…Maradona ya ce Golan Jamus ne ya dace ya lashe Gwarzon dan kwallon Duniya a bana

Shahararren dan kwallon duniya dan asalin Ajantina Diego Maradona a ranar Talatar da ta wuce ne ya bayyana ra’ayinsa a kan cewa Golan Jamus Manuel Neuer ne ya dace ya lashe Gwarzn dan kwallon Duniya a bana ba Cristiano Ronaldo ko Lionel Messi ba. Maradona ya ce duk da cewa Ronaldo ya taimaka wa kulob […]

…Maradona ya ce Golan Jamus ne ya dace ya lashe Gwarzon dan kwallon Duniya a bana
…Maradona ya ce Golan Jamus ne ya dace ya lashe Gwarzon dan kwallon Duniya a bana

Shahararren dan kwallon duniya dan asalin Ajantina Diego Maradona a ranar Talatar da ta wuce ne ya bayyana ra’ayinsa a kan cewa Golan Jamus Manuel Neuer ne ya dace ya lashe Gwarzn dan kwallon Duniya a bana ba Cristiano Ronaldo ko Lionel Messi ba.

Maradona ya ce duk da cewa Ronaldo ya taimaka wa kulob din Madrid wajen lashe gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) a karo na 10 bai cancanci ya lashe gasar ba. Haka shi ma Messi duk da ya kafa sabon tarihin dan kwallon da ya fi zura kwallaye a raga a tarihin gasar rukunin La-Liga da na gasar zakarun kulob-kulob na Turai (Champions League) shi ma bai cancanci ya lashe gasar ba.
Maradona ya ce wanda ya dace ya lashe Gwarzon dan kwallon Duniya a wannan karo shi ne golan Jamus Manuel Neuer. Ya ce Neuer ne ya taimakawa Jamus wajen lashe gasar cin kofin duniya a Brazil a bara, sannan shi ma ya taimaki kulob din Bayern Munich wajen lashe kofuna uku a Jamus a bara.
Sai dai masana harkar kwallon suna danganta Cristiano Ronaldo a matsayin wanda ake ganin zai sake lashe gasar a karo na biyu a jere.