko rance da ba da shaida da raino da duk wata yarjejeniya da za ta taimaka wajen inganta rayuwar dan Adam da ci gabansa a bayan kasa.
Ya Ma’aikin Allah! A daidai lokacin da kai da mabiyanka suke fuskantar musgunawa da cutarwa daga makiya ne ka rika karfafa batun neman ilimi. Kuma bayan yake-yake da suka kai ga Bude Makka ka yafe wa wadanda suka fitar da kai daga cikinta da karfi, ka kafa daular Musulunci ta hakika, ta yadda zuwa lokacin da ka bar duniya mafi yawan kasashen Larabawa sun karbi Musulunci, kuma kasa da karni daya da wafatinka Musulunci ya yadu zuwa kuryar yamma kamar Andalus (Spain) da kuryar gabas kamar China. Wannan ya nuna sakonka ba na Larabawa ba ne kadai ko wata kabila, a’a na daukacin duniya ne. Kai kadai ne a tsakanin Annabawa da har yanzu mabiyanka suke kokarin bin koyarwarka. Wadanda suka yi imani da kai suna barci ne irin yadda ka yi, suna tsarki irin yadda ka yi, suna riko da duk abin da ka koyar a lokacin rayuwarka tun daga tashi daga barci zuwa kwanciya. Duk wanda ya nemi ya kawo sabon abu a cikin addininka, mabiyanka na gaskiya kan mayar da shi kan hanya, su nuna rashin ingancin wannan bidi’a tasa.  Don haka muke tuna ka a yau ba tare da kade-kade da raye-raye da gwamutsuwa maza da mata da sauran bidi’o’i ba.  Kuma a lokacin da muke tunawa da kewayowar rana ko lokacin haihuwarka, muna cike da jimami kan yadda ake farautar mu mabiyanka a ko’ina a duniya. Mun zama tamkar kwanon tuwo da mayunwata suka kewaye. Ga magani ka shaida mana, amma mun kasa amfani da shi domin fita daga wannan hali.Mun yi imani komawa ga koyarwarka ce mafita!
Allah Ya kara tsira da aminci a gare ka da iyalanka da sahabbanka ya Rasulullulah!