Martabar Musulmi ta fara dawowa a Najeriya – Sarkin Wase

Mai martaba Sarkin Wase kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Filato Alhaji Sambo Haruna Mahammad ya ce yanzu martabar al’ummar Musulmi ta fara dawowa a kasar nan.Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da neman gudunmawar Naira miliyan 25 don fadada masallacin Juma’a na kungiyar Jama’atu […]

Martabar Musulmi ta fara dawowa a Najeriya – Sarkin Wase
Martabar Musulmi ta fara dawowa a Najeriya – Sarkin Wase

Mai martaba Sarkin Wase kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Filato Alhaji Sambo Haruna Mahammad ya ce yanzu martabar al’ummar Musulmi ta fara dawowa a kasar nan.
Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da neman gudunmawar Naira miliyan 25 don fadada masallacin Juma’a na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah da ke Unguwar Kwanar Shagari a garin Jos fadar Jihar Filato.
Sarki Sambo Haruna ya ce halin da al’ummar Musulmi suka samu kansu a Najeriya da Jihar Filato a yanzu, dole ne su yi wa Allah godiya saboda wannan gata da ya yi musu.
Ya ce “Mu shugabanni babu lokacin da muke cikin farin ciki kamar wannan lokaci, saboda a yanzu ’yan uwanmu Musulmi, suna da matukar muhimmanci da martaba, wanda rabon da mu ga haka an dade.”
Sarkin ya yi kira ga al’ummar Musulmi su taimaka wa kansu da kansu musamman a irin wannan aiki na fadada masallacin.
A jawabin Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya bayyana cewa kowane Musulmi da ke jihar da sauran al’umma sun yarda zaman lafiya da kwanciyar hankali ya fara dawowa a jihar. Ya ce wannan zaman lafiya da ci gaba da aka fara samu a jihar ya samu ne sakamakon addu’o’in da ake yi a kullum.
Gwamna wanda Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Barista Yusuf Gambo Hawaja ya wakilta ya bai wa al’ummar Musulmin jihar tabbacin cewa gwamnatin za ta ci gaba da tafiya da duk al’ummar jihar ba tare da nuna bambancin addini ko kabilanci ba.
Tun da farko a jawabin shugaban kwamitin aikin fadada masallacin, Alhaji Muhammad Yahaya Kega ya ce sun yanke shawarar fadada masallacin ne saboda ganin jama’ar unguwar suna karuwa. “Don haka muka yanke shawarar fadada masallacin tare da inganta shi don jama’a su ji dadin yin Sallah a ciki,” inji shi.
Ya ce an kafa kwamitin aikin na mutum 20 tun a shekarar 2013 da suka fara aikin ta hanyar yanka wa kansu kudi a duk wata.
Kega ya ce ganin irin kokarin da kwamitin yi ya sanya shugabannin kungiyar na jiha suka yanke shawarar shirya taron don a taimaka a kammala aikin fadada masallacin.
Babban mai kaddamarwa Alhaji Auwalu Maigwanjo ya bayar da gudunmawar Naira
dubu 500, sai Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya bayar da Naira dubu 500, Sakataren Gwamnatin Jihar Naira dubu 100, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati Naira dubu 100, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati Naira dubu 100.