Marka-marka a Kuros Riba na kawo cikas ga harkokin kasuwanci
Ciniki sai a hankali, domin kwashe na jiya na yi na sake ɗumamawa na fito da shi.
Marka-Marka lokaci ne da ruwan sama ke iya shafe kwana uku yana sauka ba tare da ya ɗauke a Kudu maso Kudancin Nijeriya musamman a Jihar Kuros Riba.
Aminiya ta zagaya unguwannin da ’yan asalin Arewa ke neman abincinsu ta hanyar sana’o’i daban-daban.
- Za a shafe kwana uku ana marka-marka a jihohin Arewa
- Dalilin da muka shirya addu’o’i ga marigayi Jagaban – ’Yan Arewa Magoya Bayan APC
A Unguwar Hausawa, wasu masu sayar da ɗanye da dafaffen kayan abinci suna kukan yadda mamakon ruwan sama ya hana masu sayen abinci fitowa balle su saya daga gare su.
Malama Zulai Shehu mai sayar da abinci a Unguwar Hausawa, ta shaida wa Aminiya cewa “Mu yanzu ciniki sai a hankali, domin kwashe na jiya na yi na sake ɗumamawa na fito da shi, saboda ruwan sama ya kore mana abokan ciniki.
“Kazalila yanzu wanda bai saba da irin wannan ruwan saman ba yana ɗaki yana jiran har sai an ɗauke ya fito musamman wanda ke nesa da Unguwar Hausawa.”
Malam Ibrahim Musa wani mai sayar da kayan abinci ya koka kan yadda ruwan markamarka ke jawo musu cikas a kasuwancinsu.
A kasuwar da ake sayar da garin kwaki kuwa ’yan kasuwar sun ce da zarar an shigo yanayi na damina, to, su fa sai abin da hali ya yi, musamman yadda ake samun ruwa ba ƙaƙƙautawa a garin Kalaba.
A cewar wata mai suna Angenes da ke sayar da garin kwaki, da zarar ruwa ya taɓa garin sai ya kumbura ya lalace.
Ta ce suna da abokan hulɗa da ke zuwa daga Arewa irin su Kano, Kaduna, Zariya da sauransu, amma yanzu duk sun daina zuwa saboda ruwan sama.
Sai dai a ɓangaren masu gasa nama, sun ce su kasuwa ce ta buɗe musu.
Malam Ibrahim Yusuf wani mai sayar da nama ya ce a irin wannan lokaci na ruwan sama suke cin kasuwarsu domin an fi zuwa a sayi gasasshen nama domin idan mutum yana son cin wani abu mai zafi da maida yawu, sai ya ƙaraso wajensu.
Malam Salisu Saminu mai sayar da shayi ya ce kasuwa sai godiya, domin yanzu kasuwar ta buɗe masu.
“Ka san ruwan saman nan da ake yi da zarar ya ɗauke kowa na neman abin da zai ɗumama jikinsa, don ya kori sanyi, shi ya sa ka ga da zarar wannan ta ƙare ga wata tukunyar tana jira,” in ji shi.