Marigayi Limamin Jos ya bada gudunmawa kan zaman lafiya a Filato – Gwamna Lalong

Sabon Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya ce marigayi Babban Limamin Jos Sheikh Balarabe Dawud, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Lahadin da ta gabata, ya bada gagarumar gudunmawa wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, inda ya bayyana rasuwarsa da babban rashi ga jihar da Najeriya baki daya. Gwamna […]

Marigayi Limamin Jos ya bada gudunmawa kan zaman lafiya a Filato – Gwamna Lalong
Marigayi Limamin Jos ya bada gudunmawa kan zaman lafiya a Filato – Gwamna Lalong

Sabon Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya ce marigayi Babban Limamin Jos Sheikh Balarabe Dawud, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Lahadin da ta gabata, ya bada gagarumar gudunmawa wajen kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar, inda ya bayyana rasuwarsa da babban rashi ga jihar da Najeriya baki daya.

Gwamna Simon Lalong ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziya ga iyalan marigayin a gidansa da ke Jos, inda ya ce marigayin a matsayinsa na shugaban addini ya taimaka wajen ganin an samu canji a lokacin zabubbukan da suka gabata.
Ya ce marigayin Babban Limamin ya yi kokarin haka ne domin ya ba da gudunmawarsa wajen kawo zaman lafiya da ci gaba a Najeriya. “Marigayin ya fada mini cewa babban fatarsa, shi ne mu kasance masu gaskiya da rikon amana a wannan matsayi da aka zabe mu. Don haka gwamnatinmu ba za ta taba mantawa da marigayin ba,” inji shi.
Shi ma da yake jawabi a lokacin da ya kai ta’aziya ga iyalan marigayin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce marigayin uba ne kuma shugaba ne mai gaskiya wanda ya yi ayyukansa bisa tsoron Allah a lokacin da yake raye.
Ya ce, “Ya koyar da mu ayyuka da dama da za su taimaka mana a harkokin rayuwa, “Babbar damuwata ita ce yadda za a cike gurbin da marigayin ya bari. Ina kira ga babban dan marigayin ya yi kokari ya hada kan iyalan marigayin tare da rike ayyukan gaskiya da marigayi ya yi a lokacin da yake raye,” inji shi.
Shi ma Akibishop na darikar Katolika ta Jos kuma Shugaban Majalisar Bishop-Bishop din Katolika ta Najeriya, Akibishop Ignatius Kaigama da ya kai ziyarar ta’ziyya ga iyalan marigayin, ya bayyana cewa “Mun yi ayyuka da dama kan samar da zaman lafiya tare da
marigayin ba tare da nuna wata gajiyawa ba. Kuma tunda muke tare da shi bai taba kin halartar duk wata gayyatar taron zaman lafiya da muka yi masa ba, a kullum marigayin yana cikin ayyukan samar da zaman lafiya.”
Marigayi Sheikh Balarabe Dawud wanda ya rasu a asibitin Grace bile Royal da ke Dadin Kowa a kusa da Jos bayan gajeruwar rashin lafiya, ya rasu yana da shekara 82, inda ya bar mace daya da ’ya’ya 10 maza da mata da jikoki da dama.
Marigayin wanda aka nada shi Limamin Jos a shekarar 2009 ya yi karatu a Jami’ar Al-Azhar da ke Masar, kuma shi ne shugaban Majalisar Musulmin Jos da ake kira Ulama Elders Council, kuma ya kasance dan kwamitin da Shugaban kasa ya kafa a kan rikicin da aka yi a Jos.