Maraba Da Taron kasa: Da yardar Allah za a karke lafiya
Ranar Litinin da ta gabata, a dakin taron Cibiyar Harkokin Shari`a ta kasa da ke Abuja, Shugaba Dokta Goodluck Jonathan ya kaddamar da kwamitin taron kasa, mai wakilai 492, wanda ke karkashin jagorancin tsohon Babban Cif Jojin kasar nan, Mai shari`a Idris Kutigi. Duk yawan mahalarta taron, ba mutum daya da jama`ar kasa suka zaba. […]
Ranar Litinin da ta gabata, a dakin taron Cibiyar Harkokin Shari`a ta kasa da ke Abuja, Shugaba Dokta Goodluck Jonathan ya kaddamar da kwamitin taron kasa, mai wakilai 492, wanda ke karkashin jagorancin tsohon Babban Cif Jojin kasar nan, Mai shari`a Idris Kutigi.
Duk yawan mahalarta taron, ba mutum daya da jama`ar kasa suka zaba. karewa ma da karau, hatta gwamnonin jihohin da suka amince su tura walikansu, mutum uku-uku gwamnatin tarayya ta ba su izinin su nada; sai kuma wadanda suka fito daga kungiyoyin kabilu da na addinai da na kwadago da na kare hakkin Bil Adama da na `yan Boko da na wasu kwararru da na Sarakunan gargajiya da na mata da na tsofaffin `yan Majalisun dokoki na kasa da na jami`an tsaro masu kayan Sarki da na farin kaya da na Dattawan kasa, kai har ma da na wakilan `yan kasar nan da suke zaune a kasashen waje, lamarin da ya sa ake ta zargin cewa taron na cimma wata manufar shugaban kasa ce na ya samu nasarar zaben 2015. An kiyasta za a kashe tsabar sama da Naira biliyan 7, a cikin watanni uku da za a gudanar da taron.
A ya yin kaddamar da Kwamitin, Shugaba Jonathan, ya gargadi wakilan da lallai su kauce wa tattaunawa kan batutuwan da suka jibanci ko rura wutar kabilanci ko jinshi ko yanki da son zuciya, bare kuma zargin juna da makamantansu, bisa ga illolinsu a zamantakewar kasa. A takaice ya nemi wakilan da lallai su sa kishin kasa da sadaukarwa, don ci gaban kasar nan da al`ummarta.
Shugaba Jonathan ya yi amfani da wannan dama wajen mayar da martani ga wasu `yan kasa da suke zargin yana da wata manufa ta kashin kansa da yake so ya cimmawa a wannan taro, inda ya ba da amsa da cewa, “Babbar mahufarmu ta kirkiro taron ba ta wuce kishin kasar da muke da ita ba, wajen ganin wanzazzar kasa mai inganci”.
Ya kuma tabbatar wa jama’ar kasa cewa dukkan kudurce-kudurcen da taron ya zartas, za a nemi amincewarsu ta hanyar yin kuri`ar raba-gardama, sannan kuma sai a mika ga Majalisun Dokoki na kasa don sawa a cikin kundin tsarin mulki, don haka sai ya yaba wa Majalisar Dokoki ta kasar a kan kokarin da take wajen ganin saka tanadin kuri`ar raba-gardamar a cikin shirin gyaran kundin tsarin mulkin.
Irin wannan jawabi na jan hankali da gargadi da neman wanke kai ga wakilan taro da ma `yan kasa da fatar da mahukunta kan yi wa taro irin wannan, ba wani sabon labari ba ne, ya zama tamfar al`ada, ta yadda mahukunta kan yi amfani da damar da suka samu, wajen wanke kansu daga irin rashin nasarar da taron ka iya samu daga karshe, musamman ma irin wannan da Shugaba Jonathan ya tsira da rana tsaka, bayan a baya ya sha nuna adawarsa ta yin taron ba shi da wani amfani, a lokacin da`yan adawa suka fara kiraye-kirayen sai a yi taron.
Taron, taro ne dai da tunda Shugaba Jonathan, a cikin jawabinsa na ranar 1 ga watan Oktoban bara, cikin bikin zagayowar ranar cikar kasar nan shekaru 53 da samun `yancin kai da kuma Kwamitin da ya kafa don jiwo ra`ayoyin `yan kasa a kan bukatar yinsa da abubuwan da za a tattauna, al`ummomin kasar nan daga shiyoyi shidda da ake da su suka, tanadi tsabarar da za su je da ita.
Alal misali mutanen shiyyar Kudu maso Yamma, shiyyar da ta kunshi `yan kabilar Yarabawa, a wani taro da suka yi kusan kwansu da kwarkwatarsu a Ibadan ranar 27-02-14, suka fitar da wasu manyan kudurori uku a kan su za su mayar da hankali wajen ganin tabbatuwarsu. Batutuwan su ne:-1. Lallai suna son a yi tsarin da kowace shiyya za ta rika cin gashin kanta a cikin tafiyar da mulki; 2. Lallai a duba tabarbarewar matakan tsaro da aniyar gyara; na 3, kuma na karshe a rage dinbin ikon da gwamnatin tarayya take da shi.
Shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, batutuwa shidda suka gano suna ci masu tuwo a kwarya, suke kuma neman maganinsu, su ne 1. Tabarbarewar matakan tsaro; 2. Sake duba rabon bambancin da ke akwai yanzu a kan rabon kudaden arzikin man fetur na cikin Taiku da na kan tudu; 3. A rage dimbin ikon da gwamnatin tarayya take da shi; 4. kara kirkiro jihohi; 5. Sake tsarin rabon arzikin kasa; na 6, kuma na karshe, shi ne batun lallai sai a waiwayi batun hako man fetur a Arewa.
Ita kuwa shiyyar Arewa ta Tsakiya, manyan bukatu hudu ta tafi taron da su, wadanda suka hada da tanadar wa sarakunan gargajiya ayyukan yi; kawo karshen rikicin Fulani makiya da Manoma; da bambancin dan kasa da bako; da neman a kara kirkiro jihohi.
Shiyyar Kudu maso Kudu (jihohin Neja-Delta masu arzikin man fetur) manyan bukatu 3 suka tafi da su taron. Na farko lallai arzikin kasa, kowane iri, ya zama mallakar jihohin da suke da shi, amma jihohi su rika biyan haraji ga gwamnatin tarayya; na biyu a tanadar wa sarakunan gargajiya ayyukan yi a kundin tsarin mulki; na uku a koma tsarin gwamnatin lardi-lardi.
Su kuwa mutanen shiyya ta Kudu maso Gabas manyan bukatu hudu suka tafi wajen taron da su: Akwai neman a tanadar wa sarakunan gargajiya ayyukan yi a cikin kundin tsarin mulki; da duba tsarin rabon arzikin kasa; da duba batun kara kirkiro jihohi; da son lallai a duba tsarin zaman tare.
Kusan dukkan wadannan bukatu da al`ummar kasa suka je taron da su, ba wadanda Shugaba Jonatahan bai ambace su ba, a zaman abubuwan da taron ka iya tattaunawa a cikin jawabinsa, har ma ya kara da batutuwan da suka shafi hakkokin kananan yara da neman daidaita maza da mata.
Wani abin karfafa gwuiwa da wannan taro sh ine irin kalaman a yi taka-tsantsan da aka rika ji suna fitowa daga bakunan wakilan taron, bayan an kaddamar da su. Wadanda ka iya cewa da yardar Allah, za a kare taro lafiya. Amma babban abin fata daga karshe bai wuce irin yadda za a tabbatar da samar da adalci ga mafi yawan `yan kasa, ba tare da la`akari da yadda aka raba wakilan ba, tsakanin Kudu da Arewa, inda mutanen Kudanci suka tashi da wakilai kusan 300, Arewa na da kusan wakilai 200. Tabbatar da wannan adalci ne kadai, zai sa kuri`ar raba-gardamar da za a yi, ta zo cikin sauki, sannan kuma dinbin kudade da lokaci da za a yi amfani da su, ba za su tafi a banza ba. Kar taron ya zama kamar sauran wadanda suka rigaye shi.