Martani: Abba Na Titin da Shata ya yi wa waka ya rasu shekara 14 da suka wuce – dan uwansa
Wani dan uwan marigayi Alhaji Abba Na Titi Mai Mota, mai suna Alhaji Ali Mai Canji ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda wani mutum da ya yi ikirarin cewa shi ne Abba Na Titi Mai Mota, wanda Dokta Mamman Shata ya yi wa waka, inda ya ce shi wancan dattijon da ya ayyana […]
Wani dan uwan marigayi Alhaji Abba Na Titi Mai Mota, mai suna Alhaji Ali Mai Canji ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda wani mutum da ya yi ikirarin cewa shi ne Abba Na Titi Mai Mota, wanda Dokta Mamman Shata ya yi wa waka, inda ya ce shi wancan dattijon da ya ayyana kansa da sunan dan uwansa wanda kuma jaridar Aminiya ta kawo hirarsa, a makon jiya, ba shi ba ne. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
‘Abba Na Titi Mai Mota’
“Ko Ummarun gidan danduna ya san Na Titi mai mota”
“Motar ta tashi don karfinka ko don darajar kakanka”
Abba Na Titi Nai Mota”
Aminiya: Me za ka ce a kan marigayi Abba Na Titi wanda Shata ya yi wa waka?
Alhaji Ali: Da farko dai ni da marigayi Alhaji Abba Na Titi Mai Mota, wa da kane muke. Domin da mahaifiyata Hajiya Agyara da mahaifinsa Alhaji Ida uwarsu daya, ubansu daya. Ka ga ke nan dan-uwana ne na kusa. Kuma Allah ya hada jinina da shi domin duk inda ya je ya dawo nan wajena zai zo saboda gaba nake da shi. Duk da cewa ni ma na yi yawace-yawace kafin in dawo in shiga siyasa, na san Abba a kan sana’ar tukin mota tun irin wacan Tirela babba mai uwa da diya. Inda yake zuwa Kurmi. Amma bayan shi ban taba sanin wani ya ce sunansa Abba Na Titi ba, domin inda akwai shi da mun ji. Asalin sunan Titi kuma da ake yi masa lakabi da shi, sunan ’yar uwarsa ce,uwa daya uba daya. Ka san ko a tsakanin ‘yan uwa akwai wadanda suka fi jituwa tsakaninsu, to haka ta kasance tsakaninsu da ita.
Ana masa wannan sunan ne saboda yadda yake wadansu abubuwa na ban mamaki a wadansu lokuta. Wannan ya sa ake yi masa kirari a duk lokacin da ya yi irin wadannan abubuwan mamakin. Ganin haka ya sa shi da kansa yake cewa kada a hada shi da kowa sai ’yar uwarsa Titi. Wannan shi ne dalilin da ya sa ake kiransa da sunan Na Titi. Marigayin ya yi suna sosai lokacin da yake tukin mota domin sun yi aiki tare da su Jikan-Baje da Gurshe da sauransu.
Aminiya: Ko ka san abin da ya sa Shata ya yi masa waka?
Alhaji Ali: A’a. Domin lokacin da ya yi masa waka ina kasar Ghana ina harkokina, sai dai na san wakar. Kuma wani abin tambaya ga shi wannan wanda ya ce shi ne Abba Na Titi Mai Mota wanda Shata ya yiwa waka shi ne, ya manta da cewa a cikin wakar Shatan yana lissafa sunayen garuruwa ciki har da Kanon, amma duk masu amshin suna cewa ne, “ba su da Na Titi Mai Mota. Shi kuma ya ce, haifaffen Kano ne.” Gaskiya abin ya daure mana kai matuka.
Aminiya ta yi bincike a kan abin da ya hada Shata da shi Abba Na Titi har ya yi masa waka, inda wadanda suka san dalilin suka shaida wa wakilinmu cewa: “Kasancewarsa direba mai zuwa Kurmi duk lokacin da ya dawo yakan tsaya a garin Funtuwa wajen dan uwansa, Alhaji Garba wanda a wurinsa ne ya san Shata, kuma ya ci gaba da yi wa Shatan alheri. Amma bai yi masa wakar ba.” Wata majiya ta ce Shata ya yi wa Abba Na Titi waka ta farko a garin Tama da ke cikin Karamar Hukumar ta Kankinya ne, yayin da wata majiyar ta ce, shi kanshi Na Titin lokacin yana Legas ne ya fara jin wakar tasa. Har ila yau, wani abokinsa mai suna Alhaji Ali ya ce: “Wata rana Abba Na Titi ya zo shagona ya ce yana neman tsoffin kudin nan da aka bar yayinsu da ake kira Anini da na tambaye shi abin da zai yi da su sai ya ce Shata ne ya ce ya samo masa su domin yana sonsu. Allah ya sa ina da su,na kwaso na ba shi ya kai masa. To wannan kyauta ita ce sanadiyyar da ya sa Shata ya yi masa waka.
Shi ma Aminu Magini wanda yake kane ne ga shi Abban,ya ce,”a gabana Shata ya yi wakar Abba Na Titi a gidan wasa na Nasara kulob da ke Sabon Layi Katsina, a lokacin auren Sa’in Katsina, Alhaji Amadu Na Funtuwa da Hajiya Maimuna a gidan Sarkin Daura. Ni na rike wa Abba Na Titi jakarsa muka je wajen wannan bikin. A nan na fara ganin Shata ido da ido,lokacin ina saurayi.
A nan ne ma na ga shi Ummaru dandan Dunan da shi Shatan ya yi wa waka”. Da Aminiya ta so jin ko mene ne dalilin da ya sa Shatan ya ce,”Motar ta tashi don karfinsa ko don darajar Kakansa, wanda hakan ya alakanta shi da Shariftaka? Sai Aminu ya ce,”duk da sanina cewa Abba ya kan yi wadansu abubuwa na ban mamaki amma ba Sharifi ba ne. Ka san akwai hikimar waka ga Shata wanda dan abu kalilan zai kalla ya aza ka a kai kuma abin ya yi daidai. Misali,ya ce Sarkin Zazzau jikan Mujaddadi ne,amma sai ya ce a wajen matarsa. To shi Na Titi babansa ne ya auro wata mata, to sai ta zo da wata diya wadda ita wannan diyar babbanta Sharifi ne,kuma sai Allah Ya sanya jituwa a tsakaninsu. To irin abubuwan da yake yi,sannan kuma ana kiransa Abba, ina jin sune Shatan ya yi amfani da su,domin idan ba wanda ya sani ba ba ka cewa wannan yarinya ba kanwarsa ba ce.”
Bincike ya tabbatar da cewa Alhaji Abba, wanda cikakken sunansa Ma’azu, an haife shi a garin Katsina ne kimanin shekaru 69 da suka wuce. Kuma ya rasu a cikin shekarar 2000 yana da shekaru 55 a duniya. Ya bar ‘ya’ya 10. Hakazalika, ita kanta Hajiya Titin wadda ta yi jinyar marigayin kuma ake masa inkiya da ita, ta rasu kimanin watanni biyu da suka wuce.