Marseille ta raba gari da kocinta Habib Beye
Majiyoyi sun nuna cewa Bruno Genesio, wanda ya bar Lille kwanan nan, shi ne ke kan gaba wajen maye gurbin Beye.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Marseille ta Faransa ta sanar da raba gari da kocinta, Habib Beye, bayan ya gaza jagorantar ƙungiyar zuwa samun gurbin shiga Gasar Zakarun Turai.
A cikin wata taƙaitacciyar sanarwa da ta wallafa a shafinta na intanet ranar Talata, Marseille ta ce ta kawo ƙarshen yarjejeniyarta da Beye, tare da yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.
- HOTUNA: Sakkwatawa 18 sun mutu a hatsarin mota yayin dawowa daga Legas
- Adadin waɗanda ambaliyar ruwa ta kashe a Ghana ya kai 12
Tsohon ɗan wasan baya kuma tsohon kyaftin ɗin Marseille, Beye, ya karɓi ragamar horar da ƙungiyar ne a tsakiyar watan Fabrairu bayan tafiyar Roberto De Zerbi.
An ɗora masa nauyin tabbatar da ƙungiyar ta samu tikitin shiga Gasar Zakarun Turai amma ya gaza, sai dai ya jagoranci Marseille zuwa matsayi na biyar a teburin Ligue 1, wanda ya ba ta damar shiga Gasar Europa League.
A lokacin da yake jagorantar ƙungiyar a filin wasa na Stade Vélodrome, Beye ya yi nasara a wasanni shida, ya yi canjaras biyu, sannan ya sha kashi a wasanni biyar.
Ana sa ran Marseille za ta sanar da sabon kocinta cikin ’yan kwanaki masu zuwa.
Rahotanni daga majiyoyi a cikin ƙungiyar sun nuna cewa Bruno Genesio, wanda ya bar Lille kwanan nan, shi ne ke kan gaba wajen maye gurbin Beye.
Batun naɗin sabon kocin Marseille ya ɗan tsaya cik a farkon watan Yuni bayan UEFA ta ƙaƙaba wa ƙungiyar takunkumi saboda kasa cika wasu ƙa’idojin da suka shafi daidaita kuɗaɗen shiga da kashewa.