Marasa biyan kudin lantarki ne ke korafin karin kudi —Minista

Adelabubu ya ba ido rufe suka kara kudin lantarki ga masu amfani da layin Band A ba

Marasa biyan kudin lantarki ne ke korafin karin kudi —Minista

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce kukan da ake yi kan karin kuɗin wutar lantarki ga masu amfani da layin Band A ya fito ne daga wadanda ba sa biyan kudin wutar a baya.

Adelabu, ya bayyana hakan a taron da aka yi kan Kasuwar Makamashi na Afirka karo na 8 a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce sabon tsarin farashin makamashi ya haifar da rage farashin lantarki ga masu amfani da rukunin Band A da kashi 30 zuwa 40 cikin ɗari.

Ministan ya yi zargin cewa, sabon kudin fiton ya sa aka kara kudin da ake samarwa ga masana’antun, wanda hakan ya janyo tsadar kayayyaki da ayyuka.

“Karin kudin wutar lantarkin ba wai an yi niyyar ne haka kawai ga ’yan Najeriya ba, ko kuma kara tabarbarewar tattalin arzikin kasa da ya riga ya yi sanadin hauhawar farashin kayayyaki da rage darajar Naira.

“Amma an yi niyya ne don magance ko rage wahalhalun da jama’a ke ciki.

“Wadanda ke rukunin A, idan za su kwatanta abin da suke kashewa wajen samar da makamashi daga wutar lantarki da na’urorin samar da makamashi, kafin sake sauya kuɗin fito, ba su samu kasa da kashi 30 zuwa 40 ba, a jimillar kuɗin su. Wannan ita ce gaskiya.”

“Mu ma masu amfani da wutar lantarki ne, don haka za mu iya tabbatar da hakan.

“Gaskiya ne cewa idan kuna cikin tsarin Band A, lissafinku zai ninka idan ba ƙari ba.

“Amma duba abin da kuke kashewa a kan janareta da sayen dizal da sayen man fetur, sabon tarin bai kai haka ba,” in ji ministan.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja