Martani daga makaranta (2)
Yau kuma ga karashen martanin da wasu daga cikin makaranta wannan shafi suka aiko, kamar yadda muka yi alkawari. A sha karatu lafiya! Ina barayin suke?Aminu Mu’azu Zango: To, Malam Ibrahim, ai wannan mai sauki ne, tunda muna ganin sanwa tana dahuwa, kullum ana saukewa ana raba mana, amma mun kasa daina jin yunwa. Saboda […]
Yau kuma ga karashen martanin da wasu daga cikin makaranta wannan shafi suka aiko, kamar yadda muka yi alkawari. A sha karatu lafiya!
Ina barayin suke?
Aminu Mu’azu Zango: To, Malam Ibrahim, ai wannan mai sauki ne, tunda muna ganin sanwa tana dahuwa, kullum ana saukewa ana raba mana, amma mun kasa daina jin yunwa. Saboda haka dole cikin dayan biyu, kodai wani bangare ba ya dahuwa ko kuma itacen dahuwar ba su kai ko’ina ba.
Salisu Suliman dan-Nasarawa: Wannan batu naka babu wanda zai iya cewa ba haka ba ne, saboda koda mutum yana da wani tunanin ganin an ci gaba a kasa, to in ba ya samu taimako daga Allah ba, babu wuya a dulmiyar da shi. Sai dai kawai mu ce Allah Ya kyauta Ya kuma agaje mu baki daya.
Salisu Tukur Gaiwa: Allah Ya kara daukaka Malam da za a samu irinka dubu a Najeriya kowa ya kada tamburan fuskantar gaskiya ya kuma ja damarar karo da maha’intan da ke sanya wa dankalinmu sankara, to da babu shakka a cikin ’yan shekaru kalilan za a fuskanci gaskiya a kuma bi ta a zauna lafiya. Ni ma na sanya sunana a wannan sabuwar rajistar da Malam ya bude, Allah Ya taimake mu, Ya agaza mana, Ya nuna mana shiriya, Ya ba mu ikon yin riko da ita duk rintsi duk tsanani.
Mustapha Ibrahim: Malam ai halaliyarka ka ci, kai ba barawo ba ne!. Ba ma haka ba, ba ma ka samun abin da ya dace da gudunmawar da kake ba al’umma a maganar kudin shiga. Su ma talakawan haka. Muggan shugabanni suka ja mana, mu kanana. A zamanin baya, idan kana yawan yi wa mutum (kamar mai ziyara) alheri, zai dawo ne yana jin kunyarka. Hakan ta faru ne saboda abubuwa na da sauki ga al’umma. Wannan sauki kuma, ya sanya wa jama’a wadatar zucci. Amma yanzu ko rance/bashi kake yawan bayarwa, idan ba ka yi hankali ba, sai an dulmiya ka. Ba maganar kunya ko kawaici. Dole ce ke koro jama’a. A da magani kyauta. Ingattaccen ilimi kyauta. Taki kusan kyauta. Haka lantarki da fetur. kananan kudi, sukan biya bukatu. To yanzu ’yan siyasa sun babbake komai. Sun hana komai motsin da ya dace. Don haka dole na kasa-kasa su yi ta ’yan dabaru don rufa wa kai asiri. Allah Ya kyauta.
Abdullahi Mujaheed: Malamina ke nan! barawo a harshen adabi, amma a zahiri, mu mun san ba barawon ba ne! Ni kuwa, dama ce ban samu ba, amma barawon nake!
Darda’u Idiris Safana: A zahirin gaskiya na tsaya na yi nazarin wannan kasida ta Malam don ta dace da wannan suna da na ba ta, kuma wannan batu haka yake babu sashen da bai tabo ba a cikin rayuwarmu. Fatarmu Allah Ya ba mu mafita da kuma ikon gyara al’amuranmu na yau da kullum.
Auwal G. danbarno: Malam, ai kuwa mun amince har ma za mu dora dan ba na rubutu a kan mas’alar, da ma burinmu yanzu shi ne mu yi rubutun da wata ran za a tuna da mu, rubutun da jikokinmu za su yi alfahari da mu.
Zaharradeen Bello: Amma Malam ai ba a taruwa duka a zama daya, domin duk wadannan miyagun halaye na algushu da satar dukiyar mutane da ka lissafo wani bai ma san ana yin su ba, saboda shi ba ya yi, bai kuma tarayya da mai yin.
Usman Modibbo: Allah Ya taimaki Shaihin Malami ina ba da shawara a tattara bayanan na Malam a maida su karamin littafi ko ’yar karamar kasida, don amfanin sauran jama’a.
Najib Tsafe: Farfesa, yanzu mu dukanmu makaryata ne, kuma barayi ne mu?
Lawal Abubakar: To Malam wannan dogon ta‘aliki naka ya yi, kuma Allah Ya saka da alheri, daga karshe Allah Ya ba mu ikon daina halaye marasa kyau domin kasarmu ta gyaru.
Aminu Alhassan: Ni ma haka Farfesa. Allah Ya kara ma basiri da daukaka amin. Allah Ya ba mu shugabanni na kwarai kuma Ya sauya tunanin mu talakawa da su bisa kishin kasa da bunkasarta, mu bar zalunci da yaudara da cin amana da yake abin kwalliya da alfahari a yau!
Umar Badikko Lado: Malam, ai ba a taruwa a zama daya duk duniya. Na gode.
Mun kammala!