Marainiya ta ga tasku a hannun marikiyarta
Wata marainiya da aka tsince ta da kayanta aka tana watangaririya a cikin unguwa ta ce yadda mai rikonta ke gana mata azaba ne ya sa take yawo a unguwa. Marainiyar mai suna Sa’adatu Nuhu mai kimanin shekara 13 da take makarantar firamare Tunawa da Adamu Dikko a Tudun Jukun, Zariya ta shaida wa Aminiya […]
Wata marainiya da aka tsince ta da kayanta aka tana watangaririya a cikin unguwa ta ce yadda mai rikonta ke gana mata azaba ne ya sa take yawo a unguwa. Marainiyar mai suna Sa’adatu Nuhu mai kimanin shekara 13 da take makarantar firamare Tunawa da Adamu Dikko a Tudun Jukun, Zariya ta shaida wa Aminiya cewa kanwar mahaifinta da take rike da ita ce take gana mata azaba. “Ni marainiya ce mahaifina ya rasu do haka wanda nake zaton kaka take a wurina ta dauko ni daga garin danja da ke Jihar Katsina ta kawo ni wajen ’yarta domin in rika taya ta aiki, ta ce min kuma wai ita kanwar mahaifina ne zan zauna a wurinta domin na yi karatu. To muna zaune da ita, tun da mahaifiyar nata ta tafi ta bar mu, sai ta shiga wahalar da ni, kullum sai ta doke ni kuma ta daure ni ta kuma hana ni abinci, ta ce wai ina dukan mata ’ya’ya, ko ta ce ina yi mata sata. Duk lokacin da ta aje kudinta ba ta gani ba sai ta kama ni ta yanyanka min jiki, wani lokaci kuma sai ta kama hannuna ta danna a cikin kaskon wuta.”
Ta kara da cewa, “Akwai lokacin da ta dauki muciya ta kwakkwala min a kai ya farfashe yana jini, sai ta aske min kan kuma bayana da ka gani a haka reza ta sa ta yanyanka kuma wannan tabo da ka gani a kafadata ruwan zafi ta tafasa ta kwara min. Akwai lokacin ma da ta bi ni har makarata ta nemi ta azabtar da ni, malamanmu suka taso mata ta ce wai na sace mata kudi, alhali muna da yawa a gidan kuma idan abinta ya bace sai ta ce ni na dauke. Sai malaman suka dakatar da ita sai ta hau zagin malaman har ta ce za ta bugi wata daga cikin malaman, to daga nan malaman suka ce za su kai kara kuma za su rike ni a hannunsu, dama sun ga yadda nake zuwa makaranta a kullum suna ganin akwai abin da ke faruwa da ni. Daga nan sai na dan samu sauki kadan, malaman nan su suke ba ni littattafan da nake rubutu kuma su suke ba ni kudi na ci abinci in an fito tara. To yau kuma na dawo makaranta sai kawai ta tattara kayana ta koro ni waje ta ce na tafi gidan iyayena in ba haka ba za ta kashe ni. Ni kuma da yake ban san ko’ina ba sai fito ina ta tafiya ina kuka sai wani mutumi ya dauko ni ya kawo ni makarantar wani malami na yi masa bayanin abin da yake faruwa da ni, shi ne shi kuma ya kawo ni nan gidan suka ba ni ruwa na yi wanka suka ba ni abinci na ci ni yanzu ina roko ne a koma da ni wurin mahaifiyata a can danja.”
Sa’adatu ta ce tsohuwar da ta kai ta wurin matar da ke rikonta wato mamarta ita ce ta fada mata cewa kanwar mahaifinta ne, “Ban san dangantakarmu da ita ba, ni dai ina rokon ku don Allah ku kai ni wurin mahaifiyata,” inji ta.
Mai Unguwa Malam dahiru Mamuda danjaba ya shaida wa wakilinmu cewa wani malami mai suna Malam Nura Dambo ne ya zo da ita ya ce an kawo masa ita ce cewa wai marikiyarta ta kore ta daga gida, ta ce ta bar mata gida in ba haka ba za kashe ta. “Bayan mun binciki yarinyar sai ta shaida mana cewa suna zaune ne a gidajen Dadaye da ke Tudun Jukun, Zariya kuma mun lura da halin da yarinyar ke ciki yanayi ne na wahala kuma tana bukatar taimako sai muka dauki babur muka tafi neman gidan da ta fada mana gidan Malam Ahmad bayan isarmu gidan sai muka yi sallama sai ita uwar dakinta da fito muka ce muna neman mai gidan ne sai ta ce ba ya nan sai muka ce shi muke bukatar gani saboda ’yarsa mai suna Sa’adatu don haka idan ya dawo ki ce muna bukatar ganinsa, to zuwan da bai yi ba ke nan sai muka kai batun ofishin ’yan sanda na Tudun Wada, Zariya inda su kuma ’yan sanda suka gayyato Malam Ahmad da matarsa Zuwaira da ake zargi da azabtar da yarinyar.
Su kuma ’yan sanda bayan daukar bayanai sai suka ce mu koma gida tare da yarinyar mu dawo washegari karfe 10:00 na safe domin su tura mu ofishin jin dadi da walwalar na yara,” inji shi.
Da wakilinmu ya ziyarci firamaren Adamu Dikko, shugaban makarantar Malam Sani sambo ya tabbatar da cewa sun san da matsalar yariyar domin su suke daukar wasu daga cikin dawainiyar yarinyar kamar samar mata da littattafan karatu da rubutu da ba ta kudin cin abinci da rana, kuma har sun yi barazanar karbe yarinyar domin ta zauna a gurinsu.
A ofishin ’yan sanda na Tudun Wada wani dan sanda da bai so a ambanci sunansa ba, ya ce bayan sun kammala bincike sun tura su ofisin jin dadi da walwalar kananan yara domin sune ke da hakki a kan wannan al’amari.
Sai dai da wakilinmu ya nemi jin ta bakin wadda ake zargi da azabtar da marainiyar, Zuwaira Ahmad ta ce sam ba haka ba ne kuma a ba su yarinyarsu su koma da ita wurin iyayenta.
Shugaban sashin kula da jin dadi da walwalar jama’a da maganar ke gabansa Malam Sama’ila Yaroson ya ce ya umarci wadda ake zargin Zuwaira Ahmad ta zo a ranar Talata domin tura wa a taho da mahaifiyar Sa’adatu daga garin danja amma sun ki zuwa amma yau Laraba (shekaranjiya), kanen mahaifin yarinyar mai suna Malam Basiru Abubakar da mahaifiyarta Basira Abdulkadir da suke zaune a Unguwar Bako a karamar Hukumar kankara a Jihar Katsina kuma sun je Zariyar sun tafi da yarinyar bayan da hukumomi suka tuntube su.