Marainiyar da magidanta 7 suka lalata na neman hakkinta
Mahaifiyar yarinyar ta nemi a bi mata hakkin ‘yarta mai shekaru 12 bisa zargin wasu magidanta 7 da yi mata fyade.
Mahaifiyar wata marainiya da magidanta bakwai suka yi wa fyade irin na ba-ni-in-ba-ka na rokon a bi wa diyar tata hakkinta.
Uwar yarinyar mai shekara 12 a Jihar Sakkwato ta yi rokon ne bayan wasu lauyoyi da masu kare hakkin dan Adam sun fara fafutukar ganin an yi wa marainiyar adalci.
A cikin watan Fabarairu ne magidantan suka zakke wa yarinyar mai fama da tabin hankali a wani salo na karba-karba.
Aika-aikan da suka yi wa marainiyar ya sa tana fuskantar tsangwama har ta kai ga iyayenta na dakatar da ita daga zuwa makaranta.
Da farko dangin yarinyar sun yanke kauna da samun adalci saboda an saki wadanda ake zargin a daidai lokacin da ake jiran sauraron shari’a.