Maradona zai yi takarar shugaban Hukumar FIFA

Rahotanni da ke fitowa daga Ajantina sun nuna shahararren dan kwallon duniya Diego Maradona ya yanke shawarar yin takarar shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA. Sanannen ma’aikacin gidan talabijin kuma mai wallafa littattafai dan asalin Uruguay bictor Hugu ne ya sanar da wannan labari a kafar sadarwarsa ta twitter. Ya ce Maradona […]

Maradona zai yi takarar shugaban Hukumar FIFA
Maradona zai yi takarar shugaban Hukumar FIFA

Rahotanni da ke fitowa daga Ajantina sun nuna shahararren dan kwallon duniya Diego Maradona ya yanke shawarar yin takarar shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta duniya FIFA.

Sanannen ma’aikacin gidan talabijin kuma mai wallafa littattafai dan asalin Uruguay bictor Hugu ne ya sanar da wannan labari a kafar sadarwarsa ta twitter. Ya ce Maradona dan kimanin shekara 54 ya yanke shawarar yin takarar shugabancin ne bayan shugaba mai ci Sepp Blatter ya yi murabus.
Maradona dai yana daga cikin wadanda suke sukar Sepp Blatter a kan yadda yake gudanar da mulki a hukumar ta FIFA.
Tsohon kyaftin din Ajantina da kuma kocinta, Diego Maradona ya buga wa kasarsa gasar cin kofin duniya sau hudu a karo daban-daban kafin ya yi ritaya. A shekarar 2010 ce Hukumar FIFA ta ba su kyautar gwarazen ’yan kwallon duniya na karni tare da Pele na Brazil a matsayin na hadin gwiwa.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram