Marar basira ba ya wakar dambe, In ji Ummaru Wazirin Narayau

Fitaccen mawakin dambe mai suna Ummaru wanda ake yi masa lakabi da Wazirin Narayau ya ce sai mai basira ne kawai yake iya yin waka ga ’yan dambe saboda wahalar da ke cikinta.Ummaru Wazirin Narayau wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Jihar Legas a karshen makon da ya gabata ya […]

Marar basira ba ya wakar dambe, In ji Ummaru Wazirin Narayau

Fitaccen mawakin dambe mai suna Ummaru wanda ake yi masa lakabi da Wazirin Narayau ya ce sai mai basira ne kawai yake iya yin waka ga ’yan dambe saboda wahalar da ke cikinta.
Ummaru Wazirin Narayau wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya a Jihar Legas a karshen makon da ya gabata ya ce wakar dambe ta sha bamban da sauran wakoki.
Ya ce: “Ita wakar dambe ta bambanta da sauran wakoki saboda sarkakiyar da take da shi ba kamar sauran wakokin gama-garin mutane ba da salon wakar su ba shi da wahala. Shi dambe daban yake, shi ya sa rago ko matsoraci ba ya yinsa haka ma wakar dambe daban take marar basira ko wanda ba shi da kaifin basira ba ya yinta. Ita wakar dambe za ka kalli dan dambe da irin jaruntar da yake da ita sai ka shirya masa waka, saboda haka idan ka tashi yi salon wakar da kalmomin da za ka fada a ciki, sai ka yi zurfin tunani.”
Ya ci gaba da cewa “Shi ya sa ka ga ni ko da a cikin ’yan uwana mawakan dambe na fita daban, don ni za ka iya gani na idan ba ka san ina yin wakar dambe ba za ka iya sani ba. Ni ba na nuna kaina kuma ba na yawan surutu. To haka ake son mawakin dambe ya kasance. Cikin nazari da zurfin tunani domin idan ya tashi waka ya yi basira sosai.”
Ya bayyana cewa babu wata sana’a da ke kawo arziki da suna kamar dambe sannan kuma ita ce sana’ar da ke raya wuri jama’a su taru.
Ya kara da cewa ’yan dambe sun sha fasa masa ganga yayin da yake kidan dambe a wurare daban-daban.
“Ba na mantawa an sha fasa mini gangata, amma ban fasa yin wakar dambe ba, saboda babu sana’ar da take kawo arziki kuma take raya gari kamar dambe. Ka na fara yin dambe a wuri ko kasuwa, to yanzu za ka rika ganin jama’a na kwararowa zuwa wurin domin shi dambe farin jinin gare shi mutane suna sha’awar kallonsa.” In ji shi.