Marayu dubu 10 za su amfana da tallafin Zakka a Zamfara

Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Zamfara ta ce a bana marayu dubu 10 ne za ta baiwa tallafi karkashin shirinta na zakka da wakafi. Shugaban Hukumar Malam Bashir Surajo ya bayyana haka a lokacin kaddamar da ba da tallafin da ya gudana a hedikwatar hukumar da ke Gusau a ranar Lahadin da ta gabata. […]

Marayu dubu 10 za su amfana da tallafin Zakka a Zamfara
Marayu dubu 10 za su amfana da tallafin Zakka a Zamfara

Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Zamfara ta ce a bana marayu dubu 10 ne za ta baiwa tallafi karkashin shirinta na zakka da wakafi. Shugaban Hukumar Malam Bashir Surajo ya bayyana haka a lokacin kaddamar da ba da tallafin da ya gudana a hedikwatar hukumar da ke Gusau a ranar Lahadin da ta gabata.

Malam Bashir Surajo ya ce a bara marayu dubu takwas da 300 ne suka amfana da tallafin, amma a bana an samu karin marayu, kuma ya ce marayun za a raba masu buhu dubu bakwai, buhu dubu biyu na masara da dubu biyu na shinkafa da dubu biyu na gero da kuma buhu dubu daya na sukari. Ya ce za a ba marayu shida buhu daidai na shinkafa da masara da gero, kuma kowane ya sami mudunan sukari da yadi biyar na shadda da kudin dinki Naira dubu daya. Shugaban ya ce hukumar ta bai wa kowace masarauta dama ta kawo marayu 400 da za su amfana da tallafin, inda ya ce masarautar Gusau wadda aka bai wa rabo mafi tsoka ta ba da marayu 800. Shugaban ya ce duk wadanda katin rajistarsu ya cika a badi, to sun gama amafana da tallafin ke nen, sai kuma su ba da wuri don wasu su samu, kamar yadda yake an tsara tallafin ne na shekara hurhudu.