Maraba da Shekarar 1441 Bayan Hijira
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Godiya da yabo sun tabbata ga Allah (SWT). Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Manzo, da Allah Ya sake nuna mana shigowar Shekarar Musulunci ta 1441, Bayan Hijirar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) daga Makka zuwa Madina. Annabin da ya zama cikamakin Annabawa da Manzanni, wanda Allah Bai halicci kamarsa […]
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Godiya da yabo sun tabbata ga Allah (SWT). Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Manzo, da Allah Ya sake nuna mana shigowar Shekarar Musulunci ta 1441, Bayan Hijirar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) daga Makka zuwa Madina. Annabin da ya zama cikamakin Annabawa da Manzanni, wanda Allah Bai halicci kamarsa ba kuma ba zai halitta ba har tashi Kiyama. Manzo (SAW) ya koma ga Ubangijinsa, Bayan Hijira ta shekara 10, yau an shiga shekara ta 1441. Allah Ka kara tsira ga ManzonKa. Daga lokacin da Manzo (SAW) da babban aminisa Sayyidina Abubakar da wadansu sahabbai (Allah Ya kara yarda da su) suka yi Hijira daga Makka zuwa Madina, bisa umarnin Allah (SWT), bayan ci gaba da kuntatawa daga kafiran Makka, da a lokacin ba sa son su ji an ce su bar bauta wa gumakansu su bauta wa Allah Shi kadai ne aka dasa dan ban Shekarar Hijira.
Shekarar Musulunci tana kunshe da wata 12, da kuma kwana 357 da wasu ’yan awoyi, kamar yadda masana suka kididdige, sabanin ta Miladiyya da masu kididdigar suka ce tana da kwana 365 da wasu ’yan awoyi. Watannin Musulunci su ne: Muharram wanda a yau yake da kwana shida, bayan sanarwar ganin jinjirin wata da Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci karkashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bayar na ganin watan a ranar Asabar da ta gabata bayan watan Zul-Hajji ya cika kwana 30, wanda hakan ya kawo karshen shekarar 1440 BH. Wata na biyu shi ne Safar, sai Rabi’ul Awwal, sai Rabi’us Sani, sai na biyar Jimada Ula, sai na shida Jimada Akhir, na bakwai shi ne Rajab, yayin da na takwas ya kasance Sha’aban, na tara Ramadan wato watan azumi da Bahaushe kan kira azumin gari duka. Na goma cikin watannin Musuluncin shi ne Shawwal, na goma sha daya Zul-Kida sai na goma sha biyu kuma na karshe Zul-Hajji.
A cikin wadannan watanni 12 akwai watanni hudu da Allah (SWT) Ya kebe su, Ya kuma kira su watannin alfarma da Ya haramta yaki da makamantnsa ga Musulmi, watannin hudu su ne: Muharram da Rajab da Zul-Kida da Zul-Hajji amma abin takaici, bisa ga yadda duniya ta shiga rudani, ko a kasashen da suke aiki da shari’ar Musulunci ba sa kula da wannan umarni na Allah (SWT). Haka duk da irin yadda ake ganin hanyoyin wa’azantarwa a kan ilimin sanin Allah da addininSa suna ta kara yaduwa, daga bullar sababbin hanyoyin sadarwa na zamani da a yau suka cika duniya, har gobe akwai Musulmin da ba za su iya kawo maka jerin sunayen watannin Musulunci, balle su kawo sunayen wadancan watanni hudu masu alfarma da Allah Ya haramta yaki da fitina a cikinsu.
Tun farko na bude da godiya ga Allah (SWT) da Ya nuna mana shigowar Sabuwar Shekarar Hijirar cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali gwargwadon hali, ba don Ya fi son mu ba, haka wadanda Ya karbi rayukansu kafin shigowar sabuwar shekarar, su ma ba don ba Ya son su ba, illa dai haka Ya kadarta a kanmu da su, kasancewarmu bayinSa, kuma yadda Ya so Ya yi da mu haka zai Yi. Allah mun gode da wannan baiwa taKa.
Gaba daya abin da shekara take magana a tawa ’yar guntuwar fahimtar shi ne lokaci, da irin muhimmancinsa a rayuwar al’umma baki daya, wato ma’ana kamata ya yi a kullum garin Allah ya waye, rana ta koma ga Ubangijinta, mutane a zamanmu na daidaiku, ko a hade, mu rika yi wa kanmu hisabin me muka aikata na alheri ko akasinsa.
Akasari gwamnatocin kasashe da masana’antu da kamfanoni ba sa yi wa ayyukan da sukan gabatar ko ma wasu kudirce-kudirce, har sai shekara ta kare, duk kuwa da kasancewarmu a nan kasar ba da Kalandar Musulunci muke aiki ba.
Amma kuma malaman addinin Musulunci (na Sunnah) da wasu kungiyoyin addinin Musulunci daban-daban, sukan shirya tarurruka don yi wa al’umma jawabi, wadansu ta kafofin watsa labarai ko ta hudubobinsu na Sallar Juma’a (kamar a bana da ranar Juma’a ta kasance kwana biyu da shiga sabuwar shekarar), wajen jan hankalin al’ummar Musulmi a duk inda suke su rika kiyayewa da lokaci da kokarin yin amfani da shi a kan abubuwan da za su taimaka musu duniya da Lahira, baya ga bayyana muhimman abubuwan da Hijirar ta kunsa da muhimmancinsu. Wadansu malaman kuwa sukan wuce makadi da rawa wajen bayyana wa mabiyansu wasu daga cikin sirrin da shekara da ta kama ta kunsa. Alal misali wadansu kan ce shekarar na dauke da annoba ko ta fari da cututtuka ko ambaliyar ruwan sama da makamantansu, daga karshe kuma su ba da fatawar irin abubuwan da za a yi don samun sauki.
Masu iya magana dai kan ce fahimta fuska, amma dai mun san cewa Allah Shi Ya bar wa kanSa ilimin sanin gaibu.
Mu a nan kasar shekarar 1441BH, ta tarar da mu cikin annoba iri-iri kama daga rashin tsaro irin na rikicin Boko Haram da ake cikin shekara ta 10 ana fama da shi da na yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa (wani lokaci ma a kashe wadanda aka yi garkuwar da su ko da an biya fansar), bayan satar shanu. A gefe daya kuma ga annobar fadace-fadacen Fulani makiya da manoma da a da a Arewa kadai ake fama da ita, amma a ’yan shekarun nan ta game kasa, baya ga fadace-fadace da kashe-kashe masu kama da kabilanci da addini.
A Kudu kuma ga kugen sai an yi yaki da kungiyoyin ’yan kabilar Ibo suka dade suna kadawa, kugen da a kullum kara jin amonsa ake yi, baya ga annobar rashin yarda da juna, musamman a tsakankanin manyan kabilun kasar nan uku, kai har ma tsakanin kananan kabilun. Kuma duk da yadda gwamnatoci suke cewa suna yaki da cin hanci da rashawa da fatara da talauci da rashin aikin yi, har yanzu ka iya cewa da sauran aiki, a kan samun saukin rayuwa ga talakawa.
Ba abin da ya kamata kowa ya duka a kai, da ya wuce kamantawa a duk inda ya samu kansa, kasuwa ce ko a aikin jama’a na gwamnati ne ko na masana’antu ko kamfanoni, na gwamnatoci ne ko na masu zaman kansu, sannan sai ya bi da addu’ar Allah Ya tausaya mana tare da jinkanmu bisa ga irin mawuyacin halin kuncin rayuwar da mafi yawan al’ummar kasa suke ciki a wannan shekara ta 1441, amin summa amin. Maraba da shekarar 1441BH. Allah Ya sa badi ranar ta zama ranar hutu a kasa baki daya kamar yadda ake hutun shekarar Miladiyya.