Martani a kan tarihin zuwan Fulani Zariya
A labarin da aka buga na zuwan Fulani Zariya, akwai kura-kurai da ya kamata a gyara. Na farko, lokacin da fulani suka shigo ta kwarbai, sarki na idi a bayan gari. Da aka fada masa an kwace gari sai ya nufi Kauru. To a lokacin garuruwa uku ke cin gashin kansu. Su ne: Durum da […]
A labarin da aka buga na zuwan Fulani Zariya, akwai kura-kurai da ya kamata a gyara. Na farko, lokacin da fulani suka shigo ta kwarbai, sarki na idi a bayan gari. Da aka fada masa an kwace gari sai ya nufi Kauru. To a lokacin garuruwa uku ke cin gashin kansu. Su ne: Durum da Kauru da Kajuru. Da yake ta Durum Fulani suka shigo Zariya, sai Sarki Muhammadu Makau dan sarki Isiaku da ake kira Jatau ya nufi Kauru tare da kaninsa Abubakar Ja da Abubakar Kwaka da kuma duk mutanensa. Da aka hana shi shiga garin sai ya fusata kuma aka ce ya yi masu baki, sannan ya wuce zuwa Kajuru inda sarkin Kajuru Haruna ya karbe shi tare da mutanensa. An yi yaki na wata shida ba a ci Kajuru ba. A Tudun Sansanin gabas da Rafin Romi aka yi ta gwabza yaki, ba a ci nasara ba, sai Fulani suka ce za su kwashe ‘ya’yan Kajuru har da na Sarkin Kajuru su kai su Zariya a matsayin bayi. Makau ya ce su bar wa Kajuru yaransu shi zai yi gaba, amma “za su zo su same shi.’ Fulani suka ce wa zai zo wurin Kado?
Makau ya kama hanyar zuwa Zuba. To a rafin da sarkin Kajuru suka yi sallama da Makau ya ce wa sarki Haruna ya koma don shi ma kada a zo a ci garin, har gobe ana kiranta da Rafin Gafara. A Zuba Makau bai shiga garin ba, sai ya ci gaba da neman kasa ta yaki, inda har ya kai Lapai. A can ne mayakansa suka bijire masa. Lokacin a shekara ta 1846 ne. Sai ya ce wa kaninsa Abuja da Abu kwaka su tafi don tashi ta kare. A kauyen Lapai aka kashe shi . Shi kuma Abuja ya tafi ya kafa garin da ya sa mata sunansa. Dangogin wadananan ke sarautar Abuja har yanzu da ta koma Suleja.
Albarka ba mutumin Kajuru ba ne, don mutanen Kajuru Barebari ne ba Kado kamarsa ba. Dangantakansa da Kajuru kawai ta wajen wani babban malami ne da ake kira Malam Abduljalil dan Malam Salihu dan Mahumudu dan Suleiman mutumin Yemen da suka biyo ta Kukawa zuwa Kajuru a shekarar 1825. Malam Ibrahim Tsoho dan Malam Abduljalil ne ya zo Zariya don koyar da addinin musulunci sai aka ba shi gida a sashin. Barde Jibrilla Bagobiri da ya zo Zariya daga Gobir wajen 1806 kuma shi ya kawo masu Kakaki don kiran mutane a fita zuwa fagen daga. Dangin Ibrahim Tsoho da na Barde Jibrilla su ne mazaunan Unguwar Kakaki yanzu a birnin Zariya. Da fatan wanna gyaran zai daidaita kuskuren farko.
Suleiman Saidu, dangin ne na Malam Ibrahim Tsoho, mazaunin Unguwar Kakaki. Birnin Zariya.