Maraba da sabuwar shekarar Musulunci ta 1435, Bayan Hijira
Kwanci-tashi ba wuya a wurin Allah, ga shi Allah SWT cikin ikonSa ya sake zagayo da mu wata sabuwar shekarar Musulunci, wadda ta kama a ranar Litinin din wannan makon, ranar ta yi daidai da 1 ga watan Muharram 1435, wato bayan Hijrah, wato Hiijirar da Manzo SAW, ya yi daga Makkah zuwa Madinah. Bisa […]
Kwanci-tashi ba wuya a wurin Allah, ga shi Allah SWT cikin ikonSa ya sake zagayo da mu wata sabuwar shekarar Musulunci, wadda ta kama a ranar Litinin din wannan makon, ranar ta yi daidai da 1 ga watan Muharram 1435, wato bayan Hijrah, wato Hiijirar da Manzo SAW, ya yi daga Makkah zuwa Madinah. Bisa ga tarihin Musulunci, a zamanin Khalifa na biyu Sayyidina Umar Ibni Khattab RA aka tsayar da lissafi akan shekarar Musulunci kodayake tun kafin bayyanar Annabi Muhammadu SAW, Larabawa na amfani da nasu lissafin , bisa ga abin da suka gada daga Annabi Ibrahim AS.
Masana tarihin addinin Islama sun binciko cewa a wancan lokaci da Sahabbai suka zauna shawarar tsaida lissafin shekarar an kawo shawarar a fara daga watan Rabi`ul Auwal, wanda a lissafi yanzu shi ne wata na uku a cikin jerin watannin musulunci sha biyu, saboda kasancewar a cikinsa Annabi Muhammadu SAW ya yi hijira, amma sai tattaunawa ta yi rinjaye akan a koma akan watan Al-Muharram, wanda Annabi Ibrahim AS ya sanya shi a zaman wata na daya a cikin watanni Islama.
Mai karatu ba aniyar wannan makalar ba ce ta yi dogon bayani akan wancan tarihi, don mai rubutun ba mai ilmin haka bane,illah dai aniyata ita ce in dan bi sawu akan wasu watanni da ranaiku da wala alla suke masu alfarma ko wadanda shari`a ta tabbatar da ana yin ibada a cikinsu da kuma wasu canfe-canfe da wasu miyagun dabiu da basu zo ba a cikin addinin Islama. Kazalika aniyata ce in yi tsokaci akan irin yadda ya kamata musulmi ya kasance a cikin damar da yake samu a cikin rayuwarsa, wadda ta kunshi kwanaki, watanni da shekaru.
Bari in fara da watannin nan hudu masu alfarma wato Rajab da Zul-ka`ada da Zul-Hijjah da Al-Muharram, wadannan watanni Allah SWT ya haramta yaki a cikinsu, kuma uku daga cikinsu in ban da watan Rajab a cikinsu ake aikin Hajji. Mai karatu ka ga wata hikima ta Allah, bai saukar da cewa watan Ramadan, watan da Ya saukar da littafinSa mai tsarki wato Al-kur`ani ya zama cikin watanni masu alfarma, kuma bai hana a yi yaki a ciknsa ba, duk kuwa da watan gaba dayansa watan ibadane da samun kusanci a wurin Allah fiye da sauran watanni, haka kuma wata hikimar ta Allah ita ce yadda bai sanya watan Rabi-Auwal watan da aka haifi fiyayyen halitta Manzo SAW watan da ake kira watan Maulud, da ya zama cikin wadancan watanni. Wannan kadai mai karatu ya isa ka gane cewa abin da Allah Ya ce shi ne addininSa, kuma, duk mai son saduwa da Allah lami lafiya kuma cikin rahamarSa, to, ya bi abin da Ya ce shi ne addini.
A duk lokacin da aka ce irin wannan lokaci ya zo na sabuwar shekara,za ka ga wasu Maluma sukan share wuri su gudanar da karatun shekara, a cikin irin wannan karatu ne za ka ji Malamai suna bayyana abin da shekarar ta ke tafe da shi walau, na alkhairi ko na akasin hakan. Alal misali sukan ce shekarar za ta zo da ambaliyar ruwan sama ko za a yi fari ko za a samu annoba ta wasu cututtuka da dai sauran makamantan bala`an na mace-mace da makamantansu, amma dai karshe sukan ce da mutane lallai su dukufa akan yi sadaka a cikin shekarar. Sukan kuma sama biyansu da su hada ruwan rijiya bakwai su rika sha, abin da ya ke duk a zaman surkulle, wadanda suka saba wa koyarwar Manzo SAW.
Amma kuma ni a tawa fahimtar kamar kuma yadda na ji wasu Maluman suna cewa irin wannan lokaci, lokaci ne na yi wa kai hisabi, wato ma`ana mutum ya yi waiwaye adon tafiya, akan shekarar da ta gabata akan dame dame na alkhairi ko akasinsa, ya aikata, wala alla tsakaninsa da Iyalinsa ko magabatansa ko `yan uwansa koma sauran mutane da mu`amalar yau da kullum ta kasuwa ce ko ta ofis da ta hada shi da su, haka kuma tsakaninsa da Mahalincinsa. A irin wannan lokaci na shigowar sabuwar shekarar, kamata ya yi mutum ya yi kudirin gyara irin wadancan kura-kurai, inda zai iya mayar da hakkin da ba nasa ba ga mai shi ya mayar, inda zai nemi afuwa ya nema, inda zai nemi gafara ga MahaliccinSa ya nema, sannan ya yi kudirin ba zai kara ba.
Kazalika, a irin wannan lokaci ya kamata mutum ya kuma dubi irin halin da kasarsa da mutanenta (ya fara da makwabtansa) suke ciki na wahalar rayuwa da rashin kwanciyar hankali da fadace-fadace da rigingimu na neman mulkin duniya da abin duniyar. Inda zai iya taimakawa da abin aljihunsa, ko da fada ajinsa a cikin al`umma ko kuma ya yi addu`a a cikin kin abin da yake faruwa da fatan Allah Ya kawo karshen al`amarin. A bangaren kasashen duniya da mutanensu da suke cikin irin wannan hali irin wannan matsayi ya kamata mutum ya dauka.
Ganin shigowar sabuwar shekara ga musulmi kamata ya yi ya zama wata babbar damar komawa ga Allah SWT gadan-gadan, don kuwa idan mutum ya waiwaya baya kila zai ga cewa a shekarar da ta gabata, kila ya rasa daya daga cikin mahaifansa koma duka, ko wani dan uwansa, ko amini, ko makwabci, ko abokin aiki ko na kasuwanci. Wadanda suka mutum ba wai don Allah ba Ya son su ba, kai kuma da Ya rayas ka ga sabuwar shekarar, ba don ya fi sonka ba, illa dai haka Ya so Ya aikata ga wanda Ya so a kuma lokacin da Ya so.
Da dan wannan bayani mai karatu Ni ke cewa da kai, “Maraba da sabuwar shekarar 1435, bayan Hijirah”. Allah Ya sada mu da dukkan alkhairan da ke cikinta, Ya karemu daga dukkan sharri da bala`an da ke cikinta, Ya ba mu lafiya, kwanciyar hankali, da karuwar arziki, da shugabanni na gari, Ya ba mu lafiya da zaman lafiya, idan kuma Allah Ya kaddara a cikinta zai dauki ranmu, to, Allah Ka dauke shi cikin imani ka tashe shi cikin imani, amin summa amin.