Marayu da zawarawa da tsofaffi sun samu tallafin kungiyar Izala a Ibadan
kananan yara marayu maza da mata da zawarawa da tsofaffi mabukata da yawansu ya kai 600 ne suka samu tallafin suturun sallah daga gidauniyar bayar da tallafi da kungiyar Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah JIBWIS, reshen Jihar Oyo a ranarLahadin da ta gabata a birnin Badun. Marayu 140 da zawarawa 15 ne suka samu wannan […]
kananan yara marayu maza da mata da zawarawa da tsofaffi mabukata da yawansu ya kai 600 ne suka samu tallafin suturun sallah daga gidauniyar bayar da tallafi da kungiyar Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah JIBWIS, reshen Jihar Oyo a ranarLahadin da ta gabata a birnin Badun. Marayu 140 da zawarawa 15 ne suka samu wannan tallafi daga reshen kungiyar na Bodija a yayin da marayu 200 da zawarawa 100 da tsofaffi mabukata su 100 suka samu nasu tallafin kayan sallah daga reshen unguwar Sabo na JIBWIS.
Kayan da aka raba sun hada da turamen atamfa da yadukan shadda da lullubin mata (hijabi) da huluna da takalma da kudin dinkin da aka raba wa marayun da zawarawa da mabukata a wajen kaddamar da wannan gidauniya da aka yi a masallatai biyu na Bodija da Sabo cikin birnin Ibadan.
Da yake jawabi a wajen kaddamarwar ta Bodija, Shugaban kuniyar Izalatul Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah reshen Jihar Oyo, Ustaz Salisu Abdullahi, ya ce, a bana kungiyar ta samu tara kudi Naira miliyan daya da dubu 400 da al’ummar Musulmi suka bayar saboda Allah, domin gudanar da wannan muhimmin aiki. Ya ce, an samu wadannan kudi ne daga reshen kungiyar JIBWIS na Sabo da Bodija da Akinyele da Ojo. Akwai sauran garuruwan Oyo da Ogbomoso da Shaki da Iseyin da ba su riga sun aiko da gudunmawar da suka tara a bana ba.
Sheikh Muhammed Sani Aliyu Adarawa, shi ne babban malamin da hedkwatar JIBWIS daga Abuja ta aika zuwa Jihar Oyo, domin yin wa’azi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Ramadan na bana, ya ce, akwai amfani mai girman gaske ga taimakon zawarawa, domin kare su daga fadawa hannun miyagun mutane da suke yaudararsu ga aikata ayyukan assha.
Yace idan aka taimaka wa zawarawa da suka rasa mazaje masu taimakonsu da abubuwan bukatu daidai gwargwado kuma tsakani da Allah, sannan aka taimaka wa marayun yara da iyayensu suka rigamu gidan gaskiya to, kuwa rayuwarsu za ta yi kyau, ta amfanar da al’ummar Musulmi da kasa baki daya.
Shi kuwa Shugaban reshen JIBWIS na Bodija, Alhaji Sani Ibrahim Jega, cewa ya yi, “mun samu wannan nasara ne a dalilin hadin kai da goyon baya da al’ummar Musulmi suka bayar daidai gwargwado. Saboda haka nake neman mu kara tsarkake zukatanmu da kyakkyawar manufa, domin samun taimakon Ubangiji (TWT).
Shugaban Kwamitin gidauniyar marayu da zawarawa reshen Bodija, wanda shi ne limamin babban masallacin JIBWIS na Bodija, Malam Marwan Musa, ya nuna matukar farin ciki dangane da irin yadda ‘yan uwa Musulmi suke rububin bayar da gudunmawarsu ta kudi da suturu da ya kai ga samun wannan nasara.