Marasa galihu sun kwashi gara a bikin amaryar da aka fasa
Wata amarya a Jihar Califoniya da angon da ya kamata ya auret a ya ce ya fasa auren, alhali iyayenta sun kashe kudin biki sama da Dala dubu 35, wato daidai da Naira Miliyan bakwai da dubu 70, sai iyayenta suka mayar da bikin wurin kwasar garar tande-tande da lashen marasa galihu. Uwar amarya Duane, […]
Wata amarya a Jihar Califoniya da angon da ya kamata ya auret a ya ce ya fasa auren, alhali iyayenta sun kashe kudin biki sama da Dala dubu 35, wato daidai da Naira Miliyan bakwai da dubu 70, sai iyayenta suka mayar da bikin wurin kwasar garar tande-tande da lashen marasa galihu.
Uwar amarya Duane, ta bayyana cewa ’yarta ’yar shekara 27, ta sanar da ita cewa, ita da angonta sun fasa yin auren. Don haka suka yanke cewa tunda ba za a mayar musu da kudin da suka biya a maciyar abinci ba, to su gayyato marasa galihu su kwashi gara.
“Duk da cewa ni da mijina mun ji takaicin al’amarin ga ’yar mu, amma mun samu farin ciki ganin dimbin mutanen da suka ji dadin wannan abinci,” inji Duane.
Ta ce, tuni suka biya kudin kayan tande-tande da lashe-lashen mutum 120 da aka shirya halartarsu wannan bikin aure. Sai kawai mutum 90, marasa gidajen kwana da tsofaffida iyalai masu sabuwar haihuwa suka bayyana, inda suka kwashi room da salada abincin gnocchi da makamantansu. Kai wasu ma har ado suka yi don wannan biki.
Erka Craycraft ta halarci wannan maciyar abinci tare da mijinta da ’yta’yan su biyar. Kuma daga cikin makudan kudin da aka kashe da zummar wannan biki, akwai tafiya yawon shakatawa. Sai kawai wannan uwa da ‘’yarta suka hau jirgi zuwa birnin Belize.
“Ina fatan idan ta yi nazari za ta fahimci cewa, ta juyar da mummunan bakin cikinta zuwa kyakkyawan al’amari,” a cewar Duane.
Wadannan iyalai sun yi dabarar juyar da takaicinsu zuwa ga kyautata wa marasa galihu da ba su kai su ba.