Marigayi Garba Gadi: Babban bango ya fadi
Mutuwa rigar kowa kuma sananne cewa kowane mai rai mamaci ne, sai dai rasuwar wadansu takan girgiza jama’a kamar yadda rasuwar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Muhammadu Garba Gadi Danburam din Katagum ta ksance rasuwar da ta girgiza al’ummar Jihar Bauchi da Najeriya, saboda dimbin gudunmawar da ya bayar wajen gina al’umma ta fuskar […]
Mutuwa rigar kowa kuma sananne cewa kowane mai rai mamaci ne, sai dai rasuwar wadansu takan girgiza jama’a kamar yadda rasuwar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Muhammadu Garba Gadi Danburam din Katagum ta ksance rasuwar da ta girgiza al’ummar Jihar Bauchi da Najeriya, saboda dimbin gudunmawar da ya bayar wajen gina al’umma ta fuskar siyasa da tattalin arziki.
Alhaji Garba Gadi wanda ya zama Mataimakin tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda a tsakanin shekarun 2007 zuwa 2011, sun raba gari da Gwamnan ne lokacin da tsohon Gwamnan ya koma Jam’iyyar PDP daga Jam’iyyar ANPP wadda ta kai su gadon mulki. Yuguda ya nemi Garba Gadi ya koma PDP, amma ya ki, ya yi zamansa a ANPP hakan ya sa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta tsige shi daga mukaminsa kuma tsohon shugaban majalisar, Babayo Garba Gamawa ya zama Mataimakin Gwamna. Daga baya kotu ta soke tsigewar da aka yi masa amma gwamnatin jihar ta daukaka kara zuwa Kotun Koli a sharia’ar da ake ta yi tsawon shekara bakwai har ya bar duniya.
Marigayin ya bar duniya ce a ranar Talatar makon jiya a kasar Indiya inda ya yi fama da jinya kuma an dawo da gawarsa Najeriya ranar Juma’a inda aka yi masa jana’iza ranar Asabar din da ta gabata a kofar fadar Sarkin Katagum, inda dubban mutane daga sassan Najeriya ne suka halarci jana’izarsa.
Galadiman Katagum Alhaji Usman Mahmud Abdullahi ya ce kafin rasuwar Alhaji Garba Gadi shi wakili ne a Majalisar Sarkin Katagum, kuma ya rasu ne yana da shekara 71. Ya bayyana rashinsa a matsayin babban rashi, idan aka yi la’akari da rawar da ya taka wajen gina kasar nan a matakai daban-daban. Ya ce masarautar ta samu gibi mai wuyar cikewa. Kuma ya ce za a dade ana tunawa da gaskiya da hazakar marigayin wanda hakan ya sa ya kasance daya daga cikin dattawan kasar nan. Sai ya roki Allah Ya jikansa Ya gafarta masa.
Wani mai sharhi kuma marubuci kan al’amuran yau da kullum Alhaji Musa Azare ya ce “Mun yi rashin uba tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, tsohon shugaban da ya jagoranci wakilan tsohuwar Jam’iyyar CPC lokacin da za a yi hadakar jami’yyu da ya kai ga aka kafa Jam’iyyar APC. Dattijon kirki mutum mai mutunci da karimci, mai magana daya ba ya sauyawa don kwadayi ko neman abin duniya. Za a ci gaba da tuna jajircewarsa lokacin da yake Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi inda ya ki komawa Jam’iyyar PDP wanda hakan ya yi sanadiyyar tsige shi. Ya rasu yana ci gaba da gwagwarmaya don gani ya kwato hakkinsa game da tsige shi da aka yi ba bisa ka’ida ba. Wannan shari’a tana Kotun Koli,” inji Azare. Ya ce ’yan Najeriya da al’ummar Jihar Bauchi sun rasa gwarzon dan siyasa mai kishin kasa. “Rasuwarsa gare ni babban rashi ne domin yana daya daga cikin iyayen gidana a siyasa. Allah Ya jikansa Ya sa shi a Aljannar Firdausi” ya yi masa addu’a.
Yawancin mutane da muka zanta da su a fadar Sarkin Katagum sun bayyana marigayi Garba Gadi a matsayin uba, jagora, malami, babban bango da a kowane lokaci yake zama majingina ga talakawa. Mutum ne da ke da natsuwa da sauraron jama’a da ba da dama da uziri ga kowa saboda kyakkyawan zaton da yake da shi a tsakaninsa da kowa. Sun yi addu’ar Allah Ya jikansa Ya gafarta masa.
Sun shawarci Gwamnatin Jihar Bauchi ta kawo karshen shari’ar da take yi da shi kan tsige shi ba bisa ka’ida ba daga mukamin Mataimakin Gwamna da gwamnatin Yuguda ta yi, kuma ta biya iyalansa dukan hakkokinsa, sannan ta kula da bayansa bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen gina Jam’iyyar APC da ayyukan alherin da ya yi a jihar da kasa baki daya.
Marigayi Garba Gadi ya fara takarar siyasa ce a lokacin marigayi Janar Sani Abacha, inda ya tsaya takara Sanata daga Bauchi ta Arewa ya samu nasara, amma rasuwar Abacha ta sa aka yi watsi da shirin komawa ga mulkin farar hula. Da aka sake kada kugen siyasa a 1999, Garba Gadi ya sake yin takarar Sanata amma marigayi Shettiman Katagum Alhaji Bashir Mustafa ya kada shi.
Bayan tsige shi daga Mataimakin Gwamna ya koma ofishin tsohuwar Jam’iyyar CPC a Matsayin Shugaban Ma’aikata, daga nan ne ya jagoranci wakilan jam’iyyar zuwa tarurrukan hadakar jam’iyyu da suka kafa Jam’iyyar APC.
Kafin rasuwarsa shi ne Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe.
A sakonsa na ta’aziyya ga iyalai da gwamnati da al’ummar Jihar Bauchi, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rasuwar Garba Gadi a matsayin babban rashi ga kasar nan. Sakon wanda Kakakin Shugaban Kasar Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu ya ce “Najeriya ta yi rashin mutumin kirki mai mutunci wanda ke tsayuwa kan magana daya ya hakura a wurin ba tare da kwadayi ba.”
Shugaban Kasar ya kara da cewa a cikin ’yan siyasa akwai na kwarai, ya ce Garba Gadi daya ne daga cikin ’yan siyasa mutanen kirki. Ya ce yana mutunta marigayin kwarai da gaske saboda biyayyarsa da gaskiyarsa, sai ya roki Allah Ya jikansa Ya gafarta masa.
Babban Limamin Katagum, Malam Ayuba Muhammad ne ya jagoranci Sallar Jana’izar marigayin yayin da Hakimin Shira Alhaji Baba Umar Faruk ya wakilci Mai martaba Sarkin Katagum. Sauran wadanda suka halarci jana’izarsa sun hada da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Alhaji Mahmud Yayale Ahmed da Dokta Bello Katagum da Sanata Babayo Garba Gamawa da Alhaji Halliru Dauda Jika dan Majalisar Tarayya na mazabar Ganjuwa/Darazo da dubban Musulmi.
Gwamnan Jihar Bauchi, Barista Muhammad Abubakar, ya ce jihar ta yi rashin gwarzon dattijio mai gaskiya da sadaukar da kai. Ya ce dimbin jama’ar da suka halarci jana’izar marigayin ya nuna yadda mutane suke kaunarsa.