Maraba da wannan gayyata amma fa a yi da lura

Idan Allah ya so, idan kuma komai ya tafi kamar yadda aka tsara gobe Asabar ake sa ran sabon Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari zai jagoranci karfaffan ayarin gwamnatin tarayya zuwa wajen taron shekara-shekara na bana, na kungiyar kasashen nan bakwai mafi karfin tattalin arzikin duniya akan masana `antu da ake kira G7, na kwanaki […]

Maraba da wannan gayyata amma fa a yi da lura
Maraba da wannan gayyata amma fa a yi da lura

Idan Allah ya so, idan kuma komai ya tafi kamar yadda aka tsara gobe Asabar ake sa ran sabon Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari zai jagoranci karfaffan ayarin gwamnatin tarayya zuwa wajen taron shekara-shekara na bana, na kungiyar kasashen nan bakwai mafi karfin tattalin arzikin duniya akan masana `antu da ake kira G7, na kwanaki uku da za a bude a gobe Asabar idan Allah ya nuna mana a birnin Balin na kasar Jamus. karamin Sakataren kula da harkokin kasashen waje da Kwamonwels na kasar Birtaniya Mista Phillips Hammond da ya wakilci Firayim Ministan kasar Birtaniya Mista Dabid Cameron a wajen bikin rantsar da Shugaba Buhari da aka yi a Abuja ranar juma`ar da ta gabata, shi ya kawo wannan goron gayyata ga Shugaba Bahari, amadadin Shugaban kasar ta Birtaniya, a yinin bikin rantsuwar.

kasashen da suka taru suka kafa wannan kungiya ta G7, su ne, Amurka da Birtaniya da Kanada da Japan da Itale da Jamus da Faransa, kuma bisa ga al`ada a duk shekara idan za su yi wannan taro sukan gayyaci Shugaban kasashen duniya, musamman irin namu masu tasowa, kai har ma da na wadanda suka ci gaban, da sauran jami`an duniya da kungiyoyi daban-daban masu ruwa da tsaki a cikin harkokin ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
Duk shekara kungiyar ta G7, a duk lokacin da za ta yi irin wannan taro ta kan gayyaci wanda duk ke kan kujerar mulkin kasar nan. Ba don komai ba sai don irin matsayin da Najeriya din take da shi na kasasncewar ta kasar bakar fatar da ta fi kowace kasar bakar fata yawan al`umma da kuma tattalin arziki mai bunkasa cikin hanzari, bisa ga irin albarkatun tattalin arzikin da Allah ya yi mata. Amma gayyatar wannan karon ka iya cewa ta musamman ce, kasancewar wannan shi ne karon farko a cikin tarihin samun `yancin kan kasar nan daga hannun Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya a shekarar 1960, da `yan adawa suke karbar gwamnati daga jam`iyyar da take kan mulki. Dadin dadawa kasashen suna kyautata zaton sabuwar gwamnatin Shugaba Buhari za ta kamanta mulki cikin gaskiya da adalci, sabanin wadanda suka gabace ta, musamman na `yan shekarun nan.
A lokacin da ya ke mika goron gayyatar halartar taron ga Shugaba Buhari, Mista Hammond, ya neme shi da lalle ya taho da dukkan bukatunsa wajen taron, domin a fadarsa, Farayim Minista Cameron, zai yi duk kokarinsa wajen ganin sauran kasashen kungiyar lalle sun taimaka ma kasar nan da mutanenta,ta yadda za su iya fita daga mawuyacin halin kuncin rayuwar da suke ciki. Mista Hammond ya bayyana fannonin da za su taimaka a kai, kamar fannin tabarbarewar tsaro musamman yaki da ta`addanci da wutar lantarki da makamashi da batun bakin haure da makamantan matsaloli.
Shi kuwa Mista Lee Ju Yuong, Jakada na musamman na Shugaban kasar Jamhuriyar Korea, a wajen kaddamar da Shugaba Buhari, cewa ya yi ko shakka ba ya yi kasar nan za ta fita daga irin mawuyacin kalubalen da take ciki a yanzu. Irin wadanda ya ce kasarsa ta fuskanta kafin ta kai matsayin bunkasar da ta ke a yau. “Al`ummomin kasashen duniya, suna da kyakkyawan yakinin shi (Buhari) zai jagoranci kasar nan zuwa tudun mun tsira, shi ya sanya na zo don in tabbatar wa da `yan Najeriya cewa Korea ta Kudu shirye take wajen ganin ta taimaka wa wannan sabuwar tafiya.” Inji Jakadan na musamman na kasar ta Korea.
Ita ma tsohuwar Sakatariyar harkokin kasashen wajen ta kasar Amurka, Madam Madeleine Albright da tsohon mataimakin karamin Sakataren kasashen waje mai kula da harkokin Nahiyar Afirka na kasar ta Amurka, Mista Johnnie Carson a cikin wata kasidar hadin gwiwar da suka gabatar a ranar kaddamar da Shugba Buhari mai taken “Abin da ya sa samun canjin mulki a Najeriya ya damu kasashen duniya” da aka buga a Mujallar Time Magazine ta kasar Amurka. Cewa suka yi “Bayan Shugaba Buhari ya gudanar da yakin neman zabensa, a kan zaman wanda zai yaki cin hanci da rashawa da kuma mai akidar kawo karshen matsalolin tsaro, Shugaba Buharin, yanzu yana da babban aiki a gabansa, muddin yana son ya wanzar da wannan canji. Ya kai ga nasara, yana bukatar goyon bayan al`ummomin kasashen duniya.” Inji tsofaffin jami`an gwamnatin Amurkan biyu.Madam Albright dai na cikin kungiyoyin kasa da kasa da suka sa idanu a kan yadda aka gudanar da zabubbukan kasar nan da suka gabata.
Dukkan wadannan aniya ta ba Shugban kasa Buhari cikakken hadin kai da goyon baya da ake ta samu daga Shugabannin manyan kasashen duniya, sun biyo bayan irin gagarumar gudumawar da irin wadancan kasashe suka bayar ne a cikin kusan dukkan shirye-shiryen da suka wanzar da wannan canji,bisa ga yakinin da suka yi cewa muddin a wannan karon gwamanatin Jonathan ta jam`iyyar PDP, ta ci gaba da mulki, to,kuwa su za su rasa tasu madafar a cikin tafiyar da wannan kasar.Da wannan ke nan lalle akwai bukatar sabuwar gwamnatin Shugaba Buhari, idan ta tashi tafiya wajen wancan taro, ta kara kwana da sanin da su wa take hulda, da har suka ce ta zo da kokon bararta za su cika mata shi fal da dukkan abin da ta ke bukata.
‘Yan kasa da ita kanta sabuwar gwamnati da su kansu kasashen da suka ci gaba da suka ce za su taimaka mana, kowannenmu ya kwan da sanin cewa manya-manyan matsalolin da suke gallabar kasar nan su ne na tabarbarewar matakan tsaro da suke haddasa ayyukan ta`addanci irin na `yan kungiyar Boko Haram da ta su masu sace tare da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da tabarbarewar tattalin arzikin kasa da matsanancin annobar cin hanci da rashawa da ta kai fagen yanzu jihohi 16, da ita kanta gwamnatin tarayya ma`aikatansu, ke binsu bashin kudaden albashi da alawus-alawus da suka kai sama da N46biliya. Akwai kuma matsalolin karancin wutar lantarki da makamashi da na man fetur da tabarbarewar darajar muyasar kudin kasar nan, wato Naira.Ga kuma dimbin bashin N1.3tiriliyan da ake bin gwamnatin tarayya baya ga na jihohi da makamantan matsalolin da rashin fili ba zai bari ba in kawo su duka ba.
Don haka ya zama wajibi idan Shugaba Buhari da ayarinsa sun je wancan taro, to, su tsaya kai da fatan a kan dukkan taimakon da za a ba mu wanda zai taimaki farfadowar tattalin arzikin kasarmu ne.Musamman a kan batun da ya jibanci farfado da matakan tsaro da wutar lantarki da rashin aikin yi da ya yi katutu da yaki da cin hanci da rashawa da ingantuwar ayyukan noma da kiwo da farfado da masana`antumu. Lalle su dage su gaya wa wadancan manyan kasashen duniya, cewa za mu fara rufe kofofinmu a kan kayayyakinsu da ba su da wani muhimmanci a cikin ci gaban kasarmu, kamar yadda kasashe irin su Indiya da Sin wato China suka yi suka kafa tattalin arzikinsu. Tabbas, taimako kam, kasar nan tana matukar bukatarsa, amma ba wanda zai kara durkusar da ita ba. Don haka akwai bukatar a yi da lura.