Martabar Annabin Allah: Jan hankali Ga Gwamnatin Jihar Kano
Malam Hamza Dawaki (08034753238), mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya yi tariya, ya yi tsokaci sannan ya yi kira na musamman ga hukumomin Jihar Kano, domin su dauki matakin da ya dace a kan wani mutum da a kwanakin baya aka samu ya ci mutuncin Manzon Allah, Muhammadu (saw). Ga abin da malamin […]
Malam Hamza Dawaki (08034753238), mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya yi tariya, ya yi tsokaci sannan ya yi kira na musamman ga hukumomin Jihar Kano, domin su dauki matakin da ya dace a kan wani mutum da a kwanakin baya aka samu ya ci mutuncin Manzon Allah, Muhammadu (saw). Ga abin da malamin yake cewa:
Annabin Allah wani mutum ne da babu wanda ya kai shi daraja da kima a idon duniya! Ko da kuwa za a ajiye batun addini a gefe, idan ka auna shi da dukkan halittun duniya, za ka tarar ya yi musu fintinkau a halitta da dabi’a da kamala da kaifin hankali da natsuwa da basira da kwarewa wurin iya mu’amula da tsarin jagoranci da warware matsaloli da azanci da dukkan sauran halaye da ke nuna cikar mutum.
Na san da yawa daga cikinmu, idan an ambaci Annabi MUHAMMAD (saw), hankalinmu yakan tafi a kan cewa kawai tun da Annabi ne, mu kuma a matsayinmu na Musulmi dolenmu mu ga darajarsa, fauka kulli.
kwarai haka ne kuma wannan wajibi ne amma fa ya kamata mu gane cewa, idan har ka tsaya a iya hakan, tabbas ka rage wa kanka dandanon zakin son Annabin. Ina ganin idan har kana son ka more a soyayyarsa, to lallai ya kamata ka tashi ka kara nazari da bincike game da shi da hali da dabi’a da kuma yadda ya tafiyar da rayuwarsa. Sannan idan har kana so ka san daraja da girma da mutunci da martabarsa, to ya kamata ka bibiyi yadda mutane suke ganin kimarsa tun a zamaninsa, har zuwa yau. Ba kuma wai kallo ko shaidar da Musulmi suka yi masa kadai za ka duba ba, har ta wadanda ba Musulmin ba.
Watakila hakan zai sa mu fi tabbatarwa cewa shi fa MAI KIMA NE A IDON DUNIYA, a da can da kuma a yanzu kuma har duniyar ta kare. Don haka dole ne kuma Ya zama mai kima a garin Kano.
A wannan gada, ina so ne in yi magana a kan kima da daraja da girmansa da wasu mutane wadanda ba Musulmi ba suke gani, da kuma shaidar da suka yi masa. Watakila za mu fi gane cewa ba mu kadai da abin ya zama wajibi a kanmu muka san kimarsa ba.
Na san da yawanmu za mu iya tunawa da marubucin nan dan kasar Amurka, Machael Hart. Wanda ya rubuta littafin nan mai suna ‘The hundred: Ranking of the World’s Most Influential Persons.’ A ciki ya lissafo mutane dari, wadanda ya ce duk duniya babu wadanda rayuwarsu ta taba ko ta amfani mutane kuma suka samu nasara cikin tafiyarsu kamarsu.
Tare da cewa ya lissafo mutane masu muhimmanci matuka a gare shi da sauran mutane, ciki kuwa har da Annabawa, kamar Isa da Musa (sa) da sauran shahararru a fagagensu, kamar su Isaac Newton da Aristotle da Julius Caesar da sauran muhimman mutanen da suka taka muhimmiyar rawa a duniya, wadanda yawancinsu ma ’yan uwansa ne Turawa.
Amma abin mamaki, sai ya sa Annabi MUHAMMAD (saw) a farkon lisafin nasa! Shi ma ya yarda babu tamkarsa a duniya!!
Kuma da yake ya san mafi yawan masu karanta littattafan nasa ba Musulmi ba ne, sai da ya yi togacciya da cewa:
‘’My choice of Muhammad to lead the list of the world’s most influential persons may surprises some of my readers and may be kuestioned by others, but he was the only man in history who was supremely successful in both religious and secular lebels.’’
Cewa, ya san zadin da ya yi na Annabi MUHAMMAD (saw) din a matsayin mutum na farko a jadawalin zai ba wa masu karatu mamaki, kuma wasu ma za su so jin ba’asi. Amma a tarihi shi kadai ne mutumin da ya samu cikakkiyar nasara a fannin yada addininsa da ma wasu fannonin da ba su shafi addini ba, fiye da kowa.
Dalilan da ya kawo suna da yawa, kuma suna da ban kaye kwarai.
Ya Ilahi! Idan har mutumin Amurka wanda ba Musulmi ba ya san darajar Annabi, yana kuma kokarin kare ta haka, tare da ya san mafi yawan ’yan uwansa ba za su so abin da ya yi ba, ina amfanin mutumin Najeriya ko na Kano Musulmi da ba zai tashi ya kare matsayi da kimarsa ba?
Don haka, zan yi amfani da wannan kafa, in tuna wa Mahukuntan Jihar Kano cewa, muna nan mun zuba muku idanu. Muna so mu ga yadda za ku yi da masu cin mutumcinsa da ke hannunku. Kuma ku sani cewa, muna sane da cewa Kundin Tsarin Mulki na Jihar Kano na 2000, ya tanadi hukuncin kisa ga irin wannan laifi. Don haka ba za mu lamunci wata wala-wala ba. Lallai ne a kare martabar Annabinmu a Kano, kamar yadda ake kare ta a wasu garuruwan kuma kamar yadda doka da addini suka tanada.