Marigayi dankwairo: Wakar Mai Hawan Nasara dan Bayero
Marigayi dankwairo shahararren mawakin Hausa ne na gargajiya. Haka kuma Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero shahararren sarki ne a kasar Hausa da Najeriya baki daya. Har ila yau dai, wakar ‘Mai Hawan Nasara dan Bayero’ wato wadda shi dankwairon da jama’arsa suka rera wa sarkin, ta kasance shahararra. ABDULLAHI SALIHU ABUBAKAR (BABAN SADIk) ya […]

Marigayi dankwairo shahararren mawakin Hausa ne na gargajiya. Haka kuma Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero shahararren sarki ne a kasar Hausa da Najeriya baki daya. Har ila yau dai, wakar ‘Mai Hawan Nasara dan Bayero’ wato wadda shi dankwairon da jama’arsa suka rera wa sarkin, ta kasance shahararra. ABDULLAHI SALIHU ABUBAKAR (BABAN SADIk) ya zakulo wakar kuma ya rubuce ta tsaf. Ga ta a nan mun kawo muku domin debe kewa kuma domin ta’aziyya ga mawakin da kuma sarkin. Allah Ya jikansu, amin!
Ado na Abbas,
dan Hashim shirinka shirin yaki ne.
Ado na Abbas,
dan Hashim shirinka shirin yaki ne.
Kana da halin mutanen da,
Akwai na mutanen yanzu.
Sarki, kana da halin mutanen da,
Akwai na mutanen yanzu.
To shi ko shirin mutanen da,
Shirinsu shirin yaki ne.
In kai magana ta zamna,
To kuma ba ka da mai canzawa.
To shi ko shirin mutanen yau,
Shirinsu shirin ilimi ne,
Akwai ilimi gun…
Na tabbtar,
Akwai ilimi gun Ado.
Jama’a, ina tambayarka Ado.
Ka san Dabo ya zamo sarki,
Abdullahi Majekarofi…
Shi ma ya zama, sarkin Kano
Abbas ya zama sarki.
Bayero ya zama sarki.
Kai ko ka zama sarki Alhaji…
Shin wai mi kaka tsoro?
Alhaji….
Shin wai mi kaka tsoro?
Mu kara fadar maganar ad daidai.
Kar ka bari ana fada ma,
Mike bugi kan Buzaye!
Zaki, mike bugi kan Buzaye!
Randa duk Buzu yaj ja daga,
Ya kama gudu sai Tawa.
Mai takura kaurin gaba,
Na yarda da Sarki Ado.
Mai hawan nasara dan Bayero,
Tafe dai yake bai fasa ba.
Mai hawan nasara dan Bayero,
Ado tafe dai yake bai fasa ba.
Ya yi shiri zai je Hadeja,
Ya yi shirin jama’a tai,
Hakimmai na kasar Kano,
Duk sun hallara kofar Kudu.
Sarki ko da ya’ iso,
Shu’aibu sarkin mota,
Ya dafa motar Sarki,
Yana ga Sarki ya fito.
Ga Ado dan Ado,
Ado babba dan babba,
Tafe dai yake bai fasa ba.
Har mun ka je Jogana,
Kuma mun karasa a Gezawa,
Mutane sun zo bakin titi,
Kowa ya yi gaisuwa.
Alhaji Ado Bayero,
Tafe dai yake bai fasa ba.
Mai hawan nasara dan Bayero,
Tafe dai yake bai fasa ba.
Har mun ka je a Ringim,
Mutanen da suke Ringim,
Kowa ya fito bakin titi yana gaisuwa ga Sarki.
Mai hawan nasara dan Bayero
Tafe dai yake bai fasa ba.
Mai hawan nasara dan Bayero
Tafe dai yake bai fasa ba.
Kahin mu karasa Hadeja,
Sarkin Hadeja, Sarkin Gomel,
Tafe da sauran sarakuna,
Sun tari Ado Bayero.
Ko da mun ka je cikin Hadeja,
Duk mun hallara hili,
Gwamnoni guda goma
Da sauran sarakunan Nijeriya,
Kowa ya mike tsaye,
Yana gaisuwa ga Sarki.
Mai hawan nasara dan Bayero,
Tafe dai yake bai fasa ba.
Ado tafe dai yake bai fasa ba.
’Yan Hadeja sun ga rinjaya,
Sun ga Ado Bayero.
Alkyabbar da yash shirya
Da kaya nai na jiki nai,
Alkyabbar wani sarki,
Ba ta sayan wannan alkyabbar;
Albashin wani sarki,
Na shekara ashirin da biyar,
Ba zai sayi alkyabbar ba.
Wannan ba zai sayi alkyabbar ba!
Mai hawan nasara dan Bayero,
Tafe dai yake bai fasa ba.
Ado tafe dai yake bai fasa ba.
Ka takura kaurin gaba,
Na yarda Sarki Ado.
Na Ibrahim Dabo ya zauna,
Mu je birni mu fado ma Kanawa,
Su zo su gaishe ka.
Kai Allah yaz zaba.
Alhaji kai Allah yaz zaba.
Mai takura kaurin gaba,
Na yarda da Sarki Ado
Sarki mai sandar yaki,
Kama dala’ilunka ya kama,
Duk kasar Kano ga baki dai
Kowa na murna tai.
Sarki mai sandar yaki
Kama dala’ilunka ya kama
Duk kasar Kano ga baki dai
Kowa na murna tai.
Ado, kowa na murna tai.