Martani ga Ali Baba, Malamai ba abin wasa ba ne
A watannin da suka shude, mai bai wa gwamnan Kano shawara a kan harkar Addini, wato Ali Baba ya yi wasu kalamai masu cike da cin mutunci da tozarci ga malaman addinin Musulunci. Domin kwatanta malamai da masu shirya fina-finai, kwatance ne mai cike da zalunci da rashin sanin ya kamata.A wancan lokacin, Ali Baban […]
A watannin da suka shude, mai bai wa gwamnan Kano shawara a kan harkar Addini, wato Ali Baba ya yi wasu kalamai masu cike da cin mutunci da tozarci ga malaman addinin Musulunci. Domin kwatanta malamai da masu shirya fina-finai, kwatance ne mai cike da zalunci da rashin sanin ya kamata.
A wancan lokacin, Ali Baban ya yi ikirarin cewa: Da malaman Addini da masu shirya fim din Hausa duk daya suke! Saboda a nasa kuntataccen tunani, wai dukansu fadakarwa suke yi. A wancan lokacin dai mun dauka jahilci ne kawai ya sa shi furta wadannan kalamai. Shi kuma jahili ka ga daidai yake da jaki ko kuma kare! To ta yaya kare zai yi haushi mutum ya dawo ya zama daya da shi su rika haushi? Wannan ta saka ba mu ja wata doguwar daga ba sai muka bar zancen.
A wannan lokaci kuma, da ake zaton cewa Ali Baban ya yi nadamar wadancan kalaman, kawai sai ga shi yana mai cewa, wai yana Umurtar malaman Jihar Kano da su rika sayen faya-fayen wasan kwaikwayo suna kallo domin kara habaka karatunsu. Kun ji fa! Wai malamai kuma na Addini yake gaya wa haka. Baya ga waccan kuma yanzu ya zo ya yi wannan. Ashe ke nan harkar tsabar rainin wayau ne, ba jahilci ba.
Inda za ka kara gano cewa Ali Baba ya raina Allah da Annabi, shi ne a cikin kalaminsa na gaba da yake cewa: Da ’yar wasan Hausa mai taka rawa a cikin wasar kwaikwayo domin ilmantar da jama’a, da kuma ’yar Hisba duk lada iri daya suke samu, wai domin duk aiki guda suke yi.
Kun dai san duk wanda zai iya furta hakan dole ya zamo jahili marar tunani, kuma wanda ke bakin cikin al’umma ta zauna lafiya. Tunanin da yake fado min a rai shi ne: Shin anya Ali Baba ba wata jaruma ce daga cikin ’yan matan wasan Hausa ke zuga shi yana wadannan kalamai ba? Domin rashin kan gado da ta-ido kadai ba za su sanya mutum aikata irin wadannan kura-kurai ba. Lallai dole sai da sharrin ’ya mace. Koda yake na ji wasu na cewa wai ya nakalci bori ne. Allah dai shi ne masani akan gaskiyar wannan zance.
Yanzu dai abin da yake gabanmu shi ne, muna kira ga mai girma gwamnan Jihar Kano Musa Kwankwaso da ya sani cewa, al’ummar Kano suna ganin girmansa, amma ba za su iya jure wadannan kalamai masu kona zuciya suna fitowa daga wani da yake jami’i a cikin gwamnatinsa ba. Saboda haka ya gaggauta cire Ali Baba daga kan mukaminsa saboda maslaha guda biyu.
Na farko ya gwadi kishinsa ga addini, na biyu kuma ya tsira da mutuncinsa duniya da lafira. Muna yabon gwamnatin Kwankwaso matukar yabo musamman akan yadda take karfafa aikin Hisba da ke fada da fitsara a jihar ta Kano. Amma mutuncin gwamnatin ya fara faduwa kasa warwas saboda barin wani mutum yana cin zarafin malamanmu da yawun gwamnatin. Wallahi tallahi ba za mu ci gaba da zura ido hakan na faruwa ba.
Me ye amfanin irin Ali Baba a cikin gwamnatin Kwnakwaso? Ina ma dai laifin a ce kwamishinan wasanni ne ko mai ba da shawara akan yawon bude ido? A fili take cewa bai san darajar malamai ba. Ta yaya kuma za a ce a karkashin ofishinsa suke? Ko shi kanshi Kwankwason idan ba don ya san daraja da mutuncin al’ummar Kano ba ai bai dace a ce shi ne matsayin gwamna ba.
Maganar gaskiya daya ce, Ali Baba ba mutumen kirkin da ya dace ya jagoranci mutanen kirki ba ne. Don haka muke kira ga gwamnatin Kano da ta yi wa Allah ta cire shi daga kan mukaminsa tun bai gama barar da girma da darajar Jihar Kano a idon duniya ba. Shin idan kuma gwamnan ne ke da sha’awa da ya ga Ali Baba rike da mukami, ai ba lalle sai
wanda yake kai yanzu ba. Me ya sa ba za a yi masa shugaban ’yan kasuwar jihar Kano ba, ko kuma shugaban makada da mawakan jihar Kano?
Ina jiye wa kanmu tsoron abin da kan iya faruwa nan gaba idan aka kyale wannan dan taliki yana tozarta malamai yadda yake so. Kuma ina jiye wa Ali Baban shi kansa musibar da kan iya samunsa dalilin wanna izgili da yake ta kokarin yi wa addinin Allah dare da rana. Wallahi Malamai ba abin wasa ba ne.
Allah Ya daukaki jihar Kano da masu nufinta da alhairi, Allah Ya wanzar muna da zaman lafiya a duk fadin Najeriya. Allah Ya ba mu shugabanni na gari masu son Allah da addinin Allah, ba masu neman mafita ga kawunansu ba. Allah Ya karbi kyawawan ayyukanmu, Ya yafe munanan ayyukanmu, Ya kuma yi mana arzikin cikawa da imani don alfarmar Annabi Muhammad SAW.
Nasir Abbas Babi
08033186727
08095653401