Marayu na jayayya da Muhammad Abacha a kan gida
Wani matsahi, Ahmad Sulaiman dan shekara 30, ya koka a kan abin da ya kira yunkurin nuna fin karfi da neman kwace gidansu na gado, wanda Muhammadu Abacha yake neman yi musu, a sakamakon rasuwar mahaifinsu, Alhaji Abubakar Sulaiman.Ahmad ya ce gidan nasu da Muhammad Abachan yake ikirarin nasa ne, shi ne mai lamba 6A […]
Wani matsahi, Ahmad Sulaiman dan shekara 30, ya koka a kan abin da ya kira yunkurin nuna fin karfi da neman kwace gidansu na gado, wanda Muhammadu Abacha yake neman yi musu, a sakamakon rasuwar mahaifinsu, Alhaji Abubakar Sulaiman.
Ahmad ya ce gidan nasu da Muhammad Abachan yake ikirarin nasa ne, shi ne mai lamba 6A da ke kan titin Gidado kuma yake makotaka da gidan iyalan marigayi Janar Sani Abacha, mai lamba 8 a kan wannan titi dai a birnin Kano.
Ya ce: “Bayan rasuwar mahaifinmu ranar 17 ga watan Agustar 2012 da kimanin watanni shida, Muhammad Abacha ya nuna bukatarsa ta sayen gidanmu, amma kuma har aka yi shekaru biyu bai sake yin maganar ba, har muka sayar wa A.Y. Maikifi gidan a kan Naira miliyan 150.”
Ya ce bayan sun sayar da gidan ne, har wanda ya sayi gidan ya saka wadansu mutane a ciki, sai Muhammad Abacha ya kore su daga gidan da nufin cewa gidansa ne. A sakamakon hakan ma har ya sa ’yan sanda suka kira Ahmad tare da wansa Kabiru zuwa ofishin Mukaddashin Sufeto Janar na ’yan sanda na shiyya ta daya da ke Kano, don a tuhume su.
Ya kara da cewa a sakamakon wannan barazanar da Muhammad Abacha yake yi wa rayuwarsu ne, sai suka shigar da kara gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, domin ta hana Muhammad cin zarafinsu, tare da yin bincike a kan wanda yake da hakikanin mallakar wannan gidan.
Ahmad ya kara da cewa: “Mu shida mahaifinmu ya rasu ya bari, tare da mahaifiyarmu, Hajiya Habiba Sulaiman, kuma tun a ranar 10 ga watan Yuli na bana ne kotu ta raba mana gado, har da shi wannan gida da mahaifinmu ya bari.
“Yau shekarata 30 kuma ni ma a wannan gidan aka haife ni har na kawo wannan lokacin kuma mahaifinmu tsohon ma’aikacin kamfanin UAC ne, wanda ya mallaki wannan gida daga kamfanin na UAC ta hanyar adashin gata kuma ya gama biyan komai da komai kuma muna da cikakkun takardun gidan.”
Ya kara da cewa a kokarin Muhammad na mallakar gidan har sai da ya yi amfani da wasu tsofaffin jami’an hukumar kasa da safiyo, suka yi masa takardun da zimmar cewa shi ne mai gidan. Sannan kuma ya zargi Muhammad Abacha da yin amfani da karfinsa da matsayinsa, wajen sanya ’yan sanda su tursasa musu.
A yayin da wakilin Aminiya ya tuntubi Muhammad Abacha ta waya, ya ce ya mallaki gidan ne daga kamfanin UAC kuma ban da wannan gidan ma ya sayi kadarori kimanin guda 10 daga UAC. Ya ce: “A je Kano da ko’ina ne a tambaya, na taba zuwa na ce gidan wadansu nawa ne? Tun da kuwa hakan ya faru lallai da dalili. Mu ba yara ba ne da haka kawai za mu ce gidan wadansu namu ne, sai da hujja.”
Ya kara da cewa marigayi mahaifin su Ahmad ya roki alfarmar zama a gidan ne tun a shekara ta 1997 kuma idan har su Ahmad suna da takardar mallaka wacce mahaifinsu ya sayi gidan, ai sai su nuna wa kotu, tun da sun kai maganar kotu kuma suna shiga jaridu suna yadawa. Ya kuma ce tun da yanzu lokacin siyasa ne, wasu za su so yin haka don neman bata masa suna, amma wannan ba zai hana ya nemi hakkinsa ba. Ya ce: “Tun da maganar tana gaban kotu sai mu sa ido mu ga waye mai gaskiya.”