Marhabin Baba Buhari

A ranar Asabar da ta gabata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya daga Ingila, bayan kwashe kwanaki 103 yana jinya. Domin taya murna, Bashir Yahuza Malumfashi (08065576011) ya tsara wadannan baituka guda 11:   Godiyarmu ga Allah, Da Shi Ya raya ka.   Mun yabo ga ma’aiki, Shumagaban tsarkaka.   Jinya ba mutuwa ba, […]

Marhabin Baba Buhari

A ranar Asabar da ta gabata, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya daga Ingila, bayan kwashe kwanaki 103 yana jinya. Domin taya murna, Bashir Yahuza Malumfashi (08065576011) ya tsara wadannan baituka guda 11:

 

Godiyarmu ga Allah,

Da Shi Ya raya ka.

 

Mun yabo ga ma’aiki,

Shumagaban tsarkaka.

 

Jinya ba mutuwa ba,

Ga wasu na gorin ka.

 

Sun so ka mutu,

Allah Ya ki kashe ka.

 

Sun so ka gaza,

Allah shi Ya hana ka.

 

Sun nufe ka da cuta,

Allah shi Ya kare ka.

 

Aikinka na dada kyawo,

Kullum suna zagin ka.

 

Ka bi dokar tsari,

Burinsu su kwashe ka.

 

Ka mike tsaye kikam,

Sun gaza danne ka.

 

Allah ne Ya tsaya ma,

Yau ba mai kore ka.

 

Kullum muna bayanka,

Rokonmu Allah kare ka!         

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume