Marigayi Sardauna Ahmadu Bello: Ba rabo da gwani ba!
A ranar 15 ga Janairun 1966 ne aka yi wa Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Arewa Alhaji Sa Ahmadu Bello kisan gilla. Sai dai har zuwa yau kwarjini da ayyukan kirkin da ya shimfida a Arewa suna ci gaba da haskakawa. Dalili ke nan a yau, marubuci MALAM ISHAkA SARKIN FULANI DANKAMA (08100006858), mai adireshin […]
A ranar 15 ga Janairun 1966 ne aka yi wa Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Arewa Alhaji Sa Ahmadu Bello kisan gilla. Sai dai har zuwa yau kwarjini da ayyukan kirkin da ya shimfida a Arewa suna ci gaba da haskakawa. Dalili ke nan a yau, marubuci MALAM ISHAkA SARKIN FULANI DANKAMA (08100006858), mai adireshin I-mel: [email protected] ya rubuta wannan tsokaci a matsayin tunawa da shi. Ga abin da yake cewa:
Allah Mai yadda Ya so! Mutanen duniya kowa yana da sha’awar shiga Aljanna amma babu mai sha’awar mutuwa.
Idan ana ba da labarin wani mutum mai halaye na gaskiya, adalci da rikon amana, sai ka rika sha’awarsa, amma me ya sa kai ba ka iya daukar matakin da za ka kai fagen da wancan mutum ya kai, ko ma ka yi fiye da adalci, gaskiya da rikon amanarsa ko da a mulkin iyalinka?
Duk mutumin da Allah Ya sa yake raye a yau a Arewacin kasar nan, kuma shekarunsa ba su kasa 40 ba, ya samu akalla takaitaccen labari, tarihin wane ne Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Jihar Arewa. Ko dai labarin ya samu ne a kafofin watsa labarai, wato jaridu, kasidu, littattafai, wakokin Hausa, rediyo, talabijin, ko a muhimman gine-gine, ko kunne-ya-girmi-kaka.
Marigayi Sa Ahmadu Bello, shi ne Firimiyan Jihar Arewa na wancan lokaci, jihar da a yau aka yanka ta, aka kirkiro jihohi 19 da ke kunshe da kananan hukumomi 407. Matsayin da Sa Ahmadu Bello ya rike ya kai a kwatanta shi daidai da na Firaminista ko Shugaban kasa ga mutanensa na Arewa.
Yau kimanin shekara 50 da suka gabata Allah Ya amshi ran jangwarzo, jarumi, adali, mai gaskiya Sa Ahmadu Bello da wasu ’yan ta’adda suka harbe da bindiga a ranar 15 ga watan Janairu, 1966 a gidansa. Mutumin da a kullum kewarsa na zukatan al’ummarsa na Arewa, domin adalcinsa da nasarorin da ya samu a lokacin wa’adin mulkinsa na Firimiyan Arewa.
Ya kamata mu lissafa kadan daga cikin ayyukan raya kasa da adalci da kyakkyawan jagoranci na Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello domin mai karatu ya sani ko da ba zai yarda ba. Wasu daga nasarorin da Firimiyan ya samu sun hada da:
Gudummuwarsa kan harkokin ilimi, inda ya ba da umarnin gina makarantun firamare da sakandare har da na gaba da sakandare da jami’a. Daga cikin makarantun da ya kaddamar da bikin bude su har da Makarantar Horon Malamai ta Wudil, a ranar 27 Nuwamba 1965.
Ya bude Kwalejin Horon ’Yan sanda ta Kaduna a ranar 30 Nuwamba, 1963. Ya bude Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Polytechnic) da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru Zariya a ranar 11 Oktoba 1962.
A fannin ruwan sha da noma ga jama’a, Firimiyan ya gina madatsun ruwa domin noman rani da kiwo, ma’aikatun ruwa da rijiyoyi a lardunan Arewa. Ya kaddamar da bude Ma’aikatar Ruwa ta Daura a ranar 23 ga Nuwamba, 1960. Ya bude Ma’aikatar Ruwa ta Mando-Kaduna a ranar 25 ga Maris 1960.
A fannin lafiya, Firimiyan ya gina asibitoci a larduna da asibitin kashi guda daya tilo a Dala da ke birnin Kano a ranar 21 Disamba 1959. Asibitin da ya dauki nauyin kula da majinyata kashi daga jihohin Arewa 19, a tsawon shekara 45 bayan kafa shi. Bayan wannan shekaru an samu wasu gwamnoni uku ko hudu da suka gina asibitocin kashi a jihohinsu.
A fannin tattalin arzikin kasa, Firimiyan Arewa ya gina bankuna, ya bude Bankin Baclyas da yanzu ake kira Bankin Al’umma (Union Bank) na farko a Arewa a ranar 15 Satumba 1956. Haka ma shi ne ya bude Bankin Arewa (Bank of the North) da aka mai da shi Unibersal Bank. Ya bude Hukumar Wutar Lantarki ta Arewa (ECN) a garin Bida a ranar 1 ga Janairu 1961. Ya kuma bude otel din Hamdala da ke garin Kaduna a ranar 27 ga Fabrairu 1960.
Sauran nasarorin da Firimiyan Arewa ya samu sun hada har da bude kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo. Da kamfanin simunti na Arewa a Sakkwato da Masakar Arewa a Kaduna da ta Gusau da Gidan Rediyo da Talabijin na Kaduna (Farin Gida) da filin wasa na Kaduna da sauransu.
Baya ga kadan daga nasarorin da aka lissafa a baya, Firimiyan ya rike sakatarensa wanda ba addininsu daya ba, ba kabilarsu daya ba, har tsawon karshen rayuwarsa.
A nan muna ta lalube mu samo daya daga hadimai, abokai, aminai, ministoci ko abokan aikin Firimiya da ya dauki darasi daga dabi’u ko halayensa, ya aiwatar ga jama’arsa a matsayin da ya taba rikewa ko yake rike da shi a yau. Mutumin da ba ya nuna kabilanci, mai gaskiya, mai rikon amana kamar na Firimiyan Arewa duk da cewa Firimiyan Arewa yana da ministoci guda 17 da kananan ministoci bakwai a karkashin Jihar Arewa. Kuma a lolacin Hukumar kidaya ta kasa a 1963 ta tabbatar da mutanen Najeriya sun kai miliyan 55 da dubu 620 da 268 ne, daga cikinsu Jihar Arewa na kunshe da mutum miliyan 29 da dubu 758 da 875. Yayin da Jihar Gabas ke da mutum miliyan 12 da dubu 394 da 462, sai Jihar Yamma da ke da mutum miliyan 10 da dubu 256 da 846. Sai Yamma ta Tsakiya mutum miliyan 2 da dubu 558 da 879. Legas na da mutum dubu 665 da 246.
Yau kimanin shekara 50 da rasuwar Ahmadu Bello, muna cigiyar wanda ya rike mukamin jiha daya daga cikin jihohi 19, ko ya rike mukamin shugaban karamar hukuma daga kananan hukumomi 407 da Firimiya ya shugabanta a lokacinsa, da jama’arsa za su ba da shaidar ya yi adalci, ya dogara da albashinsa, ya yi gaskiya, ya yi ayyukan raya kasa ga jama’arsa irin na Firimiya.
Duk da matsayin da Firimiyan Arewa ya rike na shugaban Jihar Arewa, ya rasu ba tare da ya bar abin da ya mallaka na kansa, ko ya sata, ko ya kwace, ko handama ko babakere na daga dukiya, ko kudi, ko motoci, ko gidaje ko kamfanoni a kasarsa ko kasar waje ba. A karshe dai gidansa biyu. Wannan ya yi daidai da jawabinsa, inda ya ce:
“Na sadaukar da kaina in yi aiki ba tare da gajiyawa ba, domin ci gaba da farin cikin sabuwar Arewa. Na yi rantsuwa da sunan Allah idan har na rasu ba zan bar komai ba amma sai dai gwagwarmaya domin ’yanci, mutunci, da martabar kasar nan.”