Mario Mandzukic ya koma Jubentus
Shahararren dan kwallon Kuroshiya da yake buga kwallo a kulob din Atletico Madrid na Sifen Mario Mandzukic ya koma kulob din Jubentus na Italiya. dan kimanin shekara 29, wanda a bara ne ya koma kulob din Atletico Madrid na Sifen daga Bayern Munich na Jamus, ya zura wa kulob din Madrid kwallaye 20 daga cikin […]
Shahararren dan kwallon Kuroshiya da yake buga kwallo a kulob din Atletico Madrid na Sifen Mario Mandzukic ya koma kulob din Jubentus na Italiya.
dan kimanin shekara 29, wanda a bara ne ya koma kulob din Atletico Madrid na Sifen daga Bayern Munich na Jamus, ya zura wa kulob din Madrid kwallaye 20 daga cikin wasanni 43 da ya yi mata a kakar wasan da ta wuce.
Rahotanni sun ce sai da kulob din Jubentus ya ajiye wa Atletico Fam miliyan 13.6 kafin ta amince masa ya camza shekar.
“Ina ssha’awar Jubentus, ina sha’awar birnin Turin, ina kuma fatar zan samu nasara a nan kuma zan yi kokari na ga na taimaka wa kulob din don ganin mu samu nasara a kakar wasa mai zuwa”, inji shi a lokacin da kulob din yake gabatar da shi ga dimbin magoya bayansa.
Da wannan canza sheka da Mandzukic ya yi, alamu sun nuna dan kwallon gabansu Carlos Tebez zai bar kulob din musamman ganin yadda shahararren dan kwallon duniya Deigo Maradona ya kyankyasa wa duniya a karshen makon jiya cewa Tebez zai koma kulob din Boca Juniors ne a kakar wasa mai zuwa don cigaba da kwallo.