Martabar Najeriya ta dawo a idon duniya – Blair

Tsohon Firayi Ministan Biritaniya, Tony Blair ya ce martabar Najeriya ta dawo a idon duniya, sakamakon yadda aka gudanar da zabe a kasar nan. Mista Tony Blair ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya kawo ziyarar taya murna ga Shugaban kasa mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari a kan nasarar da ya […]

Martabar Najeriya ta dawo a idon duniya – Blair
Martabar Najeriya ta dawo a idon duniya – Blair

Tsohon Firayi Ministan Biritaniya, Tony Blair ya ce martabar Najeriya ta dawo a idon duniya, sakamakon yadda aka gudanar da zabe a kasar nan. Mista Tony Blair ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da ya kawo ziyarar taya murna ga Shugaban kasa mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari a kan nasarar da ya samu a zaben da aka yi. A cewar Mista Blair akwai kalubale sosai da ke gaban gwamnati mai jiran gado, amma idan har aka samu taimakon jama’a, to, gwamnatin za ta iya magance matsalolin. A nasa bangaren, Janar Muhammadu Buhari ya ce ya ji dadin ziyarar ta Mista Blair kuma sun tattauna kan yadda Amurka da Biritaniya za su ci gaba da taimakon Najeriya domin ta samu nasara. Janar Buhari ya ce ’yan Najeriya sun nuna wa duniya cewa dimokuradiyya ta zauna daram a kasar nan. A karshen wannan wata ne za a rantsar da Janar Muhammadu Buhari a matsayin sabon Shugaban kasa.

Sarkin Kano ya bukaci Kwankwaso da Shekarau su hada kai
Daga Jabiru A. Hassan, Kano

Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na Biyu ya bukaci Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Ministan Ilimi kuma tsohon Gwamnan Jihar Malam Ibrahim Shekarau su kawar da bambancin siyasa tare da hada kai don ciyar da jihar gaba. Sarki Sanusi na Biyu ya yi wannan tsokaci ne yayin da Minista Ibrahim Shekarau ya jagoranci manyan jami’an ma’aikatarsa zuwa fadarsa, inda suka mika masa takardar nada shi a matsayin Uban Jami’ar Benin da Gwamnatin Tarayya ta yi. Sarkin ya ce yana da kyua a samu cikakken hadin kai a tsakanin Gwamna Kwankwaso da Minista Shekarau ta yadda Jihar Kano za ta kara bunkasa sannan tsarin siyasar jihar ya zamo alheri ga al’ummarta da kasa baki daya. Malam Sunusi ya tunatar da Ministan cewa saura ’yan kwanaki kalilan ya dawo gida Kano kuma ya ci gaba da rike matsayinsa na Sardaunan Kano, don haka wajibi ne a samu fahimtar juna a tsakanin ’yan siyasar jihar.

Idan gwamnatin APC ta neme mu za mu ba da gudunmuwa – Namoroko
Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

Wani matashin dan siyasa da ya tsaya a takarar dan Majalisar Dokokin Jihar Kebbi a karkashin Jam’iyyar PDP daga karamar Hukumar Birnin Kebbi, Alhaji Hassan Namoroko, ya ce a shirye suke idan gwamnatin APC a jihar ta neme su da su ba da gudunmawa domin ci gaban jihar duk da suna Jam’iyyar PDP. Alhaji Hassan Namoroko ya fadi haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Birnin Kebbi, inda ya ce, dama don jama’a yake siyasa idan har ya ga gwamnatin APC ta fito da tsarin kyautata wa matasa da ci gaban jihar, babu abin da zai hana shi ba da tasa gudunmawa ga gwamnatin APC a Kebbi da kasa baki daya. Ya gode kan goyon bayan da jama’a suka nuna masa, ya ce dama ya shiga takarar ce don ya kara samun damar taimaka wa matasa da bayar da gudunmawa ga ci gaban karamar Hukumar Birnin Kebbi da jihar baki daya, ya kuma ce taimakon da suke yi wa jama’a tun can farko har yanzu sai abin da ya ci gaba.