Maraba da sabuwar hukumar sake gina shiyyar Arewa Maso Gabas
Ranar Laraba 8 ga watan nan na Mayu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da membobin Hukumar sake gina shiyyar Arewa Maso Yamma, wato NEDC, a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja jim kadan kafin a fara taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta kasa. Hukumar ta NEDC mai wakilai 11, na karkashin shugabancin Manjo Janar […]
Ranar Laraba 8 ga watan nan na Mayu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da membobin Hukumar sake gina shiyyar Arewa Maso Yamma, wato NEDC, a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja jim kadan kafin a fara taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta kasa. Hukumar ta NEDC mai wakilai 11, na karkashin shugabancin Manjo Janar Paul Tarfa (mai ritaya). Yayin da Alhaji Mohammed G. Alkali yake Manajin Darakta, sai Musa Yashi a zaman Babban Darakta mai kula da ayyukan jinkan jama`a da Muhammad Jawa Babban Daraktan mulki da kudi da Umar Mohammed Babban Daraktan gudanarwa.
Sauran Daraktocin, sun hada da Mista Dabid Kente da ke wakiltar shiyyar Arewa Maso Gabas da Mista Benjamin Adenyi da ke wakiltar shiyyar Arewa ta Tsakiya da Hajiya Asama`u Mohammed da ke wakiltar shiyyar Arewa Maso Yamma da Dokta T. Ekechi mai wakiltar shiyyar Kudu Maso Gabas, sai Mista Olawale Oshun mai wakiltar shiyyar Kudu Maso Yamma da Mista Obasuke McDonald da ke wakiltar shiyyar Kudu Maso Kudu.
Shiyyar Arewa Maso Gabas da aka yi wa wannan sabuwar Hukuma ta NEDC, ta kunshi Jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Taraba da Bauchi, mai mutane sama da miliyan 25. Shiyyar da tun a 2009, yau kusan shekara 10, take fama da annobar rikicin `yan kungiyar Boko Haram. Rikicin da ake kiyasin ya halaka mutane sama da dubu 100 ba ya ga dubun dubatar da aka jikkata, sai kuma kusan miliyan 3, da ya raba da gidajensu, suka zama `yan gudun hijira ko dai a cikin jihohinsu ko a cikin kasa baki daya da ma a kasashen da ke makwabtakanmu irin su Jamhuriyar Nijar da Kamaru da Cadi, har ma da kasar Ghana. An kuma kiyasta cewa mata dubu 50, suka rasa mazajensu, yayin da yara dubu 52 suka zama marayu, duk a cikin annobar rikicin kungiyar Boko Haram din.
An kuma yi kiyasin cewa rikicin na Boko Haram ya yi sanadiyyar salwantar dukiya irin ta gine-ginen makarantu da asibitoci da kasuwanni da wuraren ibada da gidaje da sauransu, da suka kai Dalar Amurka biliyan 9.
Jihar Borno inda daga can annobar ta dauko asali tun a shekarar 2009, ita ta fi shafuwa, sai kuma makawabciyarta Jihar Yobe, sannan Jihar Adamawa. Sauran Jihohin Gombe da Taraba da Bauchi annobar ba ta tsananta a cikinsu ba kamar yadda ta tsananta a wadancan jihohi uku, da na fara ambatawa.
Kafin Majalisar Dattawa ta kafa wannan sabuwar Hukumar NEDC, a cikin watan Oktoban 2017, kuma shugaba Muhammadu Buhari ya sanya mata hannu a ranar 27 ga watan na Oktoba 2017, sannan kuma ya kaddamar da sabuwar Hukumar ta NEDC, akwai Kwamitin shugaban kasa, wato PCNI, da gwamnatin tarayya ta kafa a karkashin jagorancin Laftanar Janar Yakubu Danjuma (mai ritaya) da ya rika gudanar da ayyukan jinkai iri daban-daban a shiyyar Arewa Maso Gabas, har zuwa wannan lokaci, tare da wasu kungiyoyin bayar da tallafi na ciki da wajen kasar nan. Amma yanzu da samun wannan sabuwar Hukuma ta NEDC da dokar Majalisar Dattawa ta tabbatar, Kwamitin shugaban kasar ya tashi daga aiki kenan.
Shi ya sa da yake jawabi a wajen kaddamar da sabuwar Hukumar Daraktocin ta NEDC, shugaba Buhari ya janyo hankulansu a kan bukatar da ke akwai na su iya tattara hankulansu waje daya, don ganin sun iya kididdige irin bukatun da kowace jiha take da shi, sannan kuma su san irin matakan da za su dauka wajen magancesu.
Wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin ta dora wa Hukumar, bayan kudaden gudanarwa da gwamnatoci za su yi sun hada da karbar taimako daga kungiyoyin ba da agaji na ciki da wajen kasar nan da na Hukumomi masu zaman kansu da ma daidaikun jama`a, duk da aniyar sake gina da tsugunnar da kuma farfado da rayuwar mutanen shiyyar da rikicin Boko Haram ya daidaita.
Shugaba Buhari ya tunatar da Daraktocin NEDC din cewa yanzu ya rataya a wuyansu, su rika tuntuba tare da bibiyar ma`aikatu da hukumomi da Kamfanonin gwamnatin da za su gudanar da wasu ayyukan raya kasa a jihohin shiyyar, da aniyar tabbatar da cewa ayyukan sun dace da bukatun mutanen shiyyar, kuma an aiwatar da su yadda ya dace. Wasu kuma sdaga cikin ayyukan da shugaba Buhari ya ce Hukumar ta mayar da hankali sun hada da gina hanyoyi da gidaje da wuraren kasuwanci, da annobar `yan kungiyar Boko Haram ta daidaita. Kazalika ya nemi su mayar da hankali a kan abubuwan da za su gaggauta kawar da matsalolin talauci da jahilci da annobar zaizayar kasa da makamantan barazanar muhalli da sauran kalubalen ci gaba.
A kasafin kudin bana dai an warewa sabuwar Hukumar NEDC Naira biliyan 10, da za ta fara somin-tabi da su. Kodayake Naira biliyan 55, aka so a ba ta.
Abinka da siyasa duk da irin yadda rikicin na Boko Haram ya daidata shiyyar ta Arewa Maso Gabas, musamman Jihohin Borno da Yobe a kan tattalin arzikin kasa da ma na zamantakewa da asarar rayuwa da mayar da mutanen shiyyar `yan gudun hijirar dole, an dade ana kai ruwa rana a zauren Majalisar Dattawan kafin dokar da Sanata Mohammed Ali Ndume Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu ya gabatar, ta samu tsallake siradin Majalisar.
Saura da me? Yanzu al`ummomin wannan shiyya za su zuba idanu su ga irin canjin da za su samu daga wannan sabuwar Hukuma ta NEDC, da aka ba wuka da nama a kan yadda za a farfado da shiyyar ta Arewa Maso Gabas. Ba don kome na ce haka ba, sai don irin yadda ake ta samun badakala iri-iri cikin gudanar da ayyukan jinkai ga wadanda annobar ta Boko Haram ta shafa da ma sauran aikace-aikace na raya kasa a shiyyar baki dayanta. Alal misali kowa ya sha jin irin zarge-zargen da ake yi wa jami`an tsaro da na farar hula a kan sace abinci da sauran kayayyakin agaji da ya kamata a ba wadanda suke zaune a cikin sansanonin `yan gudun hijar da annobar ta shafa, baya ga zargin cin zarafin mata da `yan mata na yi masu fyade da ake kuka da shi.
Haka labarin sama da fadi da aringizon kwangilar ayyukan sake gina shiyyar ta Arewa Maso Gabas din suka game duniya. A ringizon da shi ya yi sanadin da tsohon Sakataren gwamnatin tarayya Injiniya Dabid Lawal, ya rasa mukaminsa. Ko kusa ba a tsammanin sake maimaita aukuwar irin haka daga wadannan shugabannin sabuwar Hukumar ta NEDC, kasancewar mafi yawansu `yan asalin jihohin da suka kunshi shiyyar ne, da ake sa ran za su sa tsoron Allah da kishin mutanensu a zukatansu, su tsaya tsayin daka wajen yin dukkan abin da zai taimaki mutanensu da yankinsu da ma kasa baki daya. Shi ya sa na ce MARABA DA SABUWAR HUKUMAR SAKE GINA SHIYYAR AREWA MASO YAMMA.
Ina yi wa masu karatu fatan mu yi Sallah da shagulgulanta lafiya. Allah Ya sa mu dace Ya amshi ibadarmu ta Azumin watan Ramadan da muke kai. Ya kuma maimaita mana a cikiin kwanciyar hankali da koshin lafiya da karuwar arziki amin summa amin.